Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid wanda aka fi sani da Digital Imam ya bayyana cewa, 'yan Darikar Sufaye su suka fi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Malam yace abin ba zai yiwa wasu dadin ji ba amma dole a fadi gaskiya.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda yace asalin Sufaye sun samo asaline daga Zuhudu, watau Gudun Duniya.
https://www.tiktok.com/@shaaweuei5p/video/7557941385383496967?_t=ZS-90JnomaD6XY&_r=1
Tauraron mawakin Batsa, wanda yace ya tuba daga wakokin batsa da yake yi a baya, 442 ya musuluntar da baturiyar da suke waka tare.
A baya, Hutudole ya kawo muku yanda 442 ya nakaltawa Baturiyar kalmar Shahada inda ta karbi Musulunci.
A yanzu kuma, 442 ya koya mata yanda ake Sallah
An ga 442 yana limanci yayin da baturiyar ke binsa a baya.
https://www.tiktok.com/@mr442_/video/7557848257540476167?_t=ZS-90Jlt9cmLFB&_r=1
Rahotanni sun ce duk da Dangote na daukar man fetur din da gidajen mai suka siya da tankokin motocin sa yana kai musu kyauta.
Har yanzu gidajen man basu rage farashin man fetur din da suke sayarwa ba.
An yi tsammanin tunda babu kudin dakon mai da gidajen man fetur din ke biya, Dangote na kai musu kyauta da tankokinsa, farashin man da suke sayarwa zai sakko kasa.
Saidai hakan bata faru ba inda hadda gidan man MRS wanda shine yafi kusa da Dangote wanda suka yi hadaka, shima a wasu wajajen farashin litarsa na kaiwa har Naija 875, kamar yanda jaridar Punchng ta ruwaito bayan yin zagaye ta ga yanda ake sayar da mai a gidajen man.
An sake ganin Tauraruwar Tiktok, wadda a baya ke yin Bidiyo da Hijabi amma aka ganta da su Soja Boy suna rawa wadda bata dace ba ta sake yin sabon Bidiyo da Soja Boy din.
A wannan karin ma an ga Iftihal Madaki na rawa tare da Soja Boy ba Hijabi.
Lamarin ya kara tabbatarwa da mutane cewa lallai itace domin kuwa ta wallafa Bidiyo a shafinta na Tiktok suna wakar tare da Soja Boy.
https://www.tiktok.com/@bigdoxxx/video/7557856750192446721?_t=ZS-90JecHofmGu&_r=1
https://www.tiktok.com/@iftih_al/video/7557864109241339157?_t=ZS-90JfgT1BQET&_r=1
Malam Abdulfatahi Sani Tijjani ya ce ya amince da gayyatar mukabala daga kungiyar Izala.
Saidai yace ba zai zauna da kananan malamai ba.
Yace a tura masa ko dai Guruntum ko kuma Sheikh Sani Rijiyar Lemu, yace yana son wadanda idan ya doke su asan ya doke Izala.
Yace kamar yanda suka buga da marigayi Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya dokeshi haka yake son sake bugawa da wani babban malamin Izala shima ya gama dashi.
https://www.tiktok.com/@habibou.adamou..227/video/7557329579254254904?_t=ZS-90IzP4iQzzN&_r=1
Tauraron Tiktok, G-Fresh Al-amin ya bayyana cewa, duk Duniya ba garin da yake so fiye da Kano amma Kano ba zata zauno masa ba.
Ya bayyana hakane inda ake bayar da misali da kamen da kawa Mai Wushirya.
G-Fresh yace Mai Wushirya na can a hannu bayan da yawa Gurguwa Kiss.
Ya kuma saka Bidiyon Soja Boy da yake cewa Babu malamin da zai halasta maka rawa da waka.
Inda G-Fresh yace Nishadantarwa kawai suke.
https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7557472377332960530?_t=ZS-90IyDWhwPhJ&_r=1
Tauraron mawaki, 442 ya baiwa Baturiya da suke waka tare kalmar Shahada.
A wani Bidiyo da ya wallafa a shafinsa an ganshi yana fadar kalmar shahada baturiyar na maimaitawa.
https://www.tiktok.com/@mr442_/video/7557805376108891400?_t=ZS-90IxGZDwi9J&_r=1
A baya dai 442 ya bayyana cewa baturiyar na son karbar Kalmar shahada inda lamarin yaso ya kawo cece-kuce.
'Yar arewa tilo kuma musulma da ke cikin shirin BBNaija, Watau Sultana a karshe an koreta daga gidan BBNaija din a Yau.
Hakan na zuwane bayan da ta nuna tsiraici kuma ta yi rashin kunya kala-kala a gidan BBNaija din.
Wasu sun bayyana jin dadinsu yayin da wasu kuma suka nuna rashin jin dadin korar Sultana
Bidiyon yanda Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya rungumi wata kawarsa a gaban matarsa ya dauki hankula.
Abinda ya kara daukar hankalin mutane shine yanda aka ga alamar kamar matar bata damu ba.
Hakan ya jawo zazzafar muhawara.
https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7556709628961148168?_t=ZS-90Ijk0dR9Dk&_r=1