Monday, May 12
Shadow

Yadda ake gane motsin ciki

Gwajin Ciki
Ana gane motsin ciki ne idan aka ji wani abu kamar filfilo a ciki. Ana kuma iya jin kamar jaririn ya harba kafa. Mace zata iya jin jijjiga. Lokacin da jariri ke fara motsi a ciki: Jariri na fara motsine a sati na 12 da daukar ciki amma ba zaki ji motsin ba. Idan kin taba haihuwa, zaki iya jin motsin jaririn a sati na 16. Amma idan baki taba haihuwa ba, sai wajan sati na 20 kamin kiji motsin jaririn. Saidai kowace mace akwai lokacin da take jin motsin jaririnta ba lallai ya zama lokaci guda ga kowace me ciki ba. Zaki iya sa jaririnki yayi motsi: Masana sunce zaki iya sa jaririnki yayi motsi, idan kina son hakan, kawai zaki kwanta ne ta bangaren hagu ne. Mafi yawanci, mace takan ji motsin jaririnta bayan ta ci abinci.

Hotuna: Mata biyu sun lakadawa wani mutum dukan tsiya har ya mu-tu saboda yaki yin lalata dasu

Abin Mamaki
Wasu mata a kasar Rasha sun lakadawa wani mutum da yaki yin lalata dasu dukan kawo wuka har ya mutu. An dai kama matan bayan faruwar lamarin. Matan su biyu ne inda daya sunanta Martha me shekaru 37 sai kuma Rosa me shekaru 29. Rahoton yace suna rawa ne tare da Alexandra me shekaru 63. Rahoton yace sun nannaushi mutumin saboda yaki yayi lalata dasu. Bayan da suka kasheshi sai suka boye gawar a cikin wani rami. Saidai an gano gawar mutumin kuma an kama matan inda aka gurfanar dasu a gaban kuliya.

Shigar ciki nasa ciwon mara

Gwajin Ciki
Eh, shigar ciki nasa ciwon mara, mata da yawa na yin fama da ciwon mara bayan sun dauki ciki. Kuma zai iya zuwa a kowane lokaci, watau a farkon shigar ciki ko kuma yayin da cikin ya tsufa. Wata zai rika zuwa mata yana tafiya lokaci zuwa lokaci, zata rika jinshi kamar irin na al'ada. Za'a iya jinshi a gefe daya na mara inda a wasu lokutan za'a iya jinshi a duka bangarorin biyu na marar. Wannan ciwon mara ba wata babbar matsala bace, an saba ganinta a wajan mata masu ciki da yawa. Zafin ciwon kan iya karuwa yayin da cikin ke kara girma. Saidai idan an shiga damuwa sosai saboda ciwon na mara ana iya zuwa ganin Likita.

Siffofin mace mai ciki

Gwajin Ciki
Mace me ciki na da siffofin da ake gane ta dasu kamar haka. Wata na yi katon ciki, Musamman me 'yan biyu ko 'yan uku, ana ganinta da katon ciki. Kamanninta zasu canja, Mafi yawa zaka ga kamannin me ciki sun canja, fuskarta ta ciko sosai. Yawan tofar da yawu, wata Mace me ciki takan rika tifar da yawu saboda rashin dandano da take ji a bakinta. Nishi: Wata mace me cikin takan rika yin nishi saboda laulayin cikin da take dauke dashi. Canjawar dabi'a: Wasu dabi'unsu na canjawa inda zaka ga wasu har duka suna yi. Yanda ita kanta mace zata gane tana da ciki: Zubar da jini wanda bana al'ada ba. Kan nono zai rika zafi, zai ya kumbura. Kasala. Ciwon Kai. Amai. Rashin son cin abinci. Yawan Fitsari. Babbat hanyar da ake gane mace na da ciki shine a yi gwaji...
Hoto: An kamashi da ka-wu-nan mutane 8 dan yin tsafi

