Monday, December 15
Shadow
Masu fita daga PDP zama su dawo ne saboda jam’iyyar mu ce kadai zata iya kada Tinubu>>Inji Shugaban PDP

Masu fita daga PDP zama su dawo ne saboda jam’iyyar mu ce kadai zata iya kada Tinubu>>Inji Shugaban PDP

Duk Labarai
Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta gargaɗi ƴanƴanta da ke shirin shiga sabuwar haɗakar ADC. Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin amintattun jam'iyyar, shugaban jam'iyyar na ƙasa Amb. Iliya Damagum ya ce jam'iyyar za ta ɗauki tsattsauran mataki kan mambobinta da ke ƙoƙarin shiga haɗakar. Damagum ya ce ƙoƙarin da haɗakar ke shirin yi ba zai yi tasiri ba, yana mai cewa da dama daga cikin mambobin haɗakar za su koma jam'iyyunsu. “Yana da kyau su sani cewa babu inda ya kamata a haɗu domin tunkarar gwamnatin APC da ya wuce jam'iyyar PDP, amma in suna ganin ba haka ba, to su je su gwada su gani, amma dai na san dole za su dawo'', in ji shi. Shugaban riƙon ya kuma gargaɗi ƴan PDP da ya ce suna ƙoƙarin ''sayar da jam'iyyar''. Kawo yanzu dai akwai jiga-...
Dalilin da ya sa ake yi wa Buhari kallon shugaba mai jan ƙafa – Garba Shehu

Dalilin da ya sa ake yi wa Buhari kallon shugaba mai jan ƙafa – Garba Shehu

Duk Labarai
Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban Najeriya, Garba Shehu ya kare salon mulkin shugaba Muhammad Buhari. Malam Garba Shehu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Arise TV, inda ya amince da cewa duk da wani lokacin ana bayyana shugabancin Buhari da mai jan ƙafa amma ya ce hakan na faruwa ne sakamakon ƙoƙarinsa na bin ƙa'ida wajen aiwatar da al'amura a ƙoƙarinsa na sauyin da yake yi daga mulkin soji zuwa na farar hula. Sai dai kuma tsohon mataimakin na Buhari, ya ce ƴan Najeriya ba su da haƙuri kasancewar suna son sha yanzu magani yanzu ko da kuwa za a saɓa ƙa'idojin dimokraɗiyya. "Yana da jan ƙafa? E, shi ma da kansa ya kan yi barkwanci dangane da hakan. Kuma ya yawan faɗin hakan lokacin da ya hau mulki a matsayinsa na soja, yana yin abun da ya g...
NAHCON ta kammala jigilar alhazan Najeriya daga Saudiyya

NAHCON ta kammala jigilar alhazan Najeriya daga Saudiyya

Duk Labarai
Hukumar Alhazan Najeriya ta kamala jigilar alhazan ƙasar da suka sauke farali a aikin hajjin bana. Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kammala aikin kwaso alhazan daga ƙasa mai tsarki a yau Laraba 2 ga watan Yulin 2025. Kimanin alhazan Najeriya 41,291 ne suka sauke farali a wanan shekara, kamar yadda hukumar ta bayyana. Jirgin ƙarshe da ya ɗauko alhazan jihar Kaduna ya taso da safiyar yau.
Ya Bude Shagon Siyar Da Yajin Daddawa Bayan Ya Kammala Digiri A Jami’ar Bayero

Ya Bude Shagon Siyar Da Yajin Daddawa Bayan Ya Kammala Digiri A Jami’ar Bayero

Duk Labarai
Ya Bude Shagon Siyar Da Yajin Daddawa Bayan Ya Kammala Digiri A Jami'ar Bayero. Bayan kammala karatunsa na digiri daga jami'ar Bayero ta Kano bai tsaya jiran aiki ba ya buɗe shagon siyar da yajin daddawa a zamanance. Yanzu haka ya dauki ma'aikata a kasansa. Inda shagon nasa yake akan titin gidan zoo dake Kano. Ya kamata matasa su yi koyi da shi. Daga Dr.Yak'S
Sanata Kwankwaso Ya Kaiwa Sani Danja Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa

Sanata Kwankwaso Ya Kaiwa Sani Danja Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Sanata Kwankwaso Ya Kaiwa Sani Danja Ziyarar Ta'aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa.
Duk jam’iyyar da zaku koma ku koma, amma fa mulki ba zai taba komawa Arewa a 2027 ba>>Bode George ya gayawa su Atiku

Duk jam’iyyar da zaku koma ku koma, amma fa mulki ba zai taba komawa Arewa a 2027 ba>>Bode George ya gayawa su Atiku

Duk Labarai
Tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Bode George ya bayyana cewa mulki ba zai koma Arewa ba a shekarar 2027 ba sai shekarar 2031. Ya bayyana hakane a matsayin martani ga komawar su Atiku jam'iyyar ADC. Yace duk jam'iyyar da zasu koma su koma amma mulki ba zai koma Arewa ba. Bode George ya bayyana irin abinda Atiku yake yi da cewa ba na mutane wayayyu bane. Bode George yace idan mutum gidansa ya lalace ba gyarawa ya kamata yayi ba? Yace fitar su Atiku ta nuna kawai lokacin nasara da jin dadi suke so amma ba zasu iya daurewa lokacin wahala ba. Yace amma dai ko menene suka yi, masu zabene dai zasu yanke shawarar wanda suke son zaba.
Da Duminsa: Tsohon Ministan Ministan shari’a, Abubakar Malami ya bar jam’iyyar APC zuwa ADC

Da Duminsa: Tsohon Ministan Ministan shari’a, Abubakar Malami ya bar jam’iyyar APC zuwa ADC

Duk Labarai
Abubakar Malami, wanda ya yi Ministan Shari'a a mulkin Buhari, ya baiyana dacewar tasa ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu ya kuma wallafa a shafinsa na facebook. Ya ce gwamnatin APC ta gaza wajen magance matsalolin talauci da tsaro a karkashin gwamnatin Tinubu, inda ya ce gwamnatin ta fi maida hankali kan harkokin siyasa maimakon magance matsalolin ƙasa.