Saturday, December 13
Shadow
Maganar Gaskiya, Malam Lawal Triumph duk da namune, sai mun fadi gaskiya, Yayi Kuskure kalaman da yayi kan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) kuma ya kamata a hukuntashi>>Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya bayyana cewa duk da Malam Lawal Triumph yana bangarensu ne amma maganar gaskiya yayi kuskure. Malam ya bayyana cewa maganar Sheikh Lawal Triumph bata dace da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba amma kuma bata fitar dashi daga Musulunci ba. Ya kawo misalin irin hakan data faru a baya inda yace ladabtarwa ce ake wa irin wannan suka yi hakan. https://www.tiktok.com/@mai.6013/video/7557115827904990482?_t=ZS-90I63lDof5M&_r=1
Mu muka rika raka ‘yan siyasa da kudaden da suka sata suna kaisu kauyukansu suna boyewa amma gashi yanzu mun gama aiki an kasa biyanmu hakkokinmu>>Tsohon Dansandan Najeriya ya koka

Mu muka rika raka ‘yan siyasa da kudaden da suka sata suna kaisu kauyukansu suna boyewa amma gashi yanzu mun gama aiki an kasa biyanmu hakkokinmu>>Tsohon Dansandan Najeriya ya koka

Duk Labarai
Tsohon dansandan Najeriya me mukamin DSP ya koka game da yanda yace an kasa biyansu hakkokinsu bayan sun kwashs Shekaru 35 suna aiki. Yace a lokacin da suke aiki, sune suka rika raka 'yan siyasa da kudaden da suka sata zuwa kauyukansu suna boyewa, yace amma gashi sun gama aiki biyansu hakkokinsu ya gagara. Ya bayyana hakane a wajan zanga-zangar neman hakokinsu da suka fito. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1974387956904571003?t=Z9OF0PHH9teHjvcwcOcFYg&s=19
Ni gadon Musulunci na yi wajan iyayena, amma matata Fasto ce kuma ban taba ce mata ta zama Musulma ba>>Inji Shugaba Tinubu

Ni gadon Musulunci na yi wajan iyayena, amma matata Fasto ce kuma ban taba ce mata ta zama Musulma ba>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a wajan jana'izar mahaifiyar shugaban jam'iyyar APC, Nana Lynda Yilwatda ya bayyana muhimmancin soyayya sama da kiyayya. Shugaban yace shi gadon Musulunci yayi a wajan iyayensa kuma bai taba neman canja addininsa ba. Yace matarsa Kirista ce, Fasto amma bai taba gaya mata ta zama musulma ba. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1974496920312905814?t=mxOlc0UaOBW-ijj_RgXGRA&s=19
Kalli Bidiyo: Da Kare da Alade duka ba Najasa bane>>Inji Sheikh Maqari

Kalli Bidiyo: Da Kare da Alade duka ba Najasa bane>>Inji Sheikh Maqari

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Ibrahim Maqari ya bayyana cewa da kare da Alade duka ba najasa bane. Ya bayyana hakane bayan wata tambaya da aka masa cewa, karene ya taba jikin wani mutum. Malam yace kare yana kamo dabba, watau ana zuwa dashi farauta ya kamo dabba kuma a ci, yace dan haka ba najasa bane. Malam ya kara da cewa, har Alade ma ba najasa bane. https://www.tiktok.com/@binyusuf37/video/7554864115823430920?_t=ZS-90H29wUGzFQ&_r=1
Kalli Bidiyon:An kama wani magidanci Da ya Dirqawa diyarsa cikin shege a jihar Yobe

Kalli Bidiyon:An kama wani magidanci Da ya Dirqawa diyarsa cikin shege a jihar Yobe

Duk Labarai
Wani Magidanci me suna Umar Maigoro ya shiga hannun jami'an tsaro bayan dirkawa diyarsa ciki. Yarinyar me shekaru 16, ya mata karyar cewa, bashi ne ya haifeta ba inda yace ida shegiya ce mahaifiyarta ta je gidansa da itane shi kuma ya rene ta. Saidai da ciki ya shiga sun yi kokarin zubar dashi amma sai Asiri ya tonu. Kalli Bidiyon jawabinsa a kasa: https://www.tiktok.com/@sirkhamerl/video/7556744491114384648?_t=ZS-90H0utX9l5d&_r=1