Hoto: An kamashi da ka-wu-nan mutane 8 dan yin tsafi

Duk Labarai
Jami'an 'yansanda a jihar Ondo sun kama wani matashi me suna Yusuf Adinoyi bayan samunsa da kawunan mutane 8. Kwamishinan 'yansandan jihar, Abayomi Oladipo, ya tabbatar da kamen inda yace an kama wanda ake zarginne ranar Litinin bayan an kafa shingen bincike. Mutumin na kan hanyar zuwa Akure ne kamin aka tare motarsu wadda yayi kokarin tserewa amma aka bishi aka kamoshi. Ya amsa laifinsa inda yace a baya yana sana'ar sayar da manja ne amma rashin lafiyar mahaifiyarsa tasa ya shiga harkar sayar da kawuna. Yace wannan ne karo na 3 da yake son sayar da kawunan inda a farko ya sayar da guda 4, sannan ya sayar da guda 3 hakanan sai yanzu zai sayar da guda 8. Kwamishinan 'yansandan yace za'a gurfanar dashi a kotu bayan kammala bincike.
Ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky ta koma kan ‘yan siyasa>>Inji Peter Obi

Ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky ta koma kan ‘yan siyasa>>Inji Peter Obi

Siyasa
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky da Obi Cubana ta je ta kama 'yan siyasa masu sata. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Yace idan da a yanzu gwamnati zata ce zata ciyar da mata kadai a Najeriya, saboda yunwar da ake ciki, maza da yawa zasu saka kayan mata su je karbar abincin. Bobrisky dai yana can daure a gidan yari saboda lika kudi a wajan biki yayin da shi kuma Obi Cubana aka gurfanar dashi ...
Na matsawa mijina dole sai ya sake ni domin mun ha’du da wani Saurayi Mai kyau a Facebook.

Na matsawa mijina dole sai ya sake ni domin mun ha’du da wani Saurayi Mai kyau a Facebook.

Soyayya
Na matsawa mijina dole sai ya sake ni domin mun ha'du da wani Saurayi Mai kyau a Facebook. Khadra, wacce ta fito a wata hira ta TV, ta ce, a shekarar 2022, na hadu da wani mutum a Facebook wanda ya fi mijina kyau. Mun kasance da soyayya mai zurfi, duk da cewa ni matar aure ce mai ‘ya’ya uku. Daga ƙarshe, ya rinjaye ni na yi jayayya da mijina, na nemi saki Kuma ya sake ni. A ranar da na rabu da mijina sai kawai shi Saurayin nawa dandalin Facebook ya yi bulokin Dina a duk shafukan da muke tattaunawa dashi.
Tsadar rayuwa: Kamfanin Guinness mai yin giya ya sanar da ficewa daga Najeriya saboda ciniki yayi kasa

Tsadar rayuwa: Kamfanin Guinness mai yin giya ya sanar da ficewa daga Najeriya saboda ciniki yayi kasa

Kasuwanci
Kamfanin Guinness mai yin kayan sha ciki har da giya ya sanar da shirinsa na ficewa daga Najeriya saboda matsanancin halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki. Kamfanin wanda ya kwashe fiye da shekra 74 yana aiki a Najeriya ya ce zai fice sannan kuma zai sayar da dukkannin hannin jari mallakarsa ga rukunin kamfanoni na Tolaram Group na ƙasar Singapore. Jaridar People's Gazette ta rawaito cewa kamfanin na Guinness dai ya yi asarar naira biliyan 61.9 a watan Yulin 2023 da Maris na 2024 bayan hawan Tinubu inda ya rage wa naira daraja. Guinness Nigeria Plc, kamfani ne wanda yake cikin jerin sunayen kamfanoni da ke hada-hadar hannayen jari a Najeriya kuma an yi masa rijista a kasar a matsayin kamfanin da ke shigar da giya samfirin Stout daga Dublin.
Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

labaran tinubu ayau, Siyasa
Mutumin da shugaba Tinubun ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce yana jajanta wa Bola Tinubu dangane da "zamewar" da ya yi. "Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokaci da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya. Ina fatan lafiyar lau." A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin ba ta yi daidai ba.