An watan sabuwar shekarar musulunci ta 1447 bayan hijira a Saudiyya.
Cikin wani saƙo da shafin Haramain na Saudiyya ya wallafa ya ce an ga watan da maraicen yau Laraba 25 ga watan Yuni.
Hakan na nufin shekarar 1446 ta zo ƙarshe wannan rana a ƙasar ta Saudiyya.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ce gatan 'yan Najeriya inda yace kada su saurari masu cewa zasu kayar dashi zabe a 2027.
Shugaban yace 'yan adawar dake hada kai da zummar kayar dashi zabe 'yan gudun hijirar siyasa ne.
Shugaban ya bayyana hakane ranar Laraba a yayin ziyarar da ya kai jihar Nasarawa ta kwana daya.
Ya yabawa gwamnan jihar, Abdullahi Sule kan aikin da yakewa mutanen jiharsa inda yace zai tallafa masa da dukkan wani aikin ci gaba da zai kawo.
An Samu Wasu Marasà Tausayì Sun Jefa Wannan Dattìjò Cikin Zulumi, Inda Aka Biyo Dare Aka Kwashe Masa Kan Kekunan Dinkin Da Yake Lallaba Rayuwarsa Da Su
Lamarin dai ya auku ne a yankin Bakin Dogo Samaru dake Zaria.
WATA SABUWA: Masu Kwàcen Waya A Kano Sun Koma Kwacen Huluna, Agogo Da Azurfa Masu Tsada.
A Kano saboda an fara barin waya a gida kafin a fita bakin aiki ko sana'a, yanzu masu kwacèñ waya sun fara cire hula da zobunan azurfa na mutane saboda sun ji kudin da ake siyan su da tsada.
Allah Ya kawo mana karshen wannan màsìfa.
Daga Sani Siro
A yau, Alhamis ne ake sa ran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai sakawa sabbin kudirin dokokin Haraji hannu a fadarsa dake Abuja.
Hakan na kunshene cikin sanarwar da kakakin shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar.
Kudirin dokokin guda 4 ne wanda tuni majalisar tarayya ta amince dasu bayan cece-kuce da suka jawo sosai.
Shuwagabannin majalisar tarayya da shuwagabannin kungiyoyin gwamnoni da ministan kudi da sauran manyan ma'aikatan Gwamnati ne zasu shaida wannan lamari a fadar shugaban kasar kamar yanda sanarwar ta tabbatar.
TIRƘASHI: Ba zan goyi bayan Tinubu ba idan ya sauke Shettima – Sheikh Jingir.
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Nijeriya Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce ba zai goyi bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ba, idan har Tinubu ya sauya mataimakinsa, Kashim Shettima.
Jingir ya bayyana cewa matsayar shi ita ce goyon baya ga Tinubu–Shettima ne kawai. Idan Tinubu ya yanke shawarar sauya Shettima da wani daga cikin mataimakinsa.
Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga Yuni, 2025, a matsayin hutu domin shiga Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447 Hijira.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma taya al’ummar Musulmi murna bisa samun damar ganin sabuwar shekarar, wadda ke farawa da watan Muharram – watan farko a kalandar Musulunci ta hijira.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a yau Laraba.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da kuma Musulmi gaba ɗaya da su yi duba kan ayyukansu na shekarar da ta gabata, tare da amfani da wannan dama domin yin addu’o’i na zaman lafiya, haɗin kai da cigaba a jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da kudirin dokoki 2 na kafa makarantar nakasassu da kuma asibitin kashi a jihar Gombe.
Majalisar Dattijai ta jinjinawa shugaban kasan kan wannan yunkuri wanda tace zai habbaka harkar ilimi da kiwon lafiya.
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a yayin zaman majalisar Dattijai na ranar Laraba.
Za'a gina makarantar nakasassun ne a karamar hukumar Dukku dake jihar.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, gajarta ce tawa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yawa shiyasa yake ta soki burutsu.
Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga.
El-Rufai a wata hira da aka yi dashi yace a wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da suka gudanar sun gano cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai ci zaben shekarar 2027 ba.
Saidai Onanuga yace babbar matsalar El-Rufai shine shi a ko da yaushe yana son ya nuna yafi sauran mutane.
Yace El-Rufai bashi da biyayya inda yawa mutane da yawa a baya ciki hadda wansa wanda tsohon soja ne.
Yace kuma makaryaci ne sosai wanda ke yin abubuwa yawanci dan kawai amfanin kansa.
A karin farko a tarihi, Musulmi me suna Zohran Mamdani ya lashe zaben fidda gwani na tsayawa takarar magajin garin birnin New York City dake kasar Amurka.
Zohran ya lashe zabenne a karkashin jam'iyyar Democrats inda ya doke tsohon gwamnan Jihar ta New York, Andrew Cuomo.
Zohran dan shekaru 33 ne kuma dan majalisa ne a Queens dake New York din.
A yanzu dai zai jira zuwa watan Nuwamba inda za'a gudanar da ainahin zaben dan ganin wanene zai zama magajin garin na Birnin New York City.
Saidai tuni yahudawan dake birnin suka ce zasu fice daga birnin sanoda nuna kiyayya ga Zohran.
Kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa, Zohran yace idan ya zama magajin garin New York City, toh lallai duk sanda Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu ya shiga birnin zai kamashi.