Sunday, December 22
Shadow

NLC ta buƙaci a gaggauta sakin shugabanta

Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta buƙaci hukumomin ƙasar su gaggauta sakin shugabanta ba tare da wani sharaɗi ba.

Da safiyar ranar Litinin ne hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kama Mista Ajaero a filin jirgin saman Abuja, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Birtaniya domin halartar taron ƙungiyar kwadago TUC, ta Birtnaiya

Cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Benson Upah ya fitar, ya ce ta sanya rassanta na jihohi da manyan ƙungiyoyin da ke ƙawance da ita cikin shirin ko-ta-kwana, kan lamarin da ta kira mai ”tayar da hankali”.

“Ƙungiyarmu ba za ta zuba ido tana ganin ana tozarta shugabanni da mambobinta ba, don haka muke buƙatar a gaggauta sakin Kwamared Ajaero, ba tare da gindaya kowane irin sharaɗi ba”, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske..

Karanta Wannan  Naso ace zan iya daukar ciki in haifa maka yara>>Dan Daudu Bobrisky ya gayawa saurayinsa

Sanarwar ta ci gaba da cewa ”an tsare mista Ajaero a wani wuri da ba a sani ba, don haka ba a san halin da lafiyarsa ke ciki ba, duk wani yunƙuri na jin halin da yake ciki ya ci-tura”.

NLC ta kuma ce yanzu haka ta shiga taron sirri da manyan shugabanninta, tana mai cewa za ta bayyana wa duniya abin da tattauna da zarar ta kammala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *