Alummar garin Mokwa na fargabar ɓarkewar cùtùkà saboda gàwàrwàkìn da ba a gano ba
Aƙalla makonni biyu da afkuwar ambaliyar ruwan da ta hallaka mutane tare da share gidaje masu dimbin yawa a garin Mokwa na jihar Neja, jama'ar yankin na kokawa kan yadda aka soma jin warin gawarwakin mutanen da har kawo yanzu ba a kai ga ganowa ba.
Jama’a dai na ci gaba da bayyana cewa warin na iya haifar da matsala ga lafiya, musamman ana fargabar barkewar kwalara kasancewar da dama daga rijiyoyin jama’a da suke samun ruwan sha sun rufta.
Daga cikin wadanda BBC ta zanta da su, sun ce tun daga ranar asabar ta karshen makon daya gabata suka soma jin warin gawarwakin.
Sai dai wasu mazauna garin na Mokwa sun ce a yanzu dai fargabar da ake da ita ta ɗan ragu bayan da aka soma yin feshin magani a wasu wurare.
Sun kuma ce Unicef ta bayar da wasu magunguna da ake sawa cikin ruwan da z...








