Tuesday, March 3
Shadow
Kotu ta soke dokar aikin Soja a Najeriya da ta ce dole sai soja yayi shekaru 15 yana aiki kamin a yadda yayi ritaya, Kotun tace soja na da ikon ajiye aiki a duk sanda yake so

Kotu ta soke dokar aikin Soja a Najeriya da ta ce dole sai soja yayi shekaru 15 yana aiki kamin a yadda yayi ritaya, Kotun tace soja na da ikon ajiye aiki a duk sanda yake so

Duk Labarai
Kotun Ma'aikata dake da zama a Abuja National Industrial Court ta soke dokar aikin soja da tace sai soja ya shafe shekaru 15 yana aiki kamin a yadda yayi ritaya. Kotun tace wannan doka ta sabawa kundin tsarin mulki dannan ta take hakkin sojojin wanda kundin tsarin mulki ya basu sannan ta bayyana dokar da cewa kamar bautar da sojojin ake. Dan haka tace ta soke wannan doka kuma a ko wane lokaci sojan Najeriya zai iya yin ritaya ya ajiya aiki. Mai shari'a, Justice Emmanuel D. Subilim ne ya yi wannan hukunci bayan da sojan sama, Flight Lieutenant J. A. Akerele.ya shigar da kara saboda yana son ya ajiye aiki amma an hanashi. Sojan yace an ki yi mai karin girma sannan ana ta wahalar dashi a gidan sojan inda wanda suka fara aiki tare an musu karin girma amma shi ba'a mai ba. Yace d...
Wata Sabuwa: Hon. Magaji Yarima Madachi Daga Jihar Bauchi ya tura 100k a asusun Uwar gidan Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu domin taya ta murna cika shekara 65 a duniya.

Wata Sabuwa: Hon. Magaji Yarima Madachi Daga Jihar Bauchi ya tura 100k a asusun Uwar gidan Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu domin taya ta murna cika shekara 65 a duniya.

Duk Labarai
Hon. Magaji Yarima Madachi Daga Jihar Bauchi ya tura 100k a asusun Uwar gidan Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu domin taya ta murna cika shekara 65 a duniya. Hon. Magaji Yarima Madachi (Dan Sararin Madachi) ya shiga jerin dubban masoya kuma magoya bayan Sen Oluremi Tinubu ta hanyar bada tasa gudummawar domin karasa aikin National Library kamar yadda ta bukata. Shi dai wannan matashi ya kasance dan jam'iyyar APC kuma mai rajin tsayawa matasa domin a temakesu. Muna Allah san Barka da wannan yunkuri nasa. Daga Ahmad Khamisu Madachi.
Sai na rage wa Tinubu ƙuri’a miliyan guda a 2027 – Kabiru Marafa

Sai na rage wa Tinubu ƙuri’a miliyan guda a 2027 – Kabiru Marafa

Duk Labarai
Tsohon Ɗan Majalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa ya sha alwashin rage wa Tinubu ƙuri'u masu yawa a zaɓen 2027. Marafa, wanda a baya-bayan nan ya sanar wa BBC ficewarsa daga jam'iyyar APC, bayan ya zargi Tinubu da ''watsar da shi bayan cin zaɓe'' ya ce sai ya kawo wa shugaban ƙasar cikas a zɓen 2027 da ke tafe. Yayin wata hira da hgidan talbijin na Channels, Sanata Marafa ya ce sai ya janyo wa Tinubu asarar kimamin ƙuria' miliyan guda. Tsohon ɗan majalisar - wanda ya kasance babban daraktan yaƙin neman zaɓen Tinubu a Zamfara a 2027 - ya ce zai nuna wa shugaban ƙasar matsayinsa a siyasar jihar Zamfara.
Ban yi kuskure ba wajen zaɓen Kashim a matsayin mataimaki – Tinubu

Ban yi kuskure ba wajen zaɓen Kashim a matsayin mataimaki – Tinubu

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba da jajircewar mataimakinsa, Kashim Shettima, wanda ya bayyana da mutum mai amana da gaskiya da yake jin daɗin aiki da shi. A wata sanarwa da ya fitar kan taya mataimakin nasa murnar cika 59 a duniya, Tinubu ya ce, "tun da na sanka har zuwa yanzu, ba ka nuna gajiyawa wajen aiki tuƙuru domin sake gina ƙasarmu. A dukkan muƙaman da ka riƙe a baya, ka nuna jajircewa wajen aiwatar da abubuwan da suka dace duk runtsi duk wahala." Tinubu ya ce yana godiya bisa irin goyon bayan da yake samu daga Shettima, "lokacin da na zaɓe ka a matsayin mataimakina, na san ban yi zaɓen tumun-dare ba, na san na ɗauko nagartacce wanda Najeriya za ta yi alfahari da shi. Kullum a aikinka na mataimaki, kana ƙoƙari wajen kawo shawarwari da tsara sababbin abubuwa da za su taim...
Mun cimma yawan kudin shigar da muke bukata na gaba dayan shekarar 2025 a watan Augusta kuma ba ta hanyar Man fetur ba>>Inji Shugaba Tinubu

