Saturday, December 13
Shadow
Kasar Ìran ta yiwa kasar Israyla mummunan kutse inda ta kwashi bayananta game da makamin kare danginta

Kasar Ìran ta yiwa kasar Israyla mummunan kutse inda ta kwashi bayananta game da makamin kare danginta

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Iran na cewa, kasar ta yiwa kasar Israyla kutse inda ta kwashi bayananta game da makamashin kare danginta. Rahoton yace kasar Iran ta dauki hayar wasu 'yan kasar Israelan aiki ne inda ta rika biyansu makudan kudade wanda suka rika bata bayanan sirri game da kasar ta Israela. Iran ta sanar da cewa ta dade tana wannan shirin kuma ba yau ta yi nasara ba amma dai ta tsaya ne kamin ta tabbatar da takardun bayanan sirrin kasar Israelan sun zo hannunta kamin ta sanar da nasarar ta. Kasar Israyla dai bata ce uffan ba kan lamarin. Saidai wasu rahotanni sun ce an kama wasu mutane da ake zargin sun hada kai da kasar Iran a cikin kasar ta Israela. A shekarun baya dai, kasar Israela itama tawa kasar Iran irin wannan kutse.
SANARWA GA MATAFIYA: Yanzu Haka Hanyar Abuja Zuwa Kano-Kaduna Ta Cunkushe, Inda Masu Ababen Hawa Suka Yi Curko-Curko Dauke Da Matafiya Musamman Masu Zuwa Hidimar Sallah

SANARWA GA MATAFIYA: Yanzu Haka Hanyar Abuja Zuwa Kano-Kaduna Ta Cunkushe, Inda Masu Ababen Hawa Suka Yi Curko-Curko Dauke Da Matafiya Musamman Masu Zuwa Hidimar Sallah

Duk Labarai
SANARWA GA MATAFIYA: Yanzu Haka Hanyar Abuja Zuwa Kano-Kaduna Ta Cunkushe, Inda Masu Ababen Hawa Suka Yi Curko-Curko Dauke Da Matafiya Musamman Masu Zuwa Hidimar Sallah. Idan da wata hanya da matafiya masu bin hanyar za su bi, gwamma su sauya don gudun fadawa cikin cunkuson. Wasu rahotonnni da Rariya ta samu, sun bayyana cewa cunkoson motocib ba ya rasa na nasaba da gyaran hanya da ake yi. Jama'a don Allah a yada (sharing) domin amfanar matafiyan dake shirin bin hanyar.
YANZU-YANZU: Jama’a Sun Ruga Cikin Gidajensu Da Gudu, Bayan Sun Ji Karar Harbe-Haŕbè A Garin Buni Gari Dake Jihar Yobe, Iñda Suķè Zàrgin masu ikirarin  Jìhàdì Nè Suka Shigo Garin

YANZU-YANZU: Jama’a Sun Ruga Cikin Gidajensu Da Gudu, Bayan Sun Ji Karar Harbe-Haŕbè A Garin Buni Gari Dake Jihar Yobe, Iñda Suķè Zàrgin masu ikirarin Jìhàdì Nè Suka Shigo Garin

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Jama'a Sun Ruga Cikin Gidajensu Da Gudu, Bayan Sun Ji Karar Harbe-Haŕbè A Garin Buni Gari Dake Jihar Yobe, Iñda Suķè Zàrgin masu ikirarin Jìhàdì Nè Suka Shigo Garin
Na yi na’am da hana hawan Sallah a Kano da hukumar ‘yansanda suka yi kuma ina zan bi wannan doka>>Inji Sarki Aminu Ado Bayero

Na yi na’am da hana hawan Sallah a Kano da hukumar ‘yansanda suka yi kuma ina zan bi wannan doka>>Inji Sarki Aminu Ado Bayero

Duk Labarai
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yace yayi murna da hana hawan Sallah da hukumar 'yansandan jihar suka yi. A ranar Talata ne hukumar 'yansandan jihar suka fitar da sanarwar cewa, sun dakatar da hawan Sallah a Kano. Hakan na zuwane jim kadan bayan da sarki Muhammad Sanusi II ya aikawa hakimai da su je hawan Sallah. Saidai a sanarwar da Sarki Aminu Ado ya fitar yace yana maraba da dakatar da hawan sallar kuma zai bi wannan doka. Sarki Aminu ya sanar da hakanne ta bakin kakakinsa, Awaisu Abbas Sanusi inda yace ya dauki wannan mataki ne bayan tuntuba da yayi da masu ruwa da tsaki
Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya ta kara yawan ziga-zirgar jirgin saboda tafiye-tafiyen Sallah

Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya ta kara yawan ziga-zirgar jirgin saboda tafiye-tafiyen Sallah

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, (NRC) ta kara yawan zirgazirgan jirgin kasar dake Jigila daga Legas zuwa Ibadan. Hakan na zuwa ne yayin da mutane ke ta tafiye-tafiye dan shagulgulan Sallah. Me magana da yawun hukumar, Callistus Unyimadu ne ya bayyana haka inda yace jirgin dake Jigila tsakanin Warri-Itakpe shima zai yi aiki na musamman a ranar Alhamis. Sannan yace jirgin Kaduna zuwa Abuja an kara mai yawan tarago.
Ma’aikatan wutar Lantarki zasu tsunduma yajin aiki

