Tuesday, December 23
Shadow
A yau zan kafa sabon Tarihin saka hannu a kudirin dokar canja Haraji da zai amfani har wadanda bama a haifa ba>>Shugaba Tinubu

A yau zan kafa sabon Tarihin saka hannu a kudirin dokar canja Haraji da zai amfani har wadanda bama a haifa ba>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, a yau, Alhamis zai kafa sabon Tarihi da Tubalin ci gaban Najeriya wanda zai amfani har ma wadanda ba'a haifa ba. Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta kafar sada zumuntarsa inda yace yana godiya ga 'yan Najeriya bisa hadin kan da suka bashi na canja fasalin Karbar Haraji a Najeriya. Shugaban yace wannan sabon kudirin na Haraji zai habaka kasuwanci a Najeriya sosai domin akwai adalci a cikinsa. Shugaban ya bayyana cewa, yana kira ga 'yan kasuwa na Duniya cewa ga dama ta samu ta zuba hannun jari a Najeriya. Ya kuma godewa, Kwamitin da ya kafa na canja fasalin karbar Harajin da majalisar dattijai da Gwamnatocin jihohi bisa gudummawar da suka bayar wajan tabbatar da canja fasalin karbar Harajin.
Shugaba Tinubu yaki sakawa sabuwar dokar NDLEA hannu, Ji Dalili

Shugaba Tinubu yaki sakawa sabuwar dokar NDLEA hannu, Ji Dalili

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ki sakawa sabuwar dokar NDLEA hannu wadda 'yan majalisa suka amince da ita. Shugaban ya aikewa da majalisar tarayya da wasika dake kunshe da dalilansa na kin sakawa sabuwar dokar hannu. Shugaba Tinubu yace dalilinsa shine sabuwar dokar na kunshe da cewa, idan hukumar ta NDLEA ta kwace kwaya ko kayan laifi, zata iya ajiye ko rike wani sashi na kayan da ta kwace. Shugaban yace dokar da ake da ita a yanzu ta tanadi cewa ne a saka ko ma wane irin abune aka kwace zuwa asusu na musamman da aka ware dan kula da kayan da aka kwace, kuma bai ga dalilin da zai sa a canja wannan tsari ba. Yace shugaban kasa ne kawai ke da ikon baiwa duk wata hukuma kudi daga cikin asusun da ake tara kudaden da aka kwace. Yace tsarin da ake kansa yafi tabbatar da tsar...
Gwamnatin Tarayya ta hada kai da matatar man fetur din Dangote dan rage farashin man

Gwamnatin Tarayya ta hada kai da matatar man fetur din Dangote dan rage farashin man

Duk Labarai
Shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bukaci a rage farashin man fetur a Najeriya. Kuma hukumar kula da sayar da man fetur din Najeriya, NEPZA a takaice ta bayyana aniyarta ta hada kai da matatar man fetur din Dangote dan tabbatar da wannan bukata ta shugaban kasa. Shugaban hukumar, Dr. Olufemi Ogunyemi ne ya bayyana haka a Abuja yayin wata ziyara da aka kai masa. Itama matatar man Dangote ta ce a shirye take dan tabbatar da wannan kudirin na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Wannan shiri zai samu nasara ne ta hanyar tabbatar da ci gaba da sayar da man fetur din Najeriya da kudin Naira maimakon dala musamman ga matatar Dangote.
Obi ya koka kan rushe ginin ƙanin sa a Legas

Obi ya koka kan rushe ginin ƙanin sa a Legas

Duk Labarai
Obi ya koka kan rushe ginin ƙanin sa a Legas Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi Allah-wadai da rushe wani gini da ya ce na ƙaninsa ne da ke jihar Legas. Ya bayyana wannan mataki a matsayin abin da ya saɓa wa doka kuma yana nuna yadda Najeriya ke ƙara nutsewa cikin rashin bin doka a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Obi ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya kai ziyarar gaggawa zuwa wurin da aka rushe ginin, inda ya nuna ɓacin ransa kan "take hakkokin ‘yan ƙasa da rashin bin ka’ida da aka yi ba tare da wata hujja ba." Daily Trust ta rawaito cewa Obi ya ce jami’an tsaro sun hana ɗan’uwansa samun damar ceto duk wani kayan da ke cikin ginin kafin a fara rushewar. Ya ƙara da cewa wannan abin da ya faru hujja ce ta yadda tsarin ...
Ni da kaina na je ofishin EFCC ba kama ni akai ba>> Inji Tsohon Me kula da kudi na kamfanin mai na kasa, NNPCL, Umar Ajiya Isa da ake zargi da satar Dala Biliyan $7.2 na gyaran matatun man fetur din Najeriya

