Monday, December 15
Shadow
Kalli Bidiyo: Wani dan siyasa ya taba tasowa tsakar dare ya kawo min kudade masu yawa amma naki karba>>Sheikh Sani Yahya Jingir

Kalli Bidiyo: Wani dan siyasa ya taba tasowa tsakar dare ya kawo min kudade masu yawa amma naki karba>>Sheikh Sani Yahya Jingir

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa, wani dan siyasa ya taba kai masa kudi cikin dare amma ya ki karba. Malam ya bayyana hakane a wa'azin da yake yi wanda Bidiyon tuni ya dade da watsuwa a kafafen sada zumunta. https://www.tiktok.com/@i.agashua001media/video/7551129407599971591?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7551129407599971591&source=h5_m&timestamp=1758540663&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7545729042580113168&share_link_id=c92b3f5d-3cae-45...
Hotuna: Kashim Shettima ya sauka a Amurka dan hakartar taron Majalisar Dinkin Duniya

Hotuna: Kashim Shettima ya sauka a Amurka dan hakartar taron Majalisar Dinkin Duniya

Duk Labarai
Kashim Shettima Ya Isa Birnin New York Na Amurka Don Halartar Taron Majalisar Ɗinkin Duniya Na 80 Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York domin halartar zaman taro na 80 na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), wanda zai gudana daga ranar Litinin zuwa 28 ga watan Satumba. An tarbe shi a filin jirgin sama na John F. Kennedy inda ya samu rakiyar ministoci da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, da Ministan Tsaro, Badaru Abubakar. Shettima, wanda yake wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabi a madadin Najeriya a taron, tare da halartar muhawarorin manyan shugabanni da kuma wasu tarurruka a gefen taron Majalisar. Haka kuma, zai sanar da sabbin kudirin Najeriya na rage dumamar yanayi (NDCs) karkashin...
Ban yadda a bincike ni ba>>Inji Gwamnan Rikon Kwarya na jihar Rivers da shugaba Tinubu ya nada bayan ya kammala wata shida

Ban yadda a bincike ni ba>>Inji Gwamnan Rikon Kwarya na jihar Rivers da shugaba Tinubu ya nada bayan ya kammala wata shida

Duk Labarai
Gwamnan rikon kwarya na jihar River, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (retd.) Ya bayyana kin amincewa da binciken da majalisar jihar ke son yi masa. Ya bayyana hakane bayan da majalisar jihar ta amince ta binciki watanni shida da yayi yana matsayin gwamnan jihar. A ta bakin me magana da yawunsa, Hector Igbikiowubu, Ibas yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya nadashi kuma majalisar tarayya ta rika lura da aikin da yake. Yace idan dai majalisar tace zata bincikeshi to tana son ta binciki shugaban kasar kenan da majalisar tarayya. Saidai yace ba bu wanda zai hana majalisar jihar binciken idan tace tana son ta yi.
Kalli Bidiyo: Yanda Shugaban Izala Sheikh Bala Lau ya janye Lasifika daga bakin Alaramma Ahmad Sulaiman yana tsaka da karanta Qur’ani ya tafi gaisawa da shugaba Tinubu ya jawo cece-kuce

Kalli Bidiyo: Yanda Shugaban Izala Sheikh Bala Lau ya janye Lasifika daga bakin Alaramma Ahmad Sulaiman yana tsaka da karanta Qur’ani ya tafi gaisawa da shugaba Tinubu ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
A ranar Juma'ar data gabata ne aka daura auren dan Sanata Abdulaziz Yari a Masallacin Sultan Bello Kaduna. Shugaban Izala,Sheikh Bala Lau ne ya ya gabatar da huduba kamin zuwan liman. Saidai a yayin da yake wa'azi, Alaramma Ahmad Sulaiman na ja masa baki, sai ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya shiga masallacin. Ai kuwa nan da nan Sheikh Bala lau ya janye lasifika daga bakin alaramma Ahmad Sulaiman yana tsaka da karatun Qur'anin ya tafi gaisawa da shugaba Tinubu. Hakan ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke ganin bai kamata ba. https://www.tiktok.com/@muhammadsunnahaljosawy/video/7552481590450900231?_t=ZS-8zvFbjBS0LA&_r=1
Kalli Bidiyo: Fasto da ya lura mata na zuwa cocinsa sanye da riga kawai babu rogar Mama a ciki ya raba musu rigar maman saidai yace ba zasu tafi da ita gida ba, da an gama zaman cocin su cire su aje mai kayansa

Wani fasto ya dauki hankula bayan da aka ga yana rabawa mata rigar mama. Faston ya bayyana rashin jin dadinsa ne da ganin yanda mata ke zuwa cocin nasa babu rigar mama. Dan hakane ya raba musu rigar maman amma yace ba zasu tafi da ita gida ba. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1969467628222661084?t=feabGIpcSzv_4kTqje1imw&s=19
Akwai yiyuwar Tinubu ba zai so sauka daga Mulki ba, zai so ci gaba da zama shugaban Najeriya har karshen rayuwarsa>>Inji El-Rufai

Akwai yiyuwar Tinubu ba zai so sauka daga Mulki ba, zai so ci gaba da zama shugaban Najeriya har karshen rayuwarsa>>Inji El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi gargadi cewa muddin 'yan Najeriya basu tashi tsaye ba suka yi abinda ya kamata a 2027 ba, to lallai Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai so ya zarce ya mulki Najeriya har iya tsawon rayuwarsa. El-Rufai ya kwatanta Abinda Tinubu ke son yi da irin mulkin shugaban kasar Kamaru, Paul Biya. El-Rufai yayi wannan maganane a yayin da Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kai masa ziyarar jaje bayan tarwatsa taron ADC da aka yi a Kaduna. El-Rufai yace ko mulkin Soja bai ga ana yin irin kamar karyar da Gwamnatin Tinubu ke yi ba Dan haka yace dolene a hada kai.