Tonon Silili: Ji yanda aka gano Matar wani Gwamnan Najeriya na ciyn amanarsa da wani
'Yar takarar mataimakin Gwamna a jihar Anambra a jam'iyyar APC, Ekwunife ta yiwa gwamnan jihar, Charles Soludo tonon Silili.
Inda ta bayyana cewa matarsa ta taba yin lalata da tsohon Gwamnan jihar, Mbadinuju
Ekwunife ta bayyana hakane a wata ganawar sirri da ta yi da wani masoyinta me suna Ifeanyi.
Tace babu wanda zata zauna ya bata mata suna haka kawai, itama sai ta fadi abi da ta sani akansu.
Ta dai fadi wadannan kalamai ne a hirar waya da suka yi wadda kuma an yi recording dinta saidai ta bayyana ba tare da sanin su ba.
Lamarin ya jawo cece-kuce sosai.
Ekwunife ta bayyana hakane bayan da gwamnan jihar, Charles Soludo ya zargeta da amfani da takardun Digiri na 3 watau PhD wanda ta samo daga jami'ar da bata da inganci a kasar Amurka.
Ekwunife ta kara da cewa solu...








