Kano: Shugaban ƙaramar hukumar Wudil ya ɗauki nauyin ɗalibai mata 33 su karanci ilimin ungozoma
Shugabann karamar hukumar Wudil, Abba Muhammad Tukur ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai mata 33 domin su karanci aikin ungozoma, da nufin inganta lafiyar mata masu juna-biyu a yankin.
Bayan daukar nauyin karatun nasu har su kammala, Tukur ya mikawa ɗaliban takardar samun gurbin karatu ta kwalejin koyar da harkokin aikin ungozoma da ke Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran shugaban karamar hukumar, Nura Mu'azu Wudil ya sanyawa hannu, inda ya ce qannan kuma kari ne kan ɗalibai mata 10 da tuni suka fara karatun.
Sanarwar ta ce, Tukur ya duba muhimmancin ilimin ƴaƴa mata, inda ya kara da cewa, hakan ne ya sa ya ware kudade masu yawa don ba su Ilimi da kuma kawo karshen yawan samun mutuwar mata masu dauke da juna biyu.
Tukur, a cewar Sakataren, ya...








