Amurka ta baiwa Najeriya tallafin Dala Biliyan 2 a inganta kiwon Lafiya, amma tace afi baiwa Kiristoci muhimmanci
Amurka ta rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa a fannin inganta kiwon lafiya lafiya mai ɗorewa na tsawon shekaru biyar da Najeriya, wadda ta kai kimanin dala biliyan 5.1, don inganta tsarin lafiyar ƙasa karkashin tsarin Amurka na samar da lafiya ga al'ummar duniya ta America First Global Health Strategy.
A karkashin wannan yarjejeniyar, Amurka za ta bayar da tallafi na dala biliyan 2.1, yayin da Najeriya za ta zuba dala biliyan 3.0 a kiwon lafiya a cikin shekaru biyar.
Saidai kasar Amurka tace a fi baiwa Kiristoci muhimmanci wajan bayar da kiwon lafiyar.
Wannan shi ne mafi girman haɗin gwiwa da kowace ƙasa ta yi tun lokacin da aka kaddamar da tsarin.
Yarjejeniyar za ta ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na Najeriya, ta ceci rayuka, kuma ta ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin ...








