Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan
Mahajjatan Najeriya a kasar Saudiyya sun koka da kalar abincin da ake basu duk da biyan Naira Miliyan 8 a matsayin kudin aikin hajjin bana.
Daya daga cikin mahajjatan me suna Babagana Digima ne ya wallafa hoton kalar abincin da ake basu a shafinsa na facebook.
Abincin dai koko ne da kosai guda 3.
Babagana Digima ya kara da cewa, mahajjata yanzu sun koma bara dan neman abinda zasu ci saboda kudinsu dala $300 daya rage daga cikin dala $500 da suke da ita har yanzu ba'a basu ba.
Hukumar Alhazai ta kasa, National Hajj Commission of Nigeria (Nahcon) da take martani akan lamarin, tace ta sa a yi bincike kan lamarin.