Wednesday, January 8
Shadow
‘Yan Najeriya na sukar mawaki Davido Saboda zargin Kawo Cryptocurrency da yasa suka tafka Asara

‘Yan Najeriya na sukar mawaki Davido Saboda zargin Kawo Cryptocurrency da yasa suka tafka Asara

Nishadi
'Yan Najeriya da yawa na sukar mawaki, Davido saboda zargin kawo Cryptocurrency da yasa suka tafka Asara. Mawakin ya kawo Cryptocurrency me suna $Davido wanda saidai bayan da mutane da yawa suka saya, farashin coin din ya fadi. Da yawa sun hau shafukan sada zumunta suna sukarshi. Dama dai harkar kasuwancin Cryptocurrency na da matukar hadari.
Bidiyo: Sabuwar Rawar da gwamnan Osun yayi ta dauki hankula

Bidiyo: Sabuwar Rawar da gwamnan Osun yayi ta dauki hankula

Duk Labarai
Sabuwar rawar da gwamnan Osun, Ademola Adeleke yayi ta dauki hankula a shafukan sada zumunta. Gwamna Adeleke ya shahara wajan rawa a guraren taruka da yake halarta. Gwamnan dai kawu ne ga shahararren mawakin Najeriya, Davido. A wannan karin ma ya sake taka rawar a wajan taron karrama mutane da jaridar Vanguard ta yi. Kalli Bidiyon a kasa: https://www.tiktok.com/@gbaramatuvoice/video/7372692648819215622?_t=8mnncGdWWP8&_r=1 Yayin da wasu ke yaba mai, wasu na ganin hakan bai dace ba a matsayinsa na gwamna.
Hoto: ‘Yan Sanda Sun Cafke Masu Karbar Adai-daita Sahu Na Sata

Hoto: ‘Yan Sanda Sun Cafke Masu Karbar Adai-daita Sahu Na Sata

Tsaro
Jami’an ‘yan sanda a jihar Adamawa sun kama wasu matasa biyu da ake zargi da karbar babur mai uku na sata. Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta samu ranar Alhamis, inda ta ce ta kuma kwato babur din da aka sace. “A ranar 28 ga watan Mayu, 2024, rundunar ‘yan sandan Adamawa ta samu bayanai game da wani keken napep da aka sace a kan titin Chochi, Rumde, Yola ta Arewa” in ji rundunar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai daukar hotonta na SP Suleiman Nguroje. “Bayan samun labarin, an tura tawagar ‘yan sanda masu sanya ido a hedikwatar Jimeta Divisional ba tare da bata lokaci ba. An yi sa’a, an kama wani Yusuf Adamu mai shekara 18 da kuma Abdul Salam Abubakar mai shekaru 18 a lokacin da suke kokarin sayar da babur din,” in ji ‘yan sandan. ...
YANZU – YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe

YANZU – YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe

Siyasa
YANZU - YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe. Majiyar mu ta a yau ta ruwaito Shugaban ya ce yana bakin ƙoƙarinsa a matakin tarayya amma ya kamata a sanya ido kan Gwamnoni su ma su riƙa yin abunda ya dace, su taimaki talakawa, "A lokacin zaɓe ana bin mutane lungu-lungu, gida-gida don neman ƙuri'unsu amma da zaran anci zabe sai kaga Gwamna ko dan siyasa ya tare a Abuja ya mance da talakawansa" inji Tinubu. Me zaku ce?
Na fice daga Kannywood har karshen duniya kuma naji dadin hakan>>Abdul Sahir

Na fice daga Kannywood har karshen duniya kuma naji dadin hakan>>Abdul Sahir

Kannywood
Jarumi kuma mawaki Abdul sahir wanda akafi sani da Mallam Ali na kwana casa’in ya ce ya fita daga masana’antar kannywood daga yau alhamis 30-05-2024, yace yayi hakan ne don samar wa kansa nutsuwa. Idan zaku iya tunawa hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar kano karkashin jagorancin Abba elmustapha ta dakatar dashi daga shiga fina-finan hausa tsawon shekaru 2, sakamakon wani vidiyon da jarumin ya saka, wanda hukumar ke ganin ya sabawa doka da tarbiyyar jihar kano. Mallam Ali na kwana casa’in ya fice daga kannywood, shin ko waye zai maye gurbinsa acikin kwana casa’in?