Wata jarumar Kannywood ta bayyana cewa, Tabbas an mata kan ta waye.
Ta bayyana cewa amma ba'a ci OC din ta ba, na kudi aka mata.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyon hirar da aka yi da ita da ya watsu sosai.
https://www.tiktok.com/@mustaphayalo/video/7555136376644046088?_t=ZS-907scJqzGHh&_r=1
Farfesa Jerry Ghana ya bayar da tabbacin cewa, tsohon shugaba kasa, Farfesa Jerry Ghana zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2027 me zuwa.
Hakan ya bayyana ne bayan da rade-radin fitowar tsohon shugaba kasar takara ke kara yaduwa.
Farfesa Jerry Ghana yace tun bayan faduwar tsohon shugaban kasan zabe a shekarar 2015, an samu shugaban kasar da yayi shekara 8 yana mulki kuma gashi an sake samun wani yayi shekaru 2 amma har yanzu 'yan Najeriya ta kiran Goodluck Jonathan ya dawo.
Yace PDP jam'iyya ce ta Adalci da ke baiwa 'yan Najeriya abinda suka zaba.
Malamin Addinin Islama, Sheikh Sani Rijiyar Lemu ya bayyana goyon baya ga Malam Lawal Triumph game da zargin da ake masa na yiwa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Batanci.
Sheikh Sani yace Kalaman da malam yayi suna tare dashi suma akan irin wannan fatawar suke.
Yace da ake cewa wai idan ba'a kama Lawal Triumph ba, shima Abduljabbar a sakeshi, yace idan so suke a saki Abduljabbar su fito kawai su fada ba sai sun yiwa wani sharri ba.
https://www.tiktok.com/@tijjanihassangwale/video/7554523563399580946?_t=ZS-906OnuDGFDV&_r=1
Shahararren mawakin siyasa, Tijjani Gandu ya bayyana goyon bayan kamawa da hukunta Malam Lawal Triumph kan zargin yiwa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Batanci.
Yace su suna kare Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a yayinda dayen bangaren kuma suna kare dan kungiyane.
Yace kuma masu zaginsa cewa, wai shi mawaki ne Jahilaine, su je su tambayi irin gudummawar da mawaka suka bayar wajan kare Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) musamman idan za'a je yaki.
https://www.tiktok.com/@tijjanigandu/video/7554170949399072008?_t=ZS-906Km3PSuBd&_r=1
Tauraruwar Kafafen sadarwa, Sadiya Haruna itama ta bi sahun masu mallakar sabuwar wayar iPhone 17 pro max.
Ta wallafa a shafinta yanda ta bude sabuwar wayar tata.
Kalli Bidiyon anan
Rahotanni sun ce kungiyar manyan ma'aikatan man fetur, PENGASSAN sun baiwa membobinsu umarnin su dakatar da aikawa matatar man fetur ta Dangote Danyen Man fetur da Gas.
Kungiyar tace ta yi hakanne da gudanar da addu'a da neman Shuwagabannin Najeriya su takawa Dangote birki kan karan tsaye da yake a harkar man fetur a Najeriya.
Hakan na zuwane bayan da Matatar Dangote din ta sallami ma'aikatan ta 800 bayan da suka shiga lingo PENGASSAN.
PENGASSAN tace Dangote ya dauko indiyawa amma ya kori 'yan Najeriya 800 da suke masa aiki.
Tace a yayin da ake biyan injiniyoyi 'yan Najeriya Albashin 385,000 a wata, Indiyawa da Dangote ya dauko yana biyansu albashin dala $5000 ne watau kwatankwacin Naira Miliyan 7.5.
Kungiyar PENGASSAN ta bukaci Dangote ya mayar da ma'aikatan 'yan Najeriya...
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya daurawa dansa mukamin 2nd Lieutenant bayan da ya kammala makarantar horas da sojoji ta NDA.
A Bidiyon da ya watsu a kafafen sadarwa anga malam yana daurawa dan nasa mukamin inda ake daukarsa hotuna.
kalli Bidiyon anan
https://x.com/Better_Kaduna/status/1971975841715572941?t=0ldID3p7wJFJq4wxNU-o8w&s=19
Malamin Addinin Islama, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayar da labarin garin da yaje aka masa dukan kawo wuka.
Saidai malam yace ya daina fadin garin saboda mutanan garin na cewa yana ja musu zagi da tsinuwa kuma an dade da yin abin.
Malam yace dan haka ya daina kiran sunan garin bayan gyaran da aka masa.
https://www.tiktok.com/@nurasara531/video/7554842961033432338?_t=ZS-9067c6ypuJl&_r=1
Malamin Addinin Musulunci, Dan Darika, Dr. Murtala Abubakar Argungun ya bayyana cewa, shi a wajensa babu Musulmi makiyin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Malam yace ko da wadanda basa Maulidi baya daukarsu a matsayin makiyan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) kawai dai akwai sabanin fahimta ne kan yanda ya kamata a girmama Annabi.
Wannan kalamai nasa sun jawo masa yabo sosai inda mutane ke cewa haka ya kamata a rika wa'azi.
https://www.tiktok.com/@drmurtalaabubakarargungu/video/7552325369139973394?_t=ZS-9061J3L3XIP&_r=1
Malamin Darika, Abdulfatahi Sani Tijjani ya bayyana cewa idan gwamnati ta kyale Sheikh Lawal Triumph bata hukuntashi ba.
Yace daliban Abdul Jabbar Zasu fito su nemi a sakeshi kuma Gwamnatin bata da hurumin ci gaba da rikeshi.
Hakanan yace wani ba zai taba Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) nan gaba ba a iya hukuntashi ba.
https://www.tiktok.com/@shaaweuei5p/video/7554541718335507730?_t=ZS-905UamenI3N&_r=1