Thursday, December 18
Shadow
A karin farko, An ga Sauro a kasar Iceland

A karin farko, An ga Sauro a kasar Iceland

Duk Labarai
Rahotanni sun ce a karin farko an ga Sauro a kasar Iceland. Kasar Iceland dai itace daya tilo da babu sauro a Cikin a tsakanin kasashen Duniya. Dalili kuwa shine kasar na da tsananin sanyi wanda sauro baya iya rayuwa a ciki. Sannan kuma basu da ruwa dake kwanciya sosai wanda shima hakan na taimakawa wajan tara sauro. Saidai duk da haka gashi a karin farko a yanzu an ga sauro a kasar.
Kalli Bidiyo: Mafi yawanci abinda zai kai mutanen Arewacin Najeriya Whuta hakkin bayin Allah ne>>Inji Sheikh Nura Khalid

Kalli Bidiyo: Mafi yawanci abinda zai kai mutanen Arewacin Najeriya Whuta hakkin bayin Allah ne>>Inji Sheikh Nura Khalid

Duk Labarai
Malam Nura Khalid ya bayyana cewa, mafi yawancin abinda zai kai mutanen Arewacin Najeriya wuta, hakkin bayin Allah ne. Malam ya kawo misali da hakkin 'ya'ya akan iyaye inda ya kawo misalin masu haihuwar 'ya'ya su barsu suna watangaririya a titi. https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7563977265688710407?_t=ZS-90ld9ZHi77Z&_r=1
Da Duminsa: Dangote zai sayar da wani sashe na matatar mansa

Da Duminsa: Dangote zai sayar da wani sashe na matatar mansa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Attajiri, Dangote zai sayar da wani kaso tsakanin kaso 5 zuwa 10 na matatar mansa a kasuwar hannun jarin Najeriya. Dangote ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a kafar  S&P Global ranar 20 ga watan October inda yace zai yi hakanne kamar yanda yawa kamfanoninsa na sukari dana Siminti. Dangote yace baya son rike fiye da kaso 65 zuwa 70 cikin 100 na hannun jarin matatar man. Yace a hankali a hankali zai rika sayar da hannun jarin matatar ya danganta ga yanda mutane ke son saye ko kuma yanayin kasuwa. Hakanan Dangote yace yana son kara yawan man fetur din da suke tacewa duk rana zuwa ganga Miliyan 1.4 a kowace rana. Idan hakan ta tabbata, matatar man Dangote zata zama ta daya a Duniya wajan yawan fitar da man fetur inda zata zarta ta kasar I...
Allah Sarki,Kalli Bidiyo gwanin ban tausai, Sun dauke ta da niyyar aikata Alfasha, Ashe matsayafa ne, duk da tana rokonsu su yi hakuri, sun mata Tsyrara suka aikata inda ba’a dawowa dan yin tsyfin kudi

Allah Sarki,Kalli Bidiyo gwanin ban tausai, Sun dauke ta da niyyar aikata Alfasha, Ashe matsayafa ne, duk da tana rokonsu su yi hakuri, sun mata Tsyrara suka aikata inda ba’a dawowa dan yin tsyfin kudi

Duk Labarai
Wannan wata Budurwa ce da lamarin ta ya baiwa mutane da yawa tausai. Wasu matasa matsafa da aka fi sani da Yahoo Boys ne suka dauketa suka kaita gida da niyyar aikata Alfasha da ita amma a karshe ashe tsafi zasu yi da ita. An ga Bidiyon ta tana ta rokon su kada su Kashye ta amma suka aikata lahira? Suka cire mata kai, da gabanta da sauran wasu sassan jikinta. A karshe dai asirinsu ya tonu an kamasu. Danna nan dan kallon Bidiyon
Kungiyar Malaman Jami’a, ASUU ta janye yajin aikin data shiga

Kungiyar Malaman Jami’a, ASUU ta janye yajin aikin data shiga

Duk Labarai
Ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta dakatar da yajin aikin gargadi na tsawon makonni biyu da ta fara, inda ta bai wa gwamnatin ƙasar wata ɗaya domin ta magance buƙatunta. Shugaban ƙungiyar, farfesa Chris Piwunayayin wata ganawa da manema labarai, ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne domin bai wa gwamnati dama ta nuna kyakkyawan niyya wajen tattauna matsalolin da suka shafi albashi da kayan aiki da inganta yanayin aiki a jami’o’in kasar. Ƙungiyar ta ce abun da yasa suka janye yajin aikin shine gwamnati ta gabatar da matsayarta kan sabunta yarjejeniysar shekarar 2009 kuma da kiraye-kirayen da suka samu daga mutane da dama daga ƙasar domin sun janye yajin aikin. Wannan ne ya sa ƙungiyar ta bai wa gwamnatin ƙasar wata ɗaya domin ta magance buƙatunta. K...