Wednesday, March 4
Shadow
Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara

Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami'o'i masu zaman kansu guda tara a faɗin Najeriya. Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, bayan taron majalisar zartarswa ta ƙasa da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja. Ya ce jami’o’in da aka amince da su sun haɗa da: Jami’ar Tazkiyah da ke jihar Kaduna Jami’ar Leadership da ke babbar birinin tarayya, Abuja Jami’ar Jimoh Babalola a jihar Kwara Jami’ar Bridget, Mbaise a jihar Imo Jami’ar Greenland da ke jihar Jigawa Jami’ar JEFAP a jihar Neja Jami’ar Azione Verde da ke jihar Imo Jami’ar Unique Open a Jihar Legas Jami’ar American Open da ke Jihar Ogun Alausa ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaji buƙatu 551 ...
Tinubu zai yi tafiya zuwa ƙasashen Japan da Brazil

Tinubu zai yi tafiya zuwa ƙasashen Japan da Brazil

Duk Labarai
Tinubu zai yi tafiya zuwa ƙasashen Japan da Brazil. Shugaba Bola Tinubu zai kai ziyara zuwa ƙasashe biyu, Japan da Brazil a yau Alhamis, 14 ga watan Agusta. Bayo Onanuga, mashawarcin shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya ce Tinubu zai tsaya a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), kafin ya zarce zuwa Japan. Ana sa ran shugaban zai halarci taron ƙasa da ƙasa na tara kan ci gaban Afirka (TICAD9) a birnin Yokohama na ƙasar Japan daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta. Onanuga ya ce Tinubu zai kuma gudanar da tarukan tattaunawa tsakanin ƙasashe da kuma ganawa da shugabannin manyan kamfanonin Japan da ke da hannun jari a Najeriya. “Bayan kammala taron TICAD9, Shugaba Tinubu zai tafi birnin Brasilia, babban birnin Ƙasar Tarayyar Brazil, domin ziyar...
Kalli Bidiyon da Rahama Sadau ta wallafa da yasa ake ta tunanin Ko Ali Jita ne ta aura

Kalli Bidiyon da Rahama Sadau ta wallafa da yasa ake ta tunanin Ko Ali Jita ne ta aura

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta wallafa Bidiyon wakarta da Ali Jita a shafinta na sda zumunta bayan daura aurenta. Hakan yasa da yawa suka rika tunanin ko dai Ali Jita dinne ta aura? kalli Bidiyon anan Cece-kuce da kaguwar ganin waye Mijin Rahama Sadau ya karade kafafen sada zumunta inda aka rika yada hotunan mutane daban-daban ana cewa sune suka aureta.
Kungiyar Yan Kwallon kafa Mata na Najeriya sun koka da cewa, har yanzu ba’a kai ga basu dala $100,000 da shugaba Tinubu ya ce ya basu ba

Kungiyar Yan Kwallon kafa Mata na Najeriya sun koka da cewa, har yanzu ba’a kai ga basu dala $100,000 da shugaba Tinubu ya ce ya basu ba

Duk Labarai
Kyaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta ce har yanzu ba a ba su dala 100,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi musu alƙawari bayan sun lashe gasar WAFCON a ƙasar Maroko ba. Ajibade, ta bayyana takaicinta game da jinkirin biyan kuɗin da aka musu alƙawari. “Ba mu karɓi kuɗin ba tukunna, amma ina fata za a biya mu. Duk alƙawuran da aka mana, yanzu dai ba mu samu komai ba.” Ajibade ta jagoranci tawagar zuwa ga nasara, inda suka sake lashe kofin WAFCON a bana. Bayan nasarar, Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan da masu horar da su lambar yabo ta ƙasa (Officer of the Order of Niger – OON). Haka kuma ya yi musu alƙawarin bai wa kowannensu dalar Amurka 100,000 da gida mai ɗaki uku. Lokacin da ya karɓe su a Fadar Shugaban Ƙasa, Tinu...
Gaskiya Sheikh Maqari yayi, Haka ya kamata kowane malami ya kasance, Ya kamata ace ana sabunta Addinin Musulunci, yayi daidai da Zamani>>Inji Gfresh bayan da Sheikh Maqari ya fashi fatawar zai iya ci gaba da yin Bidiyo da matarsa

Gaskiya Sheikh Maqari yayi, Haka ya kamata kowane malami ya kasance, Ya kamata ace ana sabunta Addinin Musulunci, yayi daidai da Zamani>>Inji Gfresh bayan da Sheikh Maqari ya fashi fatawar zai iya ci gaba da yin Bidiyo da matarsa

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya jinjinawa baban Malamin Addinin Islama, Sheikh Ibrahim Maqari bisa fatawar da ya bashi cewa, yana iya ci gaba da yin Bidiyo da matarsa yana dorawa a kafar sada zumunta. Gfresh yace haka ya kamata kowane malami ya kasance sannan yayi kira da a rika samunta addinin musulunci yana zama daidai da zamani. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7537791495114427654?_t=ZS-8yrwYYVVdHU&_r=1 Gfresh ya kuma yi kiran cewa ya kamata a a daina zagin malamai inda yace shi kome za'a fada akansa a fada amma a daina zagin malamai. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7538191754055535877?_t=ZS-8yrui0O6ino&_r=1
Zan Iya Shiga Mummunan Yanayi Idan Dangote Bai Aure Ni Ba, Saboda Tsananin Son Da Nake Yi Masa, Cewat Aishatu Haruna

Zan Iya Shiga Mummunan Yanayi Idan Dangote Bai Aure Ni Ba, Saboda Tsananin Son Da Nake Yi Masa, Cewat Aishatu Haruna

Duk Labarai
Zan Iya Shiga Mummunan Yanayi Idan Dangote Bai Aure Ni Ba, Saboda Tsananin Son Da Nake Yi Masa, Cewat Aishatu Haruna. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} ….har ta buga katin aurenta da shi Wata ’yar siyasa a jihar Bauchi mai suna Aishatu Haruna, ta ce ta shafe shekaru shida tana dakon soyayyar attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote a ranta, inda ta ce za ta iya shiga mummunan hali idan bai aure ta ba. Ta ce sau uku tana yin mafarkin ta aure shi, kuma ba ta jin za ta iya auren wani ba shi ba a duniya. A...
Farfesa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya jewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal jajen kamen da EFCC suka masa

Farfesa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya jewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal jajen kamen da EFCC suka masa

Duk Labarai
Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya jewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal jajen kamen da EFCC suka masa. An ga Malam a gidan Sanatan dake Abuja inda aka ga sauran manyan 'yan siyasa a gidan. Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya shafe kwana daya a tsare a hannun EFCC kamin daga baya suka sakeshi. Jam'iyyar ADC ta yi zargin cewa kamun yunkuri ne na dakile karfin 'yan Adawa.
Gwamnatin Tinubu ta dakatar da gina sabbin makarantun Jami’a na tsawon shekaru 7 inda tace akwai makarantun jami’a da malamai sun fi dalibai yawa

Gwamnatin Tinubu ta dakatar da gina sabbin makarantun Jami’a na tsawon shekaru 7 inda tace akwai makarantun jami’a da malamai sun fi dalibai yawa

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta dakatar da gina sabbin makarantun jami'a na tsawon shekaru 7. Gwamnatin tace makarantun da ake dasu a yanzu wasu malamai sun fi dalibai yawa, wasu ma ba'a neman shigarsu. An dauki wannan mataki ne a zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba wanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jagoranta. Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya tabbatar da hakan inda yace maimakon gina sabbin jami'o'in, Gwamnati zata mayar da hankali ne wajan gyara wadanda ake dasu da kuma daukar malamai kwararru.