Ji Cikakken Bayani kan hadarin jirgin saman Indiya inda mutane sama da 200 suka mùtù, an bayyana kudin diyyar da kamfanin jirgin zai biya iyalan màmàtàn
Wani jirgin sama mallakin kamfanin sufuri na Air Indiya ya yi hatsari inda ya faɗa kan wata unguwa da ke birnin Ahmedabad a yammacin ƙasar Indiya.
Shugaban kamfanin lura da sufurin jiragen sama na Indiya ya ce akwai fasinjoji da ma'aikata 242 a cikin jirgin.
Bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna baƙin hayaƙi ya turnuƙe bayan rikitowar jirgin.
Babu tabbacin adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata sanadiyyar hatsarin.
Jirgin na kan hanyarsa ne daga Indiya zuwa Birtaniya.
Ma'aikatan kashe gobara da masu bayar da agajin gaggawa sun garzaya wurin da lamarin ya faru.
Akwai yiwuwar dukkanin fasinjojin jirgin Indiya da ya yi hatsari sun mutu
Kamfanin dillancin labaru na AP ya ambato shugaban ƴansanda na birnin Ahmedabad na cewa akwai yiwuwar babu wanda ya ts...








