Friday, December 27
Shadow
Hukumar Wutar lantarki ta Abuja zata yankewa hedikwatar Sojoji dana ‘yansanda wuta saboda bashi

Hukumar Wutar lantarki ta Abuja zata yankewa hedikwatar Sojoji dana ‘yansanda wuta saboda bashi

Siyasa
Hukumar wutar lantarki ta Abuja ta bayyana cewa, zata yankewa manyan ma'aikatu da yawa wuta saboda bashin kudin wutar da ake binsu. Ta bayyana cewa, daga cikin hukumin da ake bin bashin akwai hukumar sojojin, dana 'yansanda da ma'aikatar mata ta tarayya, da jihar Kogi, da ma'aikatar Ilimi, da ma'aikatar masana'antu. Hukumar tace ba wata ma'aikata da zata dagawa kafa zata yanke mata wuta. Hakan na kunshene a cikin sanarwar da hukumar wutar ta fitar.

YANZU-YANZU: Real Madrid Ta Ci Kofin Zakarun Turai Karo Na 15 Bayan Ta Yi Nasara Kan Dortmoumd Da Ci 2-0

Kwallon Kafa
Kungiyar Real Madrid ta lashe kofi na 15 bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 2-0 a wasan karshe da suka buga a filin wasa na Wembley. Dani Carvajal da Vinicius Jr ne suka ci kwallayen 2. Tsohon dan wasan Real Madrid din kuma kocinta, Zinedine Zidane ne ya kai kofin filin: Kungiyar Borussia Dortmund ta gayyaci Jurgen Klupp ya kalli wasansu. Shine dai ya kaisu wasan karshe na gasar da suka buga a shekarar 2013. Mahaifi da mahaifiyar Jude Bellingham da dan uwansa sun je kallon wasan. https://twitter.com/footballontnt/status/1796957357852832007?t=AfUBdCBVKdBJiz6B_0kChQ&s=19 Hakana mawakin Amurka Jay Z ma ya je kallon wasan: https://twitter.com/ChampionsLeague/status/1796973390743351387?t=l4Xncg675YAq4gnq5hRRRg&s=19 An samu wani da yayi kutse a ...
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yi niyyar ɗaukar sojoji milyan ɗaya da ƴan sanda milyan ɗaya da a ce ya zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yi niyyar ɗaukar sojoji milyan ɗaya da ƴan sanda milyan ɗaya da a ce ya zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023

Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ya yi niyyar ɗaukar sojoji milyan ɗaya da ƴan sanda milyan ɗaya da a ce ya zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023 Ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar NNPP a zaɓén na 2023 da ya gabata, Engr Rabi'u Musa Kwankwaso ya furta hakan a hirarsa da BBC Hausa, ya ce wannan matakin zai inganta harkokin tsaron Najeriya da ya tabarbare a wasu sassan ƙasar. Wane fata zaku yi masa?
Mugunta ko cin Amana? Ji yanda shugaban wani kauye a jihar Katsina ya karbi cin hancin Naira dubu dari bakwai(700,000) ya amince aka kaiwa mutanen kauyensa hari har aka kash-she 30

Mugunta ko cin Amana? Ji yanda shugaban wani kauye a jihar Katsina ya karbi cin hancin Naira dubu dari bakwai(700,000) ya amince aka kaiwa mutanen kauyensa hari har aka kash-she 30

Katsina, Tsaro
Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Umar Dikko Radda ya bayyana yanda wani shugaban kauye ya karbi Naira dubu dari bakwai ya amince aka kai hari akan kauyenshi wanda yayi sanadiyyar kisan mutane 30. Gwamnan yace an samu hakanne a Guga dake Bakori. Ya kara da cewa ba zasu kyale ko wanene aka samu da hannu a harkar 'yan Bindigar ba. Saboda rayuwar mutanen jihar tafi ta mutum daya ko wanene shi.
Kan mu ya daure, Bamu san wanne hukunci zamu yi amfani dashi ba>>Hukumar ‘yansandan jihar Kano bayan da aka aika mata hukunce-hukuncen kotu har 5 da suka shafi masarautar Kano, saidai ta bayyana abinda zata yi nan gaba

Kan mu ya daure, Bamu san wanne hukunci zamu yi amfani dashi ba>>Hukumar ‘yansandan jihar Kano bayan da aka aika mata hukunce-hukuncen kotu har 5 da suka shafi masarautar Kano, saidai ta bayyana abinda zata yi nan gaba

Kano, Siyasa
Hukumar 'yansandan jihar Kano ta bayyana tsaka mai wuya da take ciki kan hukunce-hukuncen kotu har guda biyar da aka yi kan masarautar Kano. Kwamishinan 'yansandan jihar, Mr Usaini Gumel ne ya bayyanawa manema labarai hakan inda yace sun tattara duka wadannan hukunce-hukuncen 5 sun aikewa da shugaban 'yansanda na kasa yayin da shi kuma ya aikawa da ministan shari'a. Yace suna jiran ministan shari'ar ya gaya musu da wane hukunci zasu yi amfani. Yace da zarar sun samu umarni daga ministan shari'ar, zasu zartas da hukuncin da doka ta amince dashi. Yayi kira kan kafafen yada labarai da su rika tantance labari kamin su yadashi.
An gano Maniyyata na sayarwa da Takari Uniform dinsu a kudi me tsada a kasar Saudiyya

An gano Maniyyata na sayarwa da Takari Uniform dinsu a kudi me tsada a kasar Saudiyya

Hajjin Bana
Hukumar alhazan Najeriya, NAHCON ta gargadi maniyyatan kasar kan sayar wa wadanda ke zaune a Saudiyya domin neman kudi da aka fi sani da 'takari' tufafin da hukumar ta dinka musu domin gudanar da ayyukan hajjin. Daraktan Da'awah na hukumar ta NAHCON reshen jihar Kebbi, Sheikh Aminu Hassan ne ya bayyana haka lokacin da yake yi wa maniyyatan jhar jawabi bayan isarsu kasa mai tsarki. Akwai zarge-zargen cewa takarin na sayen tufafin wasu maniyyatan musamman mata da kudi masu yawan gaske, tare da yin bad da bami domin shiga cikinsu da fakewa da aikin hajjin wajen aikata abubuwan da ba su dace ba. Sheikh Aminu Hassan ya ce sayar da tufafin babban laifi ne da zai iya janyo wa duk wanda ya aikata hukunci mai tsanani, don haka ne ya gargadi maniyyatan su kauce wa wannan mummunar dabi'a. ...