Saturday, December 13
Shadow
Hajjin bana: Saudiyya ta hana ɗaukar hoto da taron siyasa a guraren ibada

Hajjin bana: Saudiyya ta hana ɗaukar hoto da taron siyasa a guraren ibada

Duk Labarai
Hukumomin Saudiyya sun hana daukar hoto, taruka da harkokin siyasa da daga tutoci a wuraren ibada yayin aikin Hajjin bana na 2025. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta fitar, masarautar ta bayyana cewa mahajjata ba su da izinin daukar hoto ko yin bidiyo a Masallacin Harami da ke Makkah, da Masallacin Annabi da ke Madinah, da kuma muhimman wuraren aikin hajji irin su Mina, Arafat da Muzdalifah. Ma’aikatar ta ce wannann umarni ya shafi wayoyin hannu da kuma na’urorin daukar hoto na kwararru, tare da gargadin kada a daga tuta ko alluna da ke dauke da alamomin siyasa, kabila ko akida. Hukumomin sun sake jaddada cewa irin wadannan ayyuka na iya lalata yanayin ibada da kuma haifar da rarrabuwar kai tsakanin mahajjata.
Gwamnatin tarayya ta gargadi DJ masu saka wakoki a wajan Bukukuwa da cewa su nemi lasisi ko kuma aci su tarar Naira Miliyan 1 ko daurin shekara 5 a gidan yari

Gwamnatin tarayya ta gargadi DJ masu saka wakoki a wajan Bukukuwa da cewa su nemi lasisi ko kuma aci su tarar Naira Miliyan 1 ko daurin shekara 5 a gidan yari

Duk Labarai
Hukumar kula da hakkin mallaka ta Najeriya ta gargadi DJ masu saka wakoki a gidajen biki dasu nemi lasisi ko izinin masu wakokin da suke sakawa. Hukumar tace rashin bin wannan doka na dauke da hukuncin biyan tarar Naira Miliyan daya ko zaman gidan yari na shekara 5. A kasashe irin su Amurka dai ba DJ ne ke biyan lasisi ba, me hidimar biki ko me gidan taron ko me Club ne zai biya wannan tara.
An zane wasu masoya bisa saduwa kafin aure a Indonesiya

An zane wasu masoya bisa saduwa kafin aure a Indonesiya

Duk Labarai
An zane wasu masoya bisa saduwa kafin aure a Indonesiya. An yi wa wani mutum da wata mata bulala ɗari-ɗari kowanne a bainar jama'a a lardin Aceh mai a kasar Indonesia a yau Laraba bayan da wata kotun shari'ar Musulunci ta same su da laifin yin jima'i kafin aure. An haramta yin jima'i tsakanin masoya da basu yi aure ba a garin na Aceh, wanda ya kafa tsarin shari'ar Musulunci. Indonesiya ta haramta yin jima'i ba tare da aure ba a sabon kundin dokokin Shari'ah a 2022 amma dokar ba za ta fara aiki ba sai shekara mai zuwa. Sai dai kuma an yi wa mutanen biyu bulala ɗari-ɗari ta hanyar yin goma-goma a yayin da wasu tsirarun jama'a ke kallo a wani wuri da ke Aceh babban birnin lardin, inda mace ce ta yi wa matar da ake zargin bulala, a cewar wani wakilin AFP da ke wajen da aka yi h...
Kasar mu kasa ce me cin gashin kanta dan haka bamu amince da duk wani sharadi da kasar Amurka ta gindaya na hanamu ci gaba da kokarin mallakar makamin Kare dangi ba>>Inji Ìràn

Kasar mu kasa ce me cin gashin kanta dan haka bamu amince da duk wani sharadi da kasar Amurka ta gindaya na hanamu ci gaba da kokarin mallakar makamin Kare dangi ba>>Inji Ìràn

Duk Labarai
Kasar Iran ta mayar da martani kan sharadin da kasar Amurka ta sanya mata na tattaunawar sulhu da suke kan shirinta na mallakar makamin kare dangi. Rahotanni sun bayyana cewa, Amurka ta ce Iran zata iya ci gaba da inganta makamashin kare dangi amma a hankali ba da gaggawa kamar yanda take yi a yanzu ba. Saidai Iran tace ita kasa ce me cin gashin kanta dan haka bata amince da sharadin da Amurka ta gindaya mata ba. A baya dai hukumar kula da makamashin Nokiliya ta Duniya ta bayyana cewa, Iran ta inganta makamashin Uraniyum zuwa matakin kaso 60 cikin 100 wanda gaf take da ta kai matakin kaso 90 cikin 100 wanda shine zai bata damar mallakar makamashin kare dangi.
Gwamnati ta saka tarar Naira dubu dari biyu da hamsin ko daurin watanni 3 ga duk wanda aka kama yana zubar da shara ba bisa ka’ida ba

Gwamnati ta saka tarar Naira dubu dari biyu da hamsin ko daurin watanni 3 ga duk wanda aka kama yana zubar da shara ba bisa ka’ida ba

