Shugaban rukunin Kamfanin Mai Na NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana nasarar kammala biyan bashin da ake bin kamfanin da ga kamfanonin mai na kasashen ƙetare inda ya ce a yanzu, babu mai bin kamfanin bashin sisin kwabo.
Kyari ya ce, wannan babban nasara ce da aka cimma biyo bayan cire tallafin mai a Gwamnatin Shugaba Tinubu.
“Mun rika karkatar da kudadenmu da dukiyoyinmu don tabbatar da komai na tafiya daidai a bangaren mai na PMS mai wuyar sha’ani, abinda ya rika janye hankalin NNPC daga biyan basussuka”
Mele ya ci gaba da cewa
“ Sai dai yanzu wannan matsala ta kau, za ku ga cewa ba mu da wani bashin da ake bin mu, kuma don mu tabbatar da dorewar hakan, ya zama wajibi a kawar da duk wata matsala don masana’antar ta iya samar da makamashi mai dorewa da arha da ake buƙata a ƙasar nan.”
Shugaban NNPC din ya kuma tabbatar da cewa, zuwa ƙarshen rubu’in farko na shekarar 2025, za a samu akalla manyan tashoshin rarraba CNG har 12 a faɗin ƙasar.
“A cikin rubu’in farko na 2025, za a samar da akalla tashoshi 12 na CNG, har ma da gina ƙaramar masana’antar LNG da za ta rika samar da iskar gas din al’amuran yau da kullun a kasuwa, da kuma saukaka rarraba CNG mai inganci da iskar gas ga kananan turakun samar da wutar lantarki a cikin wannan masana’anta a dan ƙanƙanin lokaci.”