Sunday, January 12
Shadow

Obasanjo da Yakubu Gowon sun goyi bayan kungiyar su shekarau dake son kwace mulki daga hannun Tinubu shekarar 2027

Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar su tsohon Gwamnan Kano kuma sanata Ibrahim Shekaru me suna LND dake son rikidewa zuwa ta siyasa, ta samu goyon bayan tsaffin shuwagabannin Najeriya, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo.

Kungiyar dai na ci gaba da tuntubar manyan ‘yan siyasa dga yankunan Kudu maso yamma da kudu maso kudu da kudu maso gabas dan cimma burinta.

Shugaban kungiyar, Dr Umar Ardo ya tabbatar da komawarta ta siyasa dan samar da Jam’iyya me karfi da hadin kai da zata karade kowane yanki a kasarnan.

Duka shuwagabannin biyu, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo sun yi na’am da wannan tafiya inda suka bayar da shawarar mayar da ita ta kasa baki daya.

Karanta Wannan  Jarumin Finafinan Hausa, Ayatullahi Tage Ya Angonce A Karon Farko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *