Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta bayyana cewa, bata cika yadda da mutane ba saboda sun cika karya.
Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda ta saki kayatattun hotuna:
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga manufar ma’aikatar ilimi ta tarayya na kayyade shekarun shiga jami’o’i, inda ya bayyana hakan a matsayin wani baƙon abu da zai janyo komabaya ga harkar ilimi a Najeriya
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana manufar a matsayin "zai haifar da naƙasu ga hakar ilimi" inda ya ce hakan ya saɓa wa ƙa'idojin tsarin ƙasar ta hanyar shiga ayyukan gwamnatocin jihohi.
Atiku ya yi nuni da cewa ilimi na cikin abubuwan da ke cikin ƙundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bai wa ƙananan hukumomin ƙasar karfi wajen tafiyar da harkokinsa.
Ya yi allah-wadai da matakin da gwamnati ta ɗauka na kafa manufofin ilimi ba kamar yadda doka ta tanada ba inda ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasa...
An saki ɗalibai da malamai ƴan asalin ƙasar Poland da aka kama a lokacin da aka yi zanga-zangar tsadar rayuwa, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Poland ya bayyana a ranar Laraba.
Mutum bakwan sun shiga hannu ne a Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, "bisa zargin su da hannu a ɗaga tutocin Rasha da ma ita kanta zanga-zangar," kamar yadda jami'an tsaron Najeriya suka bayyana.
Sai dai hukumomi a ƙasar Poland sun ce waɗanda aka kama ɗin ɗalibai ne na Jami'ar Warsaw da malaminsu, waɗanda "tsautsayi ya kai su inda bai dace ba."
Ministan Harkokin Wajen Poland, Radoslaw Sikorski ya ce yanzu an sako ɗaliban.
"Ina tabbatar da cewa an sako mutanenmu ɗin nan, yanzu haka sun koma Kano sun ci gaba da karatunsu," kamar yadda Sikorski ya wallafa wani bidiyo a shafi X.
Ya ƙara da...
Cibiyar tattarawa da yaɗa bayanai kan rikice-rikice (CCC) ta yi gargaɗin cewa garkuwa da mutane na ƙaruwa a Najeriya, inda ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyarv ƙasar da ta ayyana dokar ta-ɓaci domin magance matsalar.
Shugaban CCC, Manjo Janar Chris Olukolade, mai ritaya, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa matsalolin za su iya ta'azzara idan ba a yi abin da ya dace ba, wanda hakan zai ƙara jefa rayuwar al'umma cikin matsala da ƙara taɓarɓarar da matsalar tsaro.
Sanarwar ta ƙara da cewa garkuwa da mutane ta rikiɗe zuwa wata babbar harka ta kasuwanci, inda ƙungiyoyin ta'addanci ke amfani da lamarin domin samun kuɗin shiga.
"Sace mutum da aka yi na kwana-nan shi ne sace basarake a Masarautar Sokoto, da sace ɗaliban jami'a masu karatun kiwon lafiya guda 20, waɗanda aka sako daga ...
Bayan an shafe kwanaki ana sukar yadda gwamnatin jihar Sokoto ke tafiyar da sha’anin tsaro, musamman bayan garkuwa da kuma kashe Sarkin Gobir na Gatawa, a yanzu hukumomin jihar sun bayyana cewa suna iyakar ƙoƙarinsu kan matsalar.
A makon da ya gabata ne ƴan bindiga suka kashe Sarkin Gobir, Muhammad Isa Bawa, bayan yin garkuwa da shi na sama da mako uku, lamarin da ya janyo wa hukumomi kakkausar suka.
Wasu dai a Najeriya na zargin hukumomi da gaza yin abin da ya kamata wajen kawar da matsalar tsaro a faɗin ƙasar.
Ƴan fashin daji na kai hare-hare a jihohin arewa maso yammacin ƙasar, yayin da har yanzu ake fuskantar hare-hare nan-da-can na ƙungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas.
Hukumomin Najeriya dai sun ce suna bakin ƙoƙarinsu wajen magance matsalar.
Sai dai kisan da a...
Daga Bello Abubakar Babaji
A ranar Litinin ne Hukumar kula da harkokin Zuba hannun-jari ta Ƙasa, NSIA ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ta tara Naira biliyan 60 a ɓangaren cire tallafin taki a ƙarƙashin shirin taki na shugaban ƙasa (PFI) cikin shekaru takwas.
Hukumar, wadda tayi nazari kan ayyukan PFI, ta ce hakan wani yunƙuri ne bunƙasa masana’antar takin Nijeriya inda aka samar da masarrafa guda 84 a shiyyoyi shida na Nijeriya.
Ci gaban ya kuma tara Dala miliyan 200 daga hada-hadar cinikayyar ƙasashen wajen wanda hakan ya taimaka wajen samar da ayyuka 100,000.
Hakan nan, shirin PFI ya jagoranci raba buhunan taki mai inganci miliyan 90 ga manoma a Nijeriya.
Darakta Manaja na NSIA, Aminu Umar Sadiq ya yi ƙarin haske game da nasarorin da aka samu ta hanyar shirin waɗanda suk...