Ma’aikatan wutar Lantarki zasu tsunduma yajin aiki

Duk Labarai
Rahotanni na cewa, ma'aikatan wutar lantarki na Abuja zasu tafi yajin aiki. Ana sa ran lamarin zai saka mutanen jihohin Naija, Kogi, da Nasarawa cikin duhu. Ma'aikatan kamfamin me suna (AEDC) sun bayyana cewa, zasu tsunduma yajin aikinne saboda kasa cika alkawuran da kamfanin ya dauka bayan da suka yi yajin aiki a watan Nuwamba na shekarar 2024. A cikin sakon da suka aikawa hukumar kamfanin na AEDC sun Sanar da cewa wannan shine karo na karshe da zasu yi gargadi kuma a koda yaushe zasu iya tsunduma yajin aiki
Kaso 72 na yara a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa da suka kammala makarantun Firamare basu iya karatu ba>>Inji UNICEF

Kaso 72 na yara a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa da suka kammala makarantun Firamare basu iya karatu ba>>Inji UNICEF

Duk Labarai
Hukumar Lafiya ta yara ta majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana cewa, kaso 72 na yaran da suka kammala makarantun Firamare a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa basu iya karatu ba. Wakilin hukumar a jihar, Joseph Senesie ne ya bayyana hakan a ganawa da manema labarai inda yace yara da yawa ana hanasu samun ilimi yanda ya kamata. Yace yara Miliyan 2 ne a yankin basa samun zuwa makaranta. Yace kuma kananan hukumomi 12 a jihohin Borno da Yobe sunce akwai yara da yawa da ba'awa allurar Rigakafi ba. Yace a cikin yara 10, 3 ne kawai ake samun rijitar haihuwarsu a hukumance wanda hakan ke sa basa samun tallafin karatu, Abinci da sauransu. Saidai ya jinjinawa Gwamnatin jihar Borno kan kokarin da take na samar da tallafi ga rayuwar yara.
Kudin da ake warewa bangaren lafiya sun yi kadan matuka, ba zasu iya magance matsalar rashin lafiyar da ake fama da ita ba a Najeriya>>Inji Me kudin Duniya, Bill Gates

Kudin da ake warewa bangaren lafiya sun yi kadan matuka, ba zasu iya magance matsalar rashin lafiyar da ake fama da ita ba a Najeriya>>Inji Me kudin Duniya, Bill Gates

Duk Labarai
Me kudin Duniya, Bill Gates ya bayyana cewa kudin da ake warewa bangaren lafiya a Najeriya sun yi kadan. Yace sam kasafin kuin da ake warewa Najeriya ba zai iya magance matsalar rashin lafiyar da ake fama da ita ba a kasar. Yace kasafin kudin Najeriya zai fuskanci tangarda musaman shekara me zuwa saboda babu kudin tallafin da aka saba bayarwa. Bill Gates ya bayyana hakan ne ga manema labarai a yayin ganawar da yayi dasu a Legas. Ya ce, Karancin kudin da bangaren kula da lafiyar Najeriya ke fama dashi shine yasa kasar ke kan gaba wajan yawan mutuwar mata masu ciki da jarirai sabuwar haihuwa a Duniya. Ya kara da cewa mafi yawancin haihuwar da ake yi musamman a Arewacin Najeriya, yawanci a gida ake haihuwa kuma ko da sauran da ake kaiwa Asibiti, akwai asibitocin da basa iya yiw...
Masu raguna na kukan rashin ciniki a yayin da farashin ragunan ya yi tashi gwauron zabi

Masu raguna na kukan rashin ciniki a yayin da farashin ragunan ya yi tashi gwauron zabi

Duk Labarai
A yayin da ake shirin yin sallar Layya, Masu sayar da Raguna da yawa na kokawa da rashin ciniki. Farashin ragunan ya tashi sosai musamman saboda karancinsu da kuma matsalar tsaro da yankin Arewa ke fama dashi. Wani me sayar da rago a kasuwar Dei-Dei dake Abuja me suna Ahmed Mai-Samari yace kulle iyakar Najeriya da Nijar da hana shigo da ragunan ya taimaka wajan hauhawar farashin ragunan. Yace hakan yasa ragunan da aka kai kasuwanni sun yi kadan sosai wanda hakan yasa farashinsu ya tashi musamman idan aka kwatanta da shekarar 2024. Yace yanzu yawanci ragunan sun nunka kudinsu, wanda a shekarar data gabata aka sayar akan Naira dubu 200 yanzu sai mutum yasa Naira Dubu 400. Yace mafi karancin rago yanzu ana sayar dashi a farashin Naira 150,000 zuwa 190,000. Yace tsaka-tsaki ana ...
Ana tsaka da min Tiyata a Asibiti, sai na ji na Mutu, kuma na hadu da Jesus har ya nuna min Aljannah>>Inji Wannan Mutumin

Ana tsaka da min Tiyata a Asibiti, sai na ji na Mutu, kuma na hadu da Jesus har ya nuna min Aljannah>>Inji Wannan Mutumin

Duk Labarai
Wani mutum da yayi ikirarin ya mutu a yayin da ake tsaka da yi masa tiyata ya bayyana cewa ya hadu da Annabi Isa(AS) watau Jesus kuma wai har ya nuna masa Aljannah. Mutumin me suna Mike McKinsey dake California ta kasar Amurka ya bayyana cewa, yayi mutuwar ne ta mintuna 45. Likitoci sun bayyana cewa aikinsa ne mafi mamaki da hadari da suka taba yi inda suka ce wai ya mutu na dan wani lokaci a yayin da suke masa aikin cire appendix. Sun ce zuciyar mutumin ta daina bugawa sannan ya daina numfashi amma sun yi nasarar dawo dashi. Yace da ya mutun, ya ga Jesus wanda yayi kama da Balarabe. Yace Jesus din ya bashi hannu ya daukeshi zuwa wani guri me kyau da bai taba gani ba. Yace anan ne yasan cewa ba zai mutu ba. Ya kara da cewa, sai kawai ya farfado inda ya tabbatar cewa l...