Da Ɗuminsa: Ba Za Mu Tafi Yajin aiki ba – NLC ta bayyana
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya bayyana cewa kungiyoyin kwadago ba za su tafi yajin aiki a ranar Talata ba, dangane da sabon takaddamar mafi karancin albashi da gwamnati ke fuskanta.
Da yake bayar da dalilin daukar matakin, Ajaero ya ce har yanzu ma’aikata ba za su tafi yajin aikin ba saboda a halin yanzu alkaluman na kan teburin shugaban kasa Bola Tinubu kuma ana sa ran za a mayar da martani.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito shugaban NLC ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a ranar Litinin a taron kungiyar kwadago ta duniya da ke gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland.
Yayin da yake buga misalan gwamnatocin da suka gabata, Ajaero ya ce har yanzu akwai yuwuwar Shugaban kasa ya kara adadin da ake so a gabansa.
Sai dai ya yi kira ga Gw...





