Tuesday, December 23
Shadow
Kalli Bidiyon yanda aka kama masu kwacen waya da suka shiga gidan wata Sabuwar Amarya a Kano, abinda sukawa amaryar ya bada mamaki

Kalli Bidiyon yanda aka kama masu kwacen waya da suka shiga gidan wata Sabuwar Amarya a Kano, abinda sukawa amaryar ya bada mamaki

Duk Labarai
Wasu masu kwacen waya sun shiga gidan wata sabuwar Amarya a unguwar Gaida dake Kano. Sun caccaka mata wuka sannan suka kwace mata waya, ta rika ihun barawo har mutane suka taru. Barayin 3 ne inda jama'a da suka taru suka yi nasarar kama guda 2 daga ciki. https://twitter.com/Alameen___Abba/status/1937492720034988336?t=yzO5jHDArxWZ5dgTJQyvNA&s=19 Amaryar dai an garzaya da ita Asibiti inda tana can tana samun sauki.
Wata Kungiya ta yi kiran shugaba Tinubu ya dauki Yakubu Dogara a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2027

Wata Kungiya ta yi kiran shugaba Tinubu ya dauki Yakubu Dogara a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2027

Duk Labarai
Wata Kungiya daga yankin Arewa maso gabas ta yi kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya ajiye Kashim Shettima ya dauki Yakubu Dogara a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2027. Kungiyar me suna the Coalition of APC Support Groups in the North-East ta bayyana hakane a zaman data gudanar a ranar Litinin a jihar Gombe. Kungiyar tace Yakubu Dogara ne wanda yafi dacewa ya zama mataimakin shugaban kasa a shekarar 2027. Tace zata nada wakilai da zasu jagoranci mutane zuwa ganin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a Abuja dan isar masa da sakonsu.
Sai Tinubu ya yi sa’a ma zai zo na uku a zaɓen 2027— In ji El-Rufai

Sai Tinubu ya yi sa’a ma zai zo na uku a zaɓen 2027— In ji El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ba ya damu da yawan sauya sheƙa da ake yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki. A wata hira da aka yi da shi kai tsaye a shirin Arise TV a daren Litinin, El-Rufai ya ce shugaban ƙasa mai ci yana ɗaukar matsayin cewa tuni an gama da dawowar sa karo na biyu, ganin yadda wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa ke sauya sheƙa zuwa APC. Sai dai ya bayyana cewa: "Tinubu ba zai ci zaɓe ba. A gaskiya, zai yi sa’a idan ma ya zo na uku." Tsohon gwamnan ya zargi gwamnatin Tinubu da halin ko in kula dangane da matsanancin halin tsaro da ƙasar ke ciki, yana mai bayyana cewa an cire naira biliyan 100 daga Asusun Tarayya cikin watanni 15 da suka gabata ba tare da amincewar jihohi ko majalisar dokoki ba. Ya ce: "Tun cikin watanni 15 da suka wuce, ana...
Gaskiya ka iya Karya, ta ya zaka ce mana kun kammala jami’a da dan shekaru 13?>>Atiku Abubakar ya caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Gaskiya ka iya Karya, ta ya zaka ce mana kun kammala jami’a da dan shekaru 13?>>Atiku Abubakar ya caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, akwai daure kai da rainin hankali ace wai Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kammala jami'a tare da dan shekaru 13. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a yayin da yake kaddamar da shirinsa na Renew Hope Agenda a Abuja ya bayyana wani me suna Alex Zingman  da cewa, abokin karatunsa ne. Saidai Atiku yace shi wannan me suna Alex Zingman da Tinubu yace sun kammala jami'ar Chicago State University (CSU) tare a shekarar 1979, an haifeshine a shekarar 1966, watau yana da shekaru 13 kenan suka kammala karatu tare da shugaba Tinubu. Dan haka Atiku a sanarwar da ya fitar ta hannun me magana da yawunsa, Paul Ibe yace wata kila kundin tarihin Duniya ya manta ne bai saka wannan abokin karatu n...
‘Yan majalisar Wakilai 2 sun bar jam’iyyar PDP da Labour Party zuwa APC

‘Yan majalisar Wakilai 2 sun bar jam’iyyar PDP da Labour Party zuwa APC

Duk Labarai
'Yan majalisar wakilai biyu, Peter Akpanke, da Paul Nnamchi sun bar jam'iyyunsu inda suka koma jam'iyyar APC. Akpanke ya fito daga jihar Cross River ne kuma an zabeshi a karkashin jam'iyyar PDP amma yanzu ya bar jam'iyyar zuwa APC. Shi kuwa Nnamchi ya fito daga jihar Enugu ne kuma an zabeshi a karkashin jam'iyyar Labour party ne amma yanzu ya koma jam'iyyar APC. Kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas ya sanar da komawarsu APC a yayin zaman majalisar ranar Talata.