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Legas ta saka tarar naira 250,000 ko daurin watanni 3 a gida gyara hali ga duk wanda aka kama yana zubar da shara ba bisa ka'ida ba. Kwamishinan Muhalli da ruwa na jihar, Mr. Tokunbo Wahab ne ya fitar da sanarwar ga manema labarai a ranar Talata inda yace masu kunnen kashi wanda aka kama akai-akai zasu fuskanci hukuncin da yafi wannan tsanani. Hukumar tace tuni aka hukunta mutane 3000 kan wannan lamari inda tace kuma zata ci gaba da hukunta masu laifin.
Kasashen Larabawa sun roki shugaban Amurka, Donald Trump ya saka kungiyar ‘yan Uwa musulmi cikin jerin kungiyoyin ‘yan tà’àddà

Kasashen Larabawa sun roki shugaban Amurka, Donald Trump ya saka kungiyar ‘yan Uwa musulmi cikin jerin kungiyoyin ‘yan tà’àddà

Duk Labarai
Kasashen Larabawa sun roki shugaban Amurka, Donald Trump da ya saka Kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood cikin kungiyoyin 'yan ta'adda. Sun bayyana masa hakanne a yayin ziyarar da ya kai kasashen Larabawan a kwanakin da suka gabata. Kasashen Larabawan da yawa ne dai tuni suka Haramta ayyukan kungiyar ta 'yan uwa musulmi. Tuni dai majalisar kasar Amurka ta fara muhawara dan saka kungiyar ta 'yan uwa musulmi cikin jerin kungiyoyin ta'addanci a Duniya.
Akwai yiyuwar kara farashin Man Fetur a Najeriya saboda sabon harajin da Gwamnatin Tinubu zata sanya

Akwai yiyuwar kara farashin Man Fetur a Najeriya saboda sabon harajin da Gwamnatin Tinubu zata sanya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar kara farashin man fetur saboda wani sabon Haraji da Gwamnatin Tinubu zata kakabawa 'yan Najeriya. Ma'aikatar ayyuka ta kasa da majalisar wakilai ne suke son a fara karbar wannan haraji na amfani da titunan Najeriya. Dan haka suke bayar da shawarar maimakon a rika karbar harajin kai tsaye, a rika karbarsa ta hanyar saka kudin a cikin kudin man fetur da 'yan Najeriya ke saye. Karamin Ministan ayyuka, Mohammed Goroyo ya bayyana cewa, ya kamata a gaggauta fara karbar wannan haraji musamman saboda gibin da gwamnati ke samu akan kudaden kula da titunan kasarnan. Yace kudin da ake bukata dan kula da titunan Najeriya sun kai Naira Biliyan 800 duk shekara amma kudin da Gwamnati ke baiwa ma'aikatar basu kaiwa hakan. Dan hakane suke bukatar a...
Babu Gwamnatin Data Samu Nasara da Muka samu a shekaru biyu da suka gabata a tarihin Najeriya>>Tinubu

Babu Gwamnatin Data Samu Nasara da Muka samu a shekaru biyu da suka gabata a tarihin Najeriya>>Tinubu

Duk Labarai
Ministan Yada labarai, Muhammad Idris ya bayyana cewa, babu Gwamnatin data samu nasarar da Gwamnatin Tinubu ta samu a shekaru 2 da suka yi suna mulki. Ya bayyana hakanne a Abuja wajan wani taron karawa juna Sani kan harkar tsaro da wayar da kan 'yan kasa. Yace babu gwamnatin data samu nasarar da Gwamnatin Tinubu ta samu a shekaru biyu da suka gabata, da farko dai ya yi maganin masu ci da tallafin man fetur. Da kuma masu almundahana a harkar canjin Kudi, Ga kuma bashin karatu da yake baiwa dalibai, ga gina Tintuna da sauransu.
Bidiyo: An yi kuskuren turawa Fasto Naira Miliyan 1 mimakon dubu dari a matsayin sadaka saidai da aka ce ya mayar da kudin, yace Kudin da aka baiwa Yesu sadaka ba’a mayar dasu, me kudin ya kira ‘yansanda

Wani kirista da yayi kuskuren aikawa fastonsa Naira Miliyan daya maimakon Naira dubu dari a matsayin kudin sadaka, ya nemi faston ya mayar masa da kudinsa. Saidai Faston yace sam bai yadda da wannan maganar ba, dan kuwa kudin da aka aikawa Yesu ba'a mayar dasu. https://twitter.com/yabaleftonline/status/1929622499706191993?t=XrZ-vhZIvZDOJGk75tvSvA&s=19 Saidai me kudin ya je ya dauko 'yansanda.
Hutun Sallah da jihar Kano ta baiwa Makarantu yayi yawa, Inji ‘yan Kudancin Najeriya yayin da suke caccakar gwamnatin jihar suna cewa dama ‘yan Arewa basu san muhimmancin ilimi ba

Hutun Sallah da jihar Kano ta baiwa Makarantu yayi yawa, Inji ‘yan Kudancin Najeriya yayin da suke caccakar gwamnatin jihar suna cewa dama ‘yan Arewa basu san muhimmancin ilimi ba

Duk Labarai
''Yan kudancin Najeriya da yawa ne suke caccakar Gwamnatin jihar Kano bayan da ta ayyana kusan sati biyu a matsayin hutun sallah. Gwamnatin jihar Kano ta sanar kwanaki 12 a matsayin hutun Sallah Babbah ga makarantu. A arewa wannan ba sabon abu bane musamman lura da yanda ake dadewa a Kano ana bukukuwan sallah da ziyarar 'yan uwa. Saidai 'yan Kudun a kafafen sada zumunta sun ta caccakar gwamnatin jihar Kanon suna dariya akai.