Monday, December 9
Shadow

Mutane 10 sun mùtù da dama sun jikkata a mummunan hadarin mota da ya faru a jihar Jigawa

Mutane 10 sun mutu da dama sun jikkata a wani mummunan hadarin mota da ya faru a jihar Jigawa.

Lamarin ya farune a karamar hukumar Taura dake jihar.

Wani Shaidar gani da ido ya gayawa manema labarai cewa hadarin ya farune a kauyen ‘Yanfari dake kan hanyar Kano zuwa Hadejia a karamar hukumar Taura.

Yace motar bas ce ta daki wata Tirela dake a gefen titi inda motar ta wuntsula mutane 10 suka mutu nan take.

Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Lawan Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yace lamarin ya farune ranar November 12, 2024 kuma suna samun labari jami’an su suka garzaya wajan inda yace sun tarar direban motar da mutane 9 sun mutu.

Karanta Wannan  Ba zamu yadda a saka shari'ar Musulunci a cikin tsarin kudin mulkin Najeriya ba>>Inji Lauya Kola Alapinni

Yace akwai mutum da ya da bai mutu ba a yanzu ana duba lafiyarsa.

Yace suna kan bincike dan gano ko akwai laifin wani a hadarin da ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *