Hamas ta soki Blinken kan kalamansa game da batun tsagaita wuta
Hamas ta mayar da martani ga suka daga sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken dangane da jan ƙafa wajen amincewa da ƙudurin tsagaita buɗe wuta, inda ta ce ta yi abin da ya kamata game da tattaunawar zaman lafiya.
Hamas ta bayyana cewa ta yi abin da ya kamata dangane da sabuwar shawarar tsagaita buɗe wuta da kuma duk shawarwarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta," inda ta banbanta matsayinta da Isra'ila, wanda ta ce ba ta fito fili ta bayyana amincewa da shirin tsagaita buɗe wuta ba.
Blinken ya sha ambata cewa Isra'ila ta amince da shawarar tsagaita wuta, kodayake gwamnatin Isra'ila ba ta tabbatar da hakan a hukumance ba.
Da yake magana a Qatar a ranar Laraba, Blinken ya bayyana taƙaicin yadda Hamas ta mayar da martani, yana mai cewa Hamas ta gabatar da sauye-sauyen da ...








