Wannan wata matashiyace data zargi wani mutum da shafa mata jiki a motar bass da suka hadu.
Tace babban abin takaici shine mutane na gani sun kasa cewa komai saidai su bata hakuri.
https://twitter.com/ChuksEricE/status/1999367727601823796?t=wHqrOQjnyIpO5cr8V59Xpw&s=19
Wannan matashiyar ta yi ikirarin cewa dan uwanta wanda soja ne an yanke masa hukuncin kisa shi da abokin aikinsa a gidan soja ta hanyar Ràtàyà.
Tace laifinsu kawai dan sun nemi a basu makamai masu kyau su yàqì Bòkò Hàràm.
https://twitter.com/Mazi_Chinonso1/status/1999143974020227561?t=m56PVuvjrISeK_z2A0G5Cw&s=19
Tauraron mawakin Najeriya, Davido ya yi waka da rawa a Jidda dake kasar Saudiyya.
Bidiyon ya nuna mutane sun taru sosai sun kalli wasan na Davido.
https://twitter.com/hypetribeng/status/1999271976670757116?t=ZYxBXsQhhWCbYgvfGa173w&s=19
A baya kamin wasan, An ga Davido sanye da jallabiya yana Larabci.
Yace yama canja suna zuwa Dauda.
Fitsararriyar mawakiyar Amurka, Cardi B ta bayyana cewa ita mutuniyar kirki ce.
Tace bata shan giya kuma tana bin doka.
Ta bayyana hakane yayin da take shirin zuwa kasar Saudiyya yin waka.
Lamarin ya jawo cece-kuce da yi mata dariya da shagube.
https://twitter.com/mymixtapez/status/1999160605308035422?t=iAXjrIfLj-sn5EHvrKy1_w&s=19
Wani Bidiyo na 'yansandan Najeriya da suka nuna yanda suke shiga daji da yaki da masu garkuwa da mutane ya jawo cece-kuce.
Da yawa dai sun ce abin yayi kama da fim.
https://twitter.com/ChuksEricE/status/1999080320428339641?t=99-y-JHbHwFR9O3IgpJPKg&s=19
An rika musu barkwanci da zunde.
Karamin Ministan Tsaro, Matawalle Ya Maka Sheik Murtala Asaada A Kotu Kan Zargin Alakanta Shi Da Ta'aďdànçì.
Rahotanni nata yawo cewa Ministan ya maka Malam Assada a kotu ne biyo bayan zarge-zargen da ya dade yana masa akan hannu a ta'addancin dake faruwa musaman a jihar Zamfara.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, ta tsare tsohon ministan ƙwadago kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Chris Ngige.
Mai magana da yawun Ngige, Fred Chukwuelobe, ya tabbatar da tsare shi da safiyar ranar Alhamis, bayan wasu rahotanni da aka yaɗa cewa an sace shi.
Chukwuelobe ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Ngige yana tare da EFCC. Ba a sace shi ba.”
Har zuwa yanzu, EFCC ba ta bayyana dalilin tsare Ngige ba amma kuma ana sa ran hukumar za ta fitar da cikakken sanarwa kan tsare shi da binciken da take yi a kansa.
Ngige ya zama mutum na biyu daga cikin tsoffin ministocin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da aka tsare a kwanan nan. Kafin shi, an fara tsare tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, wanda shima yake hannun EFCC.
Shekara goma kenan tun bayan kisan da jami’an sojin Najeriya suka yi wa mabiya mazhabar Shi’a a garin Zaria na jihar Kaduna.
A wancan lokaci an yi amanna ɗaruruwan mutane ne suka mutu, da dama kuma suka jikkata, bayan zargin rundunar soji cewa mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun tare musu hanya.
Lamarin ya haddasa suka daga kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na duniya, waɗanda suka zargi sojoji da amfani da ƙarfi fiye da kima.
Shugaban dandalin tattauna al’amura naƙkungiyar mabiya Shi’a ta IMN a Najeriya, Farfesa Abdullahi Danladi, ya ce duk da wucewar shekaru goma tun bayan faruwar wannan mummunan lamari, har yanzu ba za su taɓa yafe wa waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin ba.
A tattaunawarsa da BBC, Farfesan ya ce raɗadin abin da ya faru na ci gaba da sosa zuƙatan al’ummar Sh...
Venezuela ta zargi Amurka da sata karara da kuma fashin teku bayan da dakarun Amurkan suka kwace wani jirgin ruwa na dakon mai a gabar tekun Venezuela din.
Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce matakin wani shiri ne na lalata arzikin makamashi na Venezuela da gangan.
Sai dai jami'an Amurka sun ce jirgin ruwan yana safarar man da aka sanya takunkumin sayar da shi ne zuwa Iran kuma kudin da ake samu daga cinkin ana taimaka wa kungiyoyin ta'addanci ne.
https://twitter.com/AGPamBondi/status/1998875795151024337?t=ucDi6xifDOsVYsbJydJHJQ&s=19
Lamarin ya kasance ƙarin wata sabuwar dambarwa ta matsin lambar da Amurka ke yi wa shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro - mai ra'ayin gurguzu.
Mai dai shi ne babbar hanyar samun kudade na kasar ta Venezuela