Tuesday, December 23
Shadow
‘Yansanda a jihar Kano sun kama barayin a daidaita sahu su 4, an kwato keke Napep din sata 6 a hannunsu

‘Yansanda a jihar Kano sun kama barayin a daidaita sahu su 4, an kwato keke Napep din sata 6 a hannunsu

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan jihar Kano sun kama barayin a daidaita su 4. Kuma an kwato Keke Napep din sata guda 6 a hannunsu. Kakakin 'yansandan jihar, DSP Hussaini Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar yau Alhamis. Yace a ranar 17 ga watan Yuni sun samu bayanan sirri kan wasu barayin adaidaita Namiji da mace, Auwal Mohammed, 'm', 30 wanda ke zaune a Hotoro, sai kuma Maryam Ibrahim, 'f', 25 wadda 'yar jihar Bauchi ce. Yace sun baiwa wani me adaidaita, Shu'aibu Aliyu kwaya suna kokarin kwace masa Keke Napep dinsa amma zuwan 'yansanda yasa basu yi nasara ba. Yace da bincike yayi tsanani an gano wani me suna Suleiman Lawal, wanda aka fi sani da Aljan da kuma Muhammad Tajuddeen, 'm', 32 wanda suke aiki tare dasu. Yace an kwato a daidaita 6 daga hannunsu kuma...
Najeriya ce ta daya wajan yawan mutanen da basu samun wutar lantarki a Duniya>>Inji Bankin Duniya

Najeriya ce ta daya wajan yawan mutanen da basu samun wutar lantarki a Duniya>>Inji Bankin Duniya

Duk Labarai
A sabon rahoton sa na shekarar 2025, bankin Duniya ya bayyana cewa, 'yan Najeriya Miliyan 86.8 ne ke cikin duhu basa samun wutar Lantarki a Najeriya. Bankin yace wannan shine mutane mafiya yawa da ya zarta na kowace kasar Duniya. Rahoton yace a cikin kasashen 20 da basa samun ingantacciyar wutar lantarki, guda 18 na Afrika ne. Rahoton yace kaso 60 cikin 100 na 'yan Najeriya ne ke samun wutar lantarki sannan kaso 26 cikin 100 na 'yan kasar ne ke amfani da makamashi me tsafta na girki.
Zan cika duka alkawuran da nawa ‘yan Najeriya >>Shugaba Tinubu

Zan cika duka alkawuran da nawa ‘yan Najeriya >>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa zai cika duka alkawuran da yawa 'yan Najeriya. Ya bayyana hakane a ziyarar aiki da ya kai jihar Nasarawa. Shugaban kuma ya bayar da tabbacin baiwa jihar Nasara gudummawar da take bukata wajan ci gaba musamman ta fannin ma'adanai da noma. Ya bayyana hakane yayin ziyarar da ya kaiwa Sarkin Lafiya,Sidi Bage Muhammad sannan ya jinjinawa Gwamna Abdullahi Sule game da ayyukan ci gaba da yayi a jihar.
Matar tsohon gwamnan jihar Kebbi Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ta sanar da ɗaukar nauyin duk wata waƙa da za a samu wanda zai yi a matsayin martani ga wadda mawaƙi Ali Jita ya yi ta “Uwargida”

Matar tsohon gwamnan jihar Kebbi Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ta sanar da ɗaukar nauyin duk wata waƙa da za a samu wanda zai yi a matsayin martani ga wadda mawaƙi Ali Jita ya yi ta “Uwargida”

Duk Labarai
Da Ɗumi-Ɗumi Matar tsohon gwamnan jihar Kebbi Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ta sanar da ɗaukar nauyin duk wata waƙa da za a samu wanda zai yi a matsayin martani ga wadda mawaƙi Ali Jita ya yi ta “Uwargida”. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dr. Zainab wadda ita ce amarya ga tsaron gwamnan wanda a yanzu shi ne Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙin Najeriya, a wani saƙo cikin raha da ta wallafa a shafinta na Instagram ta ambaci sunayen Naziru Sarkin Waƙa, Hamisu Breaker, Auta Waziri, Dauda Kahutu Rarara, Na...
Sai watan Janairun 2026 sabbin dokokin haraji za su fara aiki – Gwamnatin Najeriya

Sai watan Janairun 2026 sabbin dokokin haraji za su fara aiki – Gwamnatin Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta fara aiwatar da sababbin dokokin haraji da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu ba sai a watan Janairun 2026. Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan bikin saka wa dokokin huɗu hannu a yau Laraba, shugaban kwamatinn hukumar tattara harajin Zach Adedeji ya ce za su kammala tsara komai kafin lokacin aiwatar da su. Ya ƙara da cewa za su yi amfani da tazarar wata shidan wajen bai wa waɗanda ke da alhakin aiwatar da dokar damar shiryawa da kuma tabbatar da cewa an wayar da kan dukkan 'yan Najeriya game da dokokin. Ya tabbatar da cewa saka wa dokokin hannu ya sauya sunan ma'aikatarsa daga Federal Inland Revenue Service (FIRS) zuwa Nigeria Revenue Service.
Hukumar zabe me zaman Kanta, INEC zata ci gaba da yiwa ‘yan Najeriya rijistar katin zabe

Hukumar zabe me zaman Kanta, INEC zata ci gaba da yiwa ‘yan Najeriya rijistar katin zabe

Duk Labarai
Hukumar zabe me zaman kanta tace zata ci gaba da rijistar masu zabe a ranar 17 ga watan Yuli a jihar Anambra inda kuma za'a ci gaba da yi a gaba dayan Najeriya a ranar 18 ga watan Augusta. Shugaban hukumar, Prof. Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da aka yi ranar Alhamis a Abuja. Ya bayyana cewa, za'a fara rijistar ne a jihar Anambra saboda zaben gwamna da za'a gudanar a jihar.
Sharrine aka kalamin ban baiwa dana manyan filaye a Abuja ba>>Inji Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike

Sharrine aka kalamin ban baiwa dana manyan filaye a Abuja ba>>Inji Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa babu gaskiya a maganar da ake yadawa wai ya baiwa dansa filaye a manyan unguwannin Abuja. Me magana da yawun ministan, Lere Olayinkane ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar ga manema labarai inda yace ko fili daya Wike be baiwa dansa ba. A baya dai hutudole ya kawo muku rahoton dake cewa kafar Peoplesgazette ta ce ta samu bayanan sirri cewa, Wike ya rabawa 'ya'yansa filaye a Abuja. Saidai Wike yace wannan magana karyace da ta fito daga bakin 'yan jaridar da basu da kwarewa a aikinsu. Wike yace a ina za'a samu filaye da yawa a Asokoro da Maitama wanda har zai rabawa 'ya'yansa? Yace idan kuma jaridar tace gaskiyane rahoton data wallafa to ta kawo takarda me dauke da sunan dan Wike dake nuna alamar cewa ya mall...