Wuridin kudi nan take
Musulunci ya amincewa mutum ya roki Allah Arzikin Duniya da ya hada da Kudi, Mata ta gari, da sauransu.
Tirmizi ya ruwaito daga Sabit, Anas yace, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi waslalam yace "Kowannenku na da damar ya roki Allah dukkan abinda yake so, hadda rokon Allah madaurin takalmi idan ya katse.
Albani ya inganta wannan hadisi.
Wannan na nuni da cewa komai mutum zai roka ya roki Allah, saidai a nemi Albarka a cikin rayuwar Duniya da dukiyar da kuma Lahira zai fi.
Hakanan manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam, ya taba tambayar Abuzar(RA) cewa, Abu Zar me kake tunani game da mutumin da yake da tarin Duniya, zaka kirashi me Arziki?
Abu Zar(RA) ya amsa da cewa, tabbas zan kirashi da me Arziki ya Rasulullah.
Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam ya sake tambayar...