Hoto: Sojojin Najeriya sun kai samame inda suka kashe ‘yan ta’adda 6 a Kaduna
Sojojin Najeriya sun kai samame maboyar 'yan ta'adda a Jihar Kaduna inda suka kashe guda 6.
Sojojin sun yiwa 'yan Bindigar kwatan baunane inda suka kashesu tare da kwace makamai da yawa a hannunsu.
Lamarin ya farune bayan da sojojin suka samu bayanai akan ayyukan 'yan Bindigar a kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari ranar Friday, May 24, 2024.
Sojojin sun je hanyar da 'yan Bindigar zasu wuce inda suka musu kwantan bauna, suna zuwa kuwa suka afka musu.
An yi bata kashi sosai inda daga baya 'yan Bindigar suka tsere: