Thursday, March 5
Shadow
Iyayen dalibai na neman a soke jarabawar WAEC saboda yanda aka fadi da yawa

Iyayen dalibai na neman a soke jarabawar WAEC saboda yanda aka fadi da yawa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, iyaye na neman a soke jarabawar WAEC ta bana saboda yanda aka fadi jarabawar da yawa. Ba iyayen kadai ba hadda kungiyar dalibai ta kasa, NANs ta bayyana rashin jin dadi kan sakamakon jarabawar na bana. Sun bayyana musamman damuwa ga jarabawar Turanci wadda aka rubutata a lokuta marasa dadi. Jarabawar ta bana dai an ga yanda aka rika rubuta wasu jarabawowin a cikin duhu. Shin ko WAEC zata yadda da wannan kira? Saidai a jira a gani.
YANZU-YANZU: Kotu ta bada belin Ghali Isma’il Abdullahi (Sultan) da jami’an tsaro na farin kaya DSS suka kama a ƴan kwanakin baya bisa zargin cewa Tinubu bãșhi da lafiya

YANZU-YANZU: Kotu ta bada belin Ghali Isma’il Abdullahi (Sultan) da jami’an tsaro na farin kaya DSS suka kama a ƴan kwanakin baya bisa zargin cewa Tinubu bãșhi da lafiya

Duk Labarai
Kotu ta bada belin Ghali Isma’il Abdullahi (Sultan) da jami’an tsaro na farin kaya DSS suka kama a ƴan kwanakin baya bisa zargin cewa Tinubu bãșhi da lafiya. tun farko dai an kama Sultan ne saboda wani Bidiyo da ake zarginsa da wallafawa a shafinsa na Tiktok. Zargin da ake masa akwai na tunzura mutane akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
DA ƊUMI-ƊUMI: Alhaji Atiku Abubakar Ya Dauki Nauyin Karatun ‘Yan Matan Arewa Da Suka Yi Bajinta A Gasar Turanci Ta Duniya Da Aka Gudanar A Birnin Landan

DA ƊUMI-ƊUMI: Alhaji Atiku Abubakar Ya Dauki Nauyin Karatun ‘Yan Matan Arewa Da Suka Yi Bajinta A Gasar Turanci Ta Duniya Da Aka Gudanar A Birnin Landan

Duk Labarai
Alhaji Atiku Abubakar Ya Dauki Nauyin Karatun 'Yan Matan Arewa Da Suka Yi Bajinta A Gasar Turanci Ta Duniya Da Aka Gudanar A Birnin Landan Atiku zai dauki nauyin karatunsu har zuwa jami'a a duk inda suka ga daman yin karatun karkashin gidauniyarsa na Atiku Abubakar Foundation Wane fata zaku yi masa?
‘Ba za mu ɗamunci ɗabi’ar da za ta taɓa ƙimar gwamnatinmu ba’

‘Ba za mu ɗamunci ɗabi’ar da za ta taɓa ƙimar gwamnatinmu ba’

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi masu riƙe da madafun iko a gwamnatinsa. A lokacin taron majalisar zartarwar jihar, Abba gida-gida ya buƙaci mambobin majalisar zartarwarsa su yi aiki bisa ƙwarewa da mutunta aikinsu. Gargaɗin na zuwa ne bayan ritayar kwamishinan sufuri na jihar, Ibrahim Namadi kan zarginsa da hannu a belin Danwawu, mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar. “Bari na gaya muku gaskiya, ba za mu lamunci duk wata ɗabi'ar da za ta taɓa ƙimar gwamnatinmu ba, don haka dole kowane mai riƙe da muƙami ya lura da kyau kan abubuwan da zai yi,'' in ji shi. Gwamnan ya ce masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa ba ofishinsu kawai sukee wakilita ba, suna wakiltar duka gwamnatin ne. ''Mun zo gwamnati ne da nufin tsaftace tarbiyya da inganta rayuwar al...
Ana tsare da Sowore cikin tasku da cin zarafi – Lauyoyinsa

Ana tsare da Sowore cikin tasku da cin zarafi – Lauyoyinsa

Duk Labarai
Lauyoyin ffitaccen ɗan gwagwarmayar nan kuma ɗan jarida, Omoyele Sowore da hukumomin ƙasar ke tsare da shi ya yi kiran sakinsa cikin gaggawa. Lauyoyin sun yi zargin cewa ana tsare da Sowore ƙarƙashin kulawar babban sifeton ƴansandan ƙasar, cikin hali maras kyau na tasku da cin zarafinsa, lamarin da suka ce yana barazana ga kariyarsa. A ranar Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan da ya amsa gayyatar jami'an ƴansanda domin amsa wasu tambayoyi. Ɗaya daga cikin lauyoyin nasa da ya zanta da sashen Pidgin na BBC, Marshal Abubakar ya ce an gayyacci Sowore ne kan zarge-zargen laufukan bata suna da yin ƙaryar takardun ƴansanda. Ya ce ƴansanda sun nuna musu wasu takardu na ƙorafi da aka rubuta kan Soworen, yana mai zargin ƴansanda da rubuta ɗaya daga ciki ƙorafe-ƙorafen. ...
Da Duminsa: ‘Yansanda sun gano Bama-Bamai da aka ajiye a cikin Bola a Kaduna

Da Duminsa: ‘Yansanda sun gano Bama-Bamai da aka ajiye a cikin Bola a Kaduna

Duk Labarai
Rahotanni daga Kaduna na cewa 'yansandan jihar sun gano wani bam da aka ajiyeshi a Bola a jihar. Kakakin 'Yansandan jihar, Mansir Hassan ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar. Yace an gano bam dinne a cikin wasu karikitai irin na masu jari bola a wani kanfanin sarrafa kayan bolar dake unguwar Kudenden. Yace Bom din na cikin karikitan bola ne da aka dauko daga Borno zuwa Kaduna. Yace tuni 'yansanda na musamman da suka iya kwance bom suka je wajan. Yace bayan bincike an tabbatar da cewa, bam ne wanda bai tashi ba a cikin karikitan. sannan an gano jarin makamai da suka hada da Bindiga da albarusai. Yace an kulle kamfanin har sai an kammala kawar da kayan makaman.
Akwai yiyuwar Najeriya zata tarwatse kamin shekarar 2027>>Inji Nwodo

Akwai yiyuwar Najeriya zata tarwatse kamin shekarar 2027>>Inji Nwodo

Duk Labarai
Tsohon Ministan yada labarai kuma tsohon shugaban kungiyar kare muradun Inyamurai, Chief John Nnia Nwodo yayi gargadin Najeriya na iya tarwatsewa kamin shekarar 2027. Ya bayyana hakane a Abuja wajan kaddamar da wani littafin a dakin taro na Shehu Musa 'Yar'adua ranar Laraba. Nwodo yace tsarin da ake kai ba zai kai Najeriya ga ci ba, yace dole a canja fasalin kasarnan. Ya bayyana cewa a canja kundin tsarin mulki kowane yanki a bashi dama ya rika cin gashin kansa yana biyan gwamnatin tarayya haraji. Yace amma idan ba haka ba, wasu yankin ba zasu yi zabe ba sannan wasu zasu nemi ballewa daga Najeriya.
Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya amince ya tsaya takarar shugabab kasa a shekarar 2027

Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya amince ya tsaya takarar shugabab kasa a shekarar 2027

Duk Labarai
2027: Jonathan zai tsaya takarar shugaban ƙasa don fafatawa da Tinubu. Tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya amince da tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027, in ji wani amintaccen na jikinsa da ke cikin jam’iyyar PDP. Vanguard ta rawaito cewa na jikin ma Jonathan ya ce, an kai matakin karshe wajen shawo kan Jonathan da ya tsaya takara domin farfaɗo da tattalin arziki da rage wahalhalun jama’a. Majiyar ta bayyana cewa shirin dawowar Jonathan yana samun goyon bayan manyan shugabanni da dattawan ƙasa waɗanda suka yarda cewa mulkinsa na baya ya kwantar da tarzoma kuma ya daidaita tattalin arziki. An bayyana cewa Jonathan ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya), da kuma wasu manyan 'yan siyasa na Arewa da Kudancin ƙasar don neman goyon b...