Friday, March 6
Shadow
Kalli Bidiyo: Nima nace Shugaba Tinubu ya rigamu gidan gaskiya, wanda ya fasa kamani Allah ya tsin masa>>Inji Sheikh Salihu Zaria

Kalli Bidiyo: Nima nace Shugaba Tinubu ya rigamu gidan gaskiya, wanda ya fasa kamani Allah ya tsin masa>>Inji Sheikh Salihu Zaria

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Salihu Zaria ya nuna bacin ransa kan kamun da akawa me watsa labarai a kafar Tiktok, Sultan. Malamin yace shima ya fada cewa shugaban kasa ya mutu kuma wallahi sai ya mutu din ma. Yace wanda ya fasa kamashi Allah ya tsine masa Albarka. Malam yace ga wadanda ke haifar da matsalar tsaro nan ba'a kamasu ba sai Sultan. Kalli Bidiyonsa a kasa: https://www.tiktok.com/@saleemyusufmuhammadsambo/video/7533340465458908472?_t=ZS-8yVSPtBKLon&_r=1 Kama Sultan ya jawo cece-kuce da Allah wadai sosai ga gwamnatin Tinubu.
ADC ba barazana bane: Cikin Sauki Tinubu zai samu kuri’u Miliyan 15 a zaben 2027 ya lashe zabe>>Inji wani na hannun damar shugaban kasar

ADC ba barazana bane: Cikin Sauki Tinubu zai samu kuri’u Miliyan 15 a zaben 2027 ya lashe zabe>>Inji wani na hannun damar shugaban kasar

Duk Labarai
Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Nicolas Felix ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai samu kuri'u Miliyan 15 a zaben 2027. Yace wannan babu tantama akai. Ya bayyana hakane a yayin da ya rabawa wasu mabukata man fetur kyauta a Suleja dake jihar Naija ranar Alhamis. Ya ce Hadakar 'yan Adawa a ADC ba zata zamarwa Shugaba Bola Ahmad Tinubu barazana ba. Ya kara da cewa, kamar yanda 'yan Adawar suka taho suka hadu, haka kuma zasu watse.
Da Duminsa: Gwamnatin tarayya zata kara farashin man fetur nan da 1 ga watan Janairu na shekarar 2026

Da Duminsa: Gwamnatin tarayya zata kara farashin man fetur nan da 1 ga watan Janairu na shekarar 2026

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya zata kara farashin man fetur nan da 1 ga watan Janairu na shekarar 2026. Hakan na kunshene a cikin sabuwar dokar haraji wadda aka zartas a kwanakin baya. Dokar ta tanadi kara harajin kaso 5.0 cikin 100 akan man fetur wanda aka tace a gida Najeriya da kuma wanda aka shigo dashi daga kasashen waje. Saidai wasu masu sharhi na cewa hakan bai dace ba lura da yanda a yanzu haka Talaka ke fama da kansa inaga an kara farashin man fetur?
Kalli Bidiyo da Duminsa: A karshe dai Ummi Nuhu ta samu mijin aure, wanda ya fito da gaske yana son aurenta, kaleshi

Kalli Bidiyo da Duminsa: A karshe dai Ummi Nuhu ta samu mijin aure, wanda ya fito da gaske yana son aurenta, kaleshi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"transform":1,"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Rahotanni sun tabbatar da cewa, a karshe, An samu wanda ya fito yace yana son Ummi Nuhu da gaske kuma zai aureta. Daya daga cikin masu shirya fina-finan Hausa ne ya fito ya tabbatar da hakan. Yace idan aka kammala komai, zasu sanar da jama'a hali da ake ciki. Wasu dai na zargin wai kwadayin kudaden da aka tarawa Ummi ne ya kai mutumin wajanta. https://www.tiktok.com/@yakubu_producer/video/7533212974652132664?_t=ZS-8yUnsVFoX0C&_r=1 ...
Kalli Bidiyo: Gidana ya hadu sosai ta yanda babu bangaren da zaka kalla kace ni Talaka ne>>Inji Naziru Sarkin Waka

Kalli Bidiyo: Gidana ya hadu sosai ta yanda babu bangaren da zaka kalla kace ni Talaka ne>>Inji Naziru Sarkin Waka

