Bayanan Sirri da suka fito na karawa Dogarin shugaba Tinubu Mukami sun jawo cece-kuce sosai
Bayanan sirri sun fito da suka bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince a karawa dogarinsa mukami zuwa Brigadier General.
Sannan kuma a barshi ya ci gaba da gadinsa, kamar yanda wata wasika da Nuhu Ribadu ya aikawa shugaban sojoji ta bayyana.
An dai bayyana cewa, Wasikar ta sirri ce, saidai zuwa Yanzu Gwamnati bata ce uffan ba akanta.
Rahotanni dai sun ce idan hakan ta tabbata to an saba doka domin za'awa dogarin na shugaba Tinubu karin mukami ne fiye da sauran abokan karatunsa.








