Saturday, December 13
Shadow
Shoprite sun kulle shagunansu a Ibadan da Ilorin, saboda mutane basa zuwa siyayya, Hakanan a shagunan Abuja da Legas na Shoprite ba kaya saboda matsin tattalin arziki

Shoprite sun kulle shagunansu a Ibadan da Ilorin, saboda mutane basa zuwa siyayya, Hakanan a shagunan Abuja da Legas na Shoprite ba kaya saboda matsin tattalin arziki

Duk Labarai
Rahotanni sun ce Kamfanin manyan shagunan siyayya na Shoprite ya kulle a Ilorin da Ibadan saboda matsin tattalin arziki da ya hana mutane zuwa siyayya. Hakanan a Abuja da Legas, Shagunan na Shoprite ba kaya. Hakannna zuwa ne saboda matsin tattalin arziki da Najeriya ke fama dashi. A baya dai Shoprite sun kulle shagonsu dake Kano.
Kalli Bidiyo: Ina da Otal mutane suka daina zuwa, shine na mayar dashi gidan Qaruwai, a yanzu ina samun dubu dari 3 duk rana

Kalli Bidiyo: Ina da Otal mutane suka daina zuwa, shine na mayar dashi gidan Qaruwai, a yanzu ina samun dubu dari 3 duk rana

Duk Labarai
Wani me otal da yace mutane sun daina zuwa kama daki a otal dinsa, yace ya mayar da otal din gidan karuwai. Yace wani abokinsa ne ya bashi shawara kuma shawarar ta yi aiki. Yace amma matarsa tace ba zata zauna ta raini 'ya'yansu da kudin da aka samu daga gidan karuwai ba. Yace yayi-Yayi da ita takiya ta tafi gidansu, kuma tace ba zata dawo ba sa ya kulle gidan karuwan. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1968381354888020150?t=5aijlnagtqVXRDui1ypOWg&s=19
Mun raba kudin Talli Naira Biliyan 330 ga gidaje Miliyan 8.5 a Najeriya>>Inji Ministan kudi

Mun raba kudin Talli Naira Biliyan 330 ga gidaje Miliyan 8.5 a Najeriya>>Inji Ministan kudi

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya tace ta rabawa gidaje Miliyan 8.5 Tallafin kudi Naira Biliyan 330 a fadin Najeriya. Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana hakan. Ya bayyana hakane ranar Laraba a Abuja inda yace gwamnati ta dawo da raba tallafin bayan Gyare-Gyaren da aka wa tsarin. Yace suna raba kudadenne saboda ragewa mutane radadin tsadar rayuwa inda yace mutane Miliyan 15 suke son rabawa. Yace zuwa yanzu sun raba kudin a gide Miliyan 8.5 inda suke biyan Naira dubu shirin da biyar duk wata. Ministan yace sauran ma zuwa karshen shekarar nan za'abasu.
Kalli Bidiyo: Shekarata 30 da haihuwa kuma aurena 9>>Inji Wannan Tauraruwar fina-finan Hausan

Kalli Bidiyo: Shekarata 30 da haihuwa kuma aurena 9>>Inji Wannan Tauraruwar fina-finan Hausan

Duk Labarai
Tauraruwar Fina-finan Hausa ta bayyana cewa Shekarunta 30 kuma aurenta 9. Ta bayyana hakane a yayin wata ganawa da aka yi da ita inda tace auren na 9 be dade da mutuwa ba. Tace a baya, bata iya fadin haka amma yanzu zata iya fada ko dan ya zamarwa wasu darasi. https://www.tiktok.com/@mustaphayalo/video/7550385904641182994?_t=ZS-8zp8RqburxJ&_r=1
Tin kamin in hau Mulki akwai Yunwa a Najeriya, dan haka a rika min Adalci bani na kawo yunwa kasarnan ba>>Inji Shugaba Tinubu

Tin kamin in hau Mulki akwai Yunwa a Najeriya, dan haka a rika min Adalci bani na kawo yunwa kasarnan ba>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa tin kamin ya hau mulki akwai yunwa a Najeriya. Shugaban ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Daniel Bwala a yayin da ake hira dashi a gidan talabijin na TVC. Bwala yana martanine ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da ya soki Gwamnatin kan halin da mutane ke ciki. Bwala yace tun a lokacin da aka baiwa Najeriya 'yancin kai akwai yunwa a Najeriya, yace ba a lokacin Tinubu aka yi wakar Najeriya Jaga-jaga ba dan haka tun kamin hawansa akwai matsaloli da suka mamaye kasarnan. Yace amma 'yan adawar ba zasu fadi irin nasarorin da gwamnatinsu ta samu ba sai inda aka samu matsala.
Matashi daga Kano, Ibrahim Bala ya kirkiro na’urar da zata taimaka wajan hana direbobi Hadari

Matashi daga Kano, Ibrahim Bala ya kirkiro na’urar da zata taimaka wajan hana direbobi Hadari

Duk Labarai
Wani matashi daga Kano me suna Ibrahim Bala ya kirkiro na'urar da zata hana direba bacci wanda hakan ake tsammanin zai rage yawan aukuwar Hadurra. Matashin yace ya kirkiro wannan na'ura ne bayan aukuwar hadarin motar da yayi sanadiyyar salwantar rayukan 'yan kwallon Kano wanda aka alakanta da baccin da ya dauke direbansu. Tuni dai tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya shiga gaba dan ganin wannan matashi ya samu tallafi.
Da Matatar Man fetur dina bata yi nasara ba da na talauce dan da duk kadarorina bankuna zasu kwace>>Inji Dangote

Da Matatar Man fetur dina bata yi nasara ba da na talauce dan da duk kadarorina bankuna zasu kwace>>Inji Dangote

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, da Matatar mansa bata yi nasara ba da duka kadarorinsa za'a kwace ya koma kauye da zama. Yace dalili kuwa shine kadarorinsa ne ya bayar bankuna suka bashi bashin da ya gina matatar man fetur din tasa. Dangote yace an rika kiransa ana gargadin sa cewa Gwamnati ce kadai take irin wannan aikin gina matatar man fetur din da yake yi. Yace amma duk da haka yayi kunnen uwar shegu ya ci gaba.
Da Duminsa: NECO ta fitar da sakamakon jarabawar 2025 kuma an ci ba laifi

Da Duminsa: NECO ta fitar da sakamakon jarabawar 2025 kuma an ci ba laifi

Duk Labarai
Hukumar Shirya jarabawar kammala sakandare, NECO ta fitar da sakamakon jarabawar kuma kaso 60 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarabawar sun yi nasara. An saki sakamakon jarabawar ne kwanaki 54 bayan rubutata. Ragistara na NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi ya sanar da sakamakon jarabawar inda yace dalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarabawar. Wanda suka ci jarabawar kuma sun kai 818,492 wanda hakan yake nufin kaso 60.26 cikin 100 sun ci jarabawar. Wadannan wadanda suka ci lissafi da turanci ne. Hakanan yace wadanda kuma suka ci 5 credit sun kai 1,144,496, wanda hakan ke nufin kaso 84.26.