Mun cimma yawan kudin shigar da muke bukata na gaba dayan shekarar 2025 a watan Augusta kuma ba ta hanyar Man fetur ba>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, sun cimma yawan kudin shigar gaba dayan shekarar 2025 da ake bukata. Shugaban ya bayyana hakane a wajan wani taro inda yace kuma kudin ba ta bangaren man fetur suka zo ba. Yace kuma a yanzu Najeriya babu wani bankin cikin gida da yake binta bashi. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1962955483179839818?t=ZxXp8bt_-SseYE4CoIuhWA&s=19
Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai koma aiki nan da kwana 10 – Minista

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai koma aiki nan da kwana 10 – Minista

Duk Labarai
Ministan sufurin Najeriya, Sa'idu Ahmed Alkali ya ce nan da kwana goma jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da ya lalace zai koma aiki. A makon jiya ne dai jirgin ƙasan ya kauce hanya, inda ya tunsture a kusa da tashar Asham bayan ya taso daga Abuja zai tafi Kaduna ɗauke da mutum 618, ciki har da har da fasinja 583 da ma'aikatan jirgin ƙasan guda 15 da ma'aikacin jinya 1 da masu goge-goge 11, sannan aƙalla fasinja bakwai ne suka ji rauni. A wata ziyara da ministan sufurin ya kai wajen da jirgin ya kauce hanya a jiyar Litinin, ya yaba da ƙoƙarin jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da tsaron fasinjojin da sauran ma'aikatan jirgin har aka kwashe su. "A lokacin da jirgin ya tuntsure, jirgin yana tafiya ne da tarago guda bakwai. Tuni mun kwashe guda h...
Gwamnati ta bayyana jihohin arewacin Najeriya da za su iya fuskantar ambaliya a watan Satumba

Gwamnati ta bayyana jihohin arewacin Najeriya da za su iya fuskantar ambaliya a watan Satumba

Duk Labarai
Hukumar kula da madatsun ruwa ta Najeriya wato Nigeria Hydrological Services Agency (NiHSA) ta yi gargaɗin cewa aƙalla jihohin arewacin Najeriya guda 18 ne ke fuskantar barazanar ambaliya a mako biyu na farkon watan Satumban nan da aka shiga. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce jihohin Najeriya 29 ne tare da Babban Birnin Tarayya Abuja suke fuskantar barazanar ta ambaliya a tsakanin 1 zuwa 15 ga watan Satumba. Hukumar ta ce ambaliyar za ta iya shafar ƙananan hukumomi 107, da garuruwa 631, sannan aƙalla manyan titunan ƙasar 50 za su fuskanci tsaiko. Daga cikin jihohin da suka fi shiga barazanar, akwai Borno da Zamfara da Jigawa da Kebbi da Yobe da Filato da Gombe da Taraba da Sokoto, sannan akwai jihar Kaduna barazanar ba ta ƙarfi sosai.
Burkina Faso ta haramta auren jinsi

Burkina Faso ta haramta auren jinsi

Duk Labarai
Gwamnatin sojin Burkina Faso a ƙarƙashin jagorancin Faso Ibrahim Traore ta sanar da haramta auren jinsi a ƙasar baki ɗaya. Wannan na zuwa ne kimanin shekara guda bayan an amince da wani daftarin dokoki da aka yi garambawul a kan dokokin iyalin ƙasar, inda a ciki aka ƙara auren jinsi. Ƙasar da ke yankin Sahel ta kasance a cikin ƙasashen Afirka 22 a cikin 54 da suka amince da auren jinsi, lamarin da ke ɗaukar hukuncin kisa ko zaman gidan kaso mai tsaro a wasu ƙasashen. A jiya Litinin ne gwamnatin ƙasar ta amince da sabuwar dokar wadda ta haramta auren na jinsin. A sabuwar dokar, wanda aka kama da auren jinsi zai iya fuskantar zaman gidan yari na shekara biyar, kamar yadda ministan shari'a na ƙasar Edasso Rodrigue Bayala ya sanar a kafar gwamnatin ƙasar ta RTB. A bara ma dai ma...
Ban gaji Ko sisi daga mahaifina ba>>Inji Dangote

Ban gaji Ko sisi daga mahaifina ba>>Inji Dangote

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, bai gaji ko sisi daga hannun mahaifinsa ba. Ya bayyana hakane a wata tsohuwar hira da gidan jaridar Bloomberg suka yi dashi a shekarar 2020. Dangote yace bayan rasuwar mahaifinsa an bashi gadonsa amma sai ya kyautar da kudin, yace kuma yana alfahari da hakan. Sannan ya kara da cewa ya yiwa kawunsa aiki kadan inda daga baya ya bar Kano zuwa Legas inda ya fara sayar da sumunti Yace a wancan lokacin ana shigo da siminti ne cikin Najeriya.