Duk Labarai
Tauraron Mawakin Hausa, Naziru Sarkin Waka ya bayyana cewa, gidansa ya hadu sosai ta yanda babu bangaren da mutum zai kalla yace shi talaka ne. Naziru ya kara da cewa, shi Allah ya yishi mutum ne me son ,aman gida dan haka ya kayata gidansa yanda ya kamata. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. https://www.tiktok.com/@naziru.sarkin.wak443/video/7533212900316417286?_t=ZS-8yUjw0kOVQf&_r=1
Sabon Rikici: Tsohon Mataimakin shugaban jam’iyyar ADC, Nafi’u Bala ya fito yace shine sabon shugaban jam’iyyar ba David Mark ba

Sabon Rikici: Tsohon Mataimakin shugaban jam’iyyar ADC, Nafi’u Bala ya fito yace shine sabon shugaban jam’iyyar ba David Mark ba

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ADC, Nafi’u Bala wanda kuma dan takarar gwamna ne na jam'iyyar a jihar Gombe ya fito yayi ikirarin cewa shine ahugaban riko na jam'iyyar. Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar da tsakar dare. Yace ba zasu amince da David Mark a matsaykn shugaban jam'iyyar na riko ba inda yace an karya doka da aka baiwa wadanda ba asalin 'yan jam'iyyar ragamar shugabancin jam'iyyar ba. Hakan na zuwane bayan da aka mikawa David Mark shugabancin jam'iyyar na riko.
Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya karawa shugaban Kwastam wa’adi

Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya karawa shugaban Kwastam wa’adi

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya karawa shugaban Kwastam, Bashir Adeniyi yawan wa'adinsa. Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis. Sanarwar tace shugaban kwastam din, Mr. Bashir Adewale Adeniyi, MFR ya kamata ya ajiye aiki nan da 31 ga watan Augusta 2025. Amma an kara masa wa'adi zuwa shekara daya. Sanarwar tace an kara masa wa'adinne dan ya ci gaba da ayyukan gyara Najeriya sannan shugaba Tinubu ya yaba da aikinsa.
Gwamnati ta fara yiwa ‘yan ADC tayin Mukamai dan su yi watsi da jam’iyyar

Gwamnati ta fara yiwa ‘yan ADC tayin Mukamai dan su yi watsi da jam’iyyar

Duk Labarai
Tsohon shugaban jam'iyyar Hadakata ta ADC, Ralph Nwosu ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta masa tayin mukamin Minista har sau 3 dan ya bar jam'iyyar amma yaki. Ya bayyana hakane a ranar Talata a yayin da aka mikawa David Mark shugabancin jam'iyyar a hukumance. Yace kokarin na gwamnati yana son dakile kaifin duk wasu 'yan adawa ne dan mayar da Najeriya tsarin tafarkin jam'iyya daya. Yace an masa tayin kujerar Minista guda 3 ne dan ya dauki daya yayi kyauta da guda 2. Saidai yace ya zabi Dimokradiyyar Najeriya da ci gabanta. Ya kara da cewa, Najeriya ba zata zama kasa me jam'iyya daya ba bayan kokarin da aka yi na ganin an kawar da tsarin mulkin kama karya na soja. Yace tun bayan bayyana hadakatar 'yan Adawa a jam'iyyar ta ADC membobin jam'iyyar sun karu zuwa mutane Miliyan...
Idan Peter Obi ya dawo PDP ya tsaya takarar shugaban kasa, babu wani dan takara daga Arewa da zai iya kayar dashi>>Inji Farfesa Jerry Gana

Idan Peter Obi ya dawo PDP ya tsaya takarar shugaban kasa, babu wani dan takara daga Arewa da zai iya kayar dashi>>Inji Farfesa Jerry Gana

Duk Labarai
Farfesa Jerry Gana ya bayyana cewa idan Peter Obi ya koma PDP ya tsaya takarar shugaban kasa, babu dan takarar shugaban kasa daga Arewa da zai iya kayar dashi. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. Yace suna kan kokarin ganin sun jawo hankalin Peter Obi ya klma jam'iyyar su ta PDP. Yace kuma bayan Peter Obi din, akwai wani ma wanda yafi Peter Obi nagarta da karbuwa da suke kokarin kawowa PDP ya musu takara.