Sunday, December 21
Shadow
Jihohin Taraba, Adamawa, Borno da Yobe sun fada duhu bayan da wutar Lantarkinsu ta lalace, ji ranar da za’a gyara

Jihohin Taraba, Adamawa, Borno da Yobe sun fada duhu bayan da wutar Lantarkinsu ta lalace, ji ranar da za’a gyara

Duk Labarai
Jihohi 4 daga cikin 6 na yankin Arewa maso gabas, watau jihohin Taraba, Adamawa, Borno da Yobe sun fada duhu bayan da wutar lantarkinsu ta lalace. Da misalin karfe 10:00 am na safiyar ranar Talata, 10 ga watan Yuni ne wutar ta samu matsala. Kuma ana tsammanin sai nan da Ranar Asabar, da misalin karfe 5:00 pm za'a gyara wutar. Lamarin ya taba harkokin kasuwanci