Maganin yawan bacci

Magunguna
Domin magance yawan bacci, ka tsarawa kanka yanda zaka rika bacci kuma ya zama a kullun a daidai wannan lokacin kake kwanciya. Sannan ka kiyaye, kada ka rika shan Coffee ko giya, sannan kada ka rika cin abinci me yawa sosai musamman da dare kamin ka kwanta. Sannan ka rika motsa jiki akai-akai. Sannan ka daina kallon TV akalla awa daya kamin ka kwanta, saboda hasken TV ko waya na iya kawo tangarda wajan yin bacci. Idan da hali, ka yi wanka da ruwan dumi kamin ka kwanta. Hakanan kada a sha taba kamin a kwanta. Idan kana da kiba da yawa a yi kokarin ragewa ta hanyar azumi ko motsa jiki. Yana da kyau kuma a rika shan ruwa akai-akai.

Wanene matashi

Duk Labarai
Matashi yana nufin mutum me karancin shekaru, kakkarfa, wanda bai kammala fahimtar menene rayuwa ba. Yawanci ana alakanta mutane maza da mata dake tsakanin shekaru 15 zuwa 25 da matasa. Saidai a wani kaulin, wasu sun ce har dan shekaru 30, wasu ma sun ce kai dan shekaru 40 ka za'a iya kiranshi da matashi. Duk da yake cewa dan shekaru 30 zuwa 40 za'a iya cewa sun fahimci menene rayuwa, amma daya daga cikin abinda ake fassara kalmar matashi dashi akwai karfi. Kuma dan shekaru 30 zuwa 40 indai ba yana da wata zaunanniyar cuta ba, zaka ga da karfinsa. Kuma manyan mutane zasu iya kiran kanana da matasa. Misali dan shekaru 60 zai iya kiran dan shekaru 30 zuwa 40 da matashi. Dan shekaru 40 zai iya kiran dan shekaru 15 zuwa 25 da matashi. Dan haka kalmar matashi na da yalwa...

Kalaman godiya ga saurayi

Duk Labarai
Idan saurayinki ya miki kyauta, yana da kyau ki gode masa hakan zai kara bashi karfin gwiwar sake yi miki wata kyautar nan gaba. Ga kalaman Godiya ga Saurayi kamar haka: Nagode sosai Allah yasa ka fi haka. Allah saka maka da Mafificin Alheri. Kyauta na daga cikin alamun soyayya, a kullun kana kara nuna min irin yanda ka damu dani, nagode da wannan kyauta. Ka sakani cikin farin ciki sosai, fatana shine Allah ya bani ikon faranta maka nima. Baka gajiya da yi min kyauta, hakan na kara narkar dani a cikin soyayyarka. Kamin kyautar da ban taba tunin samu ba, ban da kalaman da zan iya nuna cikakkiyar godiya ta gareka, dan haka kawai zance Allah saka maka da Alheri. Wanda ya damu da kai shi ke maka kyauta, na gode da damuwa dani. Kyautarka na kara tabbatar min da zaka m...

Maganin tari na gargajiya

Duk Labarai
Akwai magungunan tari na gargajiya da yawa. A wannan rubutun, zamu bayyana su daya bayan daya: Ana hada maganin tari na gargajiya da Karas, Lemun Tsami, Suga da Zuma. Yanda ake hadawa shine, a samu karas din a wanke sannan a daddatsashi. A matse ruwan lemun tsamin a zubasu a mazubi daya da zuma da sukarin. A barshi ya kai awa 24 a ajiye. Sannan a fara sha karamin cokali kullun sau biyu a rana. Ana kuma iya hada maganin Mura da Zuma da Albasa. Ana yanka Albasar a saka cikin kwano, daga nan kuma sai a zuba zuma a saman Albasar. A rufe a barshi yayi akalla awanni 12. Bayan nan sai a fara sha. Saidai yaro dan shekaru 2 baya sha, sannan me ciwon sugar kada ya rika sha da yawa.

Amfanin ganyen abarba

Duk Labarai
A yayin da dayawa yadda ganyen Abarba suke, amma yana da matukar amfani sosai. Daya daga cikin amfanin ganyen abarba shine yana maganin kumburi da kuma matsalolin da suka shafi hanci. Sannan a wani kaulin an ruwaito cewa, ganyen Abarba na kara karfin kashi. Idan mutum ya kone, fatar wajan ta lalace, ana amfani da ganyen Abarba wajan gyara wajan da fatar ta lalace. Ga me habo ko zubar da jini ta hanci, Ana tafasa ganyen Abarba a hada da zuma dan magance wannan matsala. Hakanan ana amfani da ganyen Abarba wajan saka kayan sawa da yin igiya da sauransu. Ana baiwa dabbobi, irin su shanu ganyen Abarba a matsayin abinci. Ana amfani da ganyen abarba wajan saka nama yayi laushi. Ana kuma amfani dashi wajan kayan kwalliya. Ana kuma zubashi a abinci dan karawa abincin Arm...