Gyaran fuska da kwai
Ana amfani da kwai wajan gyaran fuska sosai dan magance matsalolin da kan iya shafar fuska.
Ga hanyoyin da ake amfani da kwan kamar haka:
Ana fasa kwan a cire kwaiduwar a bar ruwan kwan kawai sai a hada da zuma, da ruwan lemun tsami ai ta bugawa har sai sun hadu.
Idan ya hadu sosai sai a wanke fuska da ruwan dumi.
A fara shafawa a hannu adan barshi zuwa mintuna biyar, idan ba'a ga wata matsala ba, daga nan sai a shafa a fuska,dalilin yin hakan shine wasu yana musu reaction.
A barshi ya kai mintuna 10 zuwa 15 a fuska? Daga nan sai a wanke.
Ana iya yin hakan sau 3 a mako.
Wannan hadi yana sa fatar fuska ta yi laushi ta yi kyau sosai? Yana maganin kurajen fuska da kawar da tattarewar fuska da kuma maganin tsufan fuska.
Sannan kuma ana yin hadin Ruwan kwai, Shima a cire...