Wannan hotunan kadarorin tsohon Ministan shari'a Abubakar Malami kenan da EFCC ta gano da darajarsu ta kai Naira Biliyan 212.
Kadarorin na jihohin Kebbi, Kano ne.
Rahotanni sun ce malaman jinya 16,000 ne wanda suka yi karatu a Najeriya suka tsere zuwa kasar Ingila suke aiki a can.
Hakan ya farune a tsakanin shekarun 2017 zuwa 2025.
Kuma Rahoton yace hadda Ungozoma ne ke tserewa daga Najeriyar zuwa kasar Ingila.
An samu wannan bayanai ne daga rijistar da kasar Ingilar ta fitar.
Wannan na nuni da cewa, Najeriya na fuskantar karancin malaman jinya yayin da 'yan kasar ke tserewa zuwa kasashen Turai dan aiki a can saboda albashi me kyau da ake biya acan din.
Kafar Channels TV suna shan suka saboda yanda suka rubuta Rahoton abinda ya faru a masallaci a jihar Borno jiya.
Abin fashewa ya fashe a masalacin jihar Borno inda wasu suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata.
Saidai Channels TV a rahoton data kawo tace abin fashewar ya fashene a Maiduguri yayin da ake bikin Kirsimeti.
Da yawa dai sun zargi Channels TV da Munafurci saboda bas saka cewa a masallaci abinnya faru ba hakanan wasu na cewa babu abinda ya hada tashin abin fashewar da Kirsimeti tunda ba a coci ya faru ba.
https://twitter.com/abdool_moh/status/2003928512697127192?t=dGCUI_2x8o4uCjHm8S_MRw&s=19
Malam Lawal Triumph ya bayyana cewa, ya ji wani malami na wa'azin cewa akwai wani abu da ake sayarwa wanda da Alade ake yinsa kuma mutanen mu musulmai na ci.
Yace amma malamin bai fito da abin fili ba watakila saboda yana tsoron kada kamfanin su kaishi kara ne.
Malam yace tun da dai ba da sanin mutane ke ci ba, basu da laifi.
https://www.tiktok.com/@taskarmalanlawantriumph/video/7587549699377302804?_t=ZS-92VaLuRO7iS&_r=1
Tauraron Tiktok, Hassan Make-Up ya fito ya rantse da Qur'ani cewa ba Maryam Yahya bace ta yi cikin shege ba har ta haihu.
Ya bayyana hakane a shafinsa na Tiktok inda yace shi ya je har gidan su wadda ta haihun amma ba Marya Yahya bace.
https://www.tiktok.com/@officielhassanmakeup227/video/7587530542569065739?_t=ZS-92V4rK6yi4e&_r=1
An ga dan gidan Zidane, Luca Zidane yana addu'a kamin wasansu da kasar Sudan.
Kuma kasarsa ta Algeria ta yi nasara da 3-0 akan Sudan a wasan.
https://twitter.com/FaithfullBaller/status/2003933593224290654?t=LcxYMjf8DQrTLh94qxk_cw&s=19
Malamin addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi ya maka wasu mutane 2 a kotu saboda zargin bata masa suna.
Malam ya shigar da karanne ta hannun lauyansa, Suleiman Danlami Lere, Esq., kuma wadanda ake Tuhuna sune George Udom da- Bello Isiaka.
Ana zarginsu da yada wani rubutu da suka dangantashi da Sheikh Gumi inda suka ce wai yawa sabon Ministan tsaron, Christopher Musa barazanar cewa wai idan bai daina kaiwa Tshàgyèràn Dhàjì hare-hare ba, zai kaiwa iyalansa hari.
Sheikh Gumi yace wannan rubutu karyane kuma bashi yayi shi ba.
https://twitter.com/el_uthmaan/status/2003886918912651402?t=Ktz8lxPRke7IGbeFjVhmyQ&s=19
Faston nan dan kasar Ghana da yayi ikirarin an masa wahayi wai ranar Kirsimeti za'a yi tashin Qiyama, yanzu kuma ya fito yace ya roki Allah a daga ranar tashin qiyar kuma an daga.
Yace dalili shine yana son ya fadada jiragen ruwan da ya gina da zasu dauki mutane dan kamar a cewarsa ruwane za'a yi wanda zai mamaye Duniya.
Faston dai yayi kira ga mabiyansa dasu tuba.
https://twitter.com/withAlvin__/status/2003920200392134840?t=qkAwSQeruSOEOlUWqh4T4g&s=19
Wannan matar ta dauki hankulan mutane sosai bayan da ta dauko waya tana Bidiyon a Asibiti bayan mutuwar mahaifiyarta.
Ta rika kalamai na kama da wadda ta zauce.
https://twitter.com/Teeniiola/status/2003818363194315200?t=ZN-LpmcOkFl4CkgiKHDX-w&s=19
Dan gida marigayi shahararren mawakin Najeriya, Fela Kuti, watau Femi Kuti yace shi bai taba yin addu'a ba kuma baya yi saboda wasa ya dauki addu'a.
https://twitter.com/dammiedammie35/status/2003731499036901408?t=OlWXvwnC8pzlEdJQMfaTPg&s=19