Thursday, December 26
Shadow
Kalli Hoton Duniyar Mars da aka dauko daga sararin samaniya, Saidai da yawa na cewa basu yadda da hoton ba

Kalli Hoton Duniyar Mars da aka dauko daga sararin samaniya, Saidai da yawa na cewa basu yadda da hoton ba

Abin Mamaki
Wannan hoton, Tauraron dan Adam mallakin hukumar sararin samaniya ta kasar Amurka, NASA ce daukoshi daga Duniyar Mars, Saidai mutane da yawa sun ce basu yadda ba. An dai dauki hoton ne a ranar 6 ga watan Yunin 2024 da muke ciki. https://twitter.com/MarioNawfal/status/1799797996059554084?t=dL0PGQzE548EtTrzSvEUkA&s=19 Hoton dai yayi matukar kama da Duniyar da muke ciki.
Jin dadin Mulkin Tinubu yasa Gwamnatin jihar Sokoto ta sakawa daya daga cikin Titunan jihar sunan dan shugaban kasa, Seyi Tinubu

Jin dadin Mulkin Tinubu yasa Gwamnatin jihar Sokoto ta sakawa daya daga cikin Titunan jihar sunan dan shugaban kasa, Seyi Tinubu

Siyasa, Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Ali na fuskantar caccaka daga bakunan da yawa daga cikin 'yan Najeriya bayan sakawa wani titi a jihar Sokoto sunan dan shugaban kasa, Seyi Tinubu. Kafar Peoplesgazette ta bayyana cewa tsohon sunan titin shine Pepsi Road. Tace kuma a ranar 3 ga watan Yuni ne ya kamata a kaddamar da titin amma hakan bata samu ba.
Kalli Hoton mutumin da ya sa-yar da ‘ya’yan cikinsa har guda 6 a jihar Sokoto

Kalli Hoton mutumin da ya sa-yar da ‘ya’yan cikinsa har guda 6 a jihar Sokoto

Abin Mamaki
An kama wannan mutumin me suna Malam Bala Abubakar a jihar Sokoto bayan samunaa da laifin sayar da yara har guda 28. Wani abin mamaki ma shine cikin yaran da ya sayar hadda 'ya'yansa guda 6. An dai yadda da Malam Bala Abubakar a matsayin me kula da marayu. Hukumar 'yansanda ta jihar Sokoto tace yana sayar da yaranne ga wasu mata Elizabeth Oja da Kulu Dogonyaro da sunan za'a kai yaran Abuja dan wani mutum ya rika basu kulawa me kyau. Malam Bala dai yana zaunene a unguwar Tudun Wada dake jihar Sokoto. Kuma wanda suka sanshi sun yi mamakin abinda ya aikata. Lamarin dai yana hannun 'yansanda inda ake ci gaba da bincike.
DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yan Crypto sun sa ankulle Tweeter account din Naziru Sarkin Waka

DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yan Crypto sun sa ankulle Tweeter account din Naziru Sarkin Waka

Kannywood, Nazir Ahmad Sarkin Waka
Hakan ya samo asali ne bayan zagin da yayi wa 'yan mining inda yake cewa " Iya mining ɗinka iya talaucin ka" ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da yake yawo a kafofin sada zumunta. Kalaman da mawakin yayi yayi matuƙar da hankulan yan Crypto wanda yakai ga har sun fara fitowa kafofin sada zumunta suna mayar masa da martani, daga bisa ni kuma suka fara turawa mai kampanin tweeter korafin su, wanda daga karshe korafin su ya samu karbuwa har yakai ga an tsaida a shafin sa na tweeter a halin yanzu. Zuwa yanzu sun koma tura korafin su ga sauran kampanonin sada zumunta inda yake da account dasu kama daga facebook, tiktok Instagram. Shin ya kuke ganin matakin da suka ɗauka ?
Wata Mata Ta Cika Da Mamaki Bayan Da Ta Je Duba Gidan Da Ta Ke Ginawa Ta Tarar Wasu Sun Tare A Gidan

Wata Mata Ta Cika Da Mamaki Bayan Da Ta Je Duba Gidan Da Ta Ke Ginawa Ta Tarar Wasu Sun Tare A Gidan

Abin Mamaki
Wata Mata Ta Cika Da Mamaki Bayan Da Ta Je Duba Gidan Da Ta Ke Ginawa Ta Tarar Wasu Sun Tare A Gidan Wata mata da take ƙoƙarin gina gidan kanta a Abuja tayi mamaki bayan da ta tarar da wasu hausawa sun tare a gidan da ta ke ginawa a Abuja. Matar ta ce ta cika da mamaki bayan da ta tarar da mutanen a gidan, wanda bata kammala ginawa ba, su kuma har da gadonsu da kayayyakinsu sun shigar cikin gidan sun tare a ciki. Ta ce bata damu ba, domin har tukwicin Naira dubu biyu ta basu, lokacin da ta umarce su da su kwashe kayansu su fice daga gidan.
‘Yar Najeriya ta kash-she kanta bayan da ta yi lalata da kare kuma aka yi hira da ita akan lamarin kuma bidiyon ya yadu, daga baya ta shiga damuwa sosai ta je ta kash-she kanta, Kalli Bidiyon anan

‘Yar Najeriya ta kash-she kanta bayan da ta yi lalata da kare kuma aka yi hira da ita akan lamarin kuma bidiyon ya yadu, daga baya ta shiga damuwa sosai ta je ta kash-she kanta, Kalli Bidiyon anan

Abin Mamaki
Wata 'yar Najeriya data yi lalata da kare kuma aka yi hira da ita, hirar ta yadu sosai, ta shiga damuwa ta kashe kanta. Matar me suna Kemi ta bayyana cewa wasu danginta ne suka fara yin lalata da ita a rayuwa wanda hakan ya jefata cikin matsananciyar damuwa. Tace wasu lokutan takan yi amfani da karnuka dan ta gamsu ta bangaren jima'i. Matar dai a sakon data bari na karshe kamin ta kashe kanta, tace ta yafewa mahaifiyarta duk da yake ta kasa bata tarbiyyar data kamata.

Maganin ciwon kai kowane iri

Magunguna
Ciwon kai na da magunguna na turawa wanda suke aiki da kyau, musamman idan ba me tsanani bane sosai. Magungunan dake magance ciwon kai sun hada da. Aspirin Paracetamol da Ibuprofen. Hakanan masana sunce kwanciya a cikin daki me duhu, wanda babu hasken wutar lantarki ko na rana na taimakawa wajan magance matsalar ciwon kai. Abincin da ake son me yawan ciwon kai ya rika ci: Nama Ganye, irin su Kabeji, Zogale da sauransu. Gyada. Madara. Kwai. Ana kuma amfani da wadannan dabarun na kasa dan magance matsalar ciwon kai: Amfani da tsumma me sanyi a dora a goshi. Ko Amfani da tsumma me dumi a dora a goshi ko a bayan kai. Ana amfani da Ganyayyaki da aka saka a firjin suka yi sanyi. Ana iya yin wanka da ruwan sanyi. Hasken wutar lantarki, Hasken ...

Maganin ciwon ido kowane iri

Magunguna
Maganin ciwon ido ya danganta da dalilin samuwar ciwon idon. Idan ciwon idon ya fara ne dalilin wani abu da aka ci ko aka shafa, a kyaleshi zai warke da kansa. Akwai magungunan digawa, dana shafawa dama na sha wanda ake amfani dasu kuma yawanci cikin awanni 24 suke warkar da ciwon ido. Amma ga magunguna kamar haka da za'a iya amfani dasu: Ana iya amfani da tsumma me dumi ko kuma me sanyi wanda ba mai cutarwa ba kuma a samu tsumman me kyau, wankakke a dora akan idon. Ana kuma iya amfani da maganin digawa. Ana iya murza idon amma ba sosai ba. Ana kuma iya saka jakar Grean Tea a cikin Firjin idan ta yi sanyi a dora akan idon. Shima Ruwan Gishiri ana amfani dashi wajan magance irin wadannan matsalolin. Wane Lokaci ne ya kamata a ga Likita? Idan ciwon idon be warke...

Maganin kowace irin cuta

Addu'a, Ilimi
Babban maganin kowace irin cuta shine Qur'ani. Kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fada cewa: "Kuma mun saukar da qur'ani wanda warakane kuma rahama ne ga masu imani, amma ba zai amfani masu laifi da komai ba sai bata" Al-Isra’ 17:82. Wannan waraka na nufin ta zahiri da badili. Kamar yanda ma'aikin Allah, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallan) yake karanta suratul Falaq da Nasi akansa da iyalansa a yayin da suke fama da rashin Lafiya. Idan da hakan ba waraka bane, ba zai rika yi ba. Muslim (2192) ya ruwaito cewa, Matar Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wasallam) A'isha ta ruwaito cewa, idan Annabi Muhammad( Sallallahu Alaihi Wasallam) bashi da lafiya, takan karanta masa Falaqi da Nasi ta shafa masa. Hakanan Muslim (2192) ya ruwaito cewa, Matar manzon Allah(SAW) A'...