Ni da kaina na je ofishin EFCC ba kama ni akai ba>> Inji Tsohon Me kula da kudi na kamfanin mai na kasa, NNPCL, Umar Ajiya Isa da ake zargi da satar Dala Biliyan $7.2 na gyaran matatun man fetur din Najeriya

Duk Labarai
Tsohon Babban Jami’in Kudi (CFO) na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Umar Ajiya Isa, ya karyata rahotannin da ke cewa jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kama shi a ranar Litinin bisa zargin almundahana. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ajiya ya bayyana cewa, akasin yadda ake yadawa, shi da kansa ne ya je ofishin EFCC domin amsa tambayoyi, ba tare da an kama shi ba dangane da zargin handame cinikin man fetur har ma dala biliyan $7.2 a matatun mai na Warri da Port Harcourt. “Ba wanda ya kama ni kan zargin batan wata dala biliyan $7.2 a matatar mai. Na je ofishin EFCC ne da kaina domin amsa tambayoyi sannan na koma gida. Na ji takaici ganin rahotanni a kafafen yada labarai da ke cewa an kama ni bisa zargin damfara,” in ji shi. “Na yi aiki a...
Ni Da Rarara Abokan Juna Ne, Inji Shugaba Tinubu

Ni Da Rarara Abokan Juna Ne, Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Ni Da Rarara Abokan Juna Ne, Inji Shugaba Tinubu
Da Duminsa: Hukumar ‘yansandan farin kaya ta kama masu satar mutane dan neman kudin fansa su 6 a filin jirgin sama dake Kaduna bayan da suka dawo daga aikin Hajji

Da Duminsa: Hukumar ‘yansandan farin kaya ta kama masu satar mutane dan neman kudin fansa su 6 a filin jirgin sama dake Kaduna bayan da suka dawo daga aikin Hajji

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, hukumar 'Yansandan farin kaya DSS ta kama masu garkuwa da mutane 6 da suka dawo daga aikin Hajji a filin sauka da tashin jiragen saman jihar. An kamasu ne da misalin karfe 3:40am kamar yanda wata majiya ta gayawa majiyarmu. Wadanda aka kama din mata 3 ne maza 3 kamar yanda rahoton ya tabbatar. An kama su ne da daren ranar Talata. Zuwa yanzu dai ba'a fitar da bayanai kan sunaye ko hotunan wadanda aka kama din ba. Ko da a watan Mayu da ya gabata dai an kama wani me garkuwa da mutane me suna Sani Galadi da ke shirin tafiya zuwa aikin Hajji.
An kama malamin jami’a saboda wallafa Bidiyon rawa na dan Gwamnan Bauchi

An kama malamin jami’a saboda wallafa Bidiyon rawa na dan Gwamnan Bauchi

Duk Labarai
Kotu a jihar Bauchi na shirin yanke hukunci kan wani malamin jami'a da ya wallafa tsohon Bidiyon dan gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad yana rawa. A yau Alhamis ne ake sa ran kotun zata yanke hukuncin neman belin malamin me suna Dr. Abubakar Ahmad wanda dan gwamnan me suna Shamsudeen Bala Mohammed ne ake zargin ya shigar dashi kara. Malamin na koyarwa ne a kwalejin Federal College of Horticulture dake jihar. An kamashi ne saboda wani tsohon Bidiyon da ya wallafa na dan Gwamnan da matarsa suna rawa. Me ikirarin kare hakkin bil'adama kuma mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore ne ya wallafa hakan. Yace An tsare malamin makarantar na tsawon makonni 2 bisa cin zarafi da rashin adalci. Matar malamin me suna Fatima ta nemi a saki mijinta. Fatima ta yi kira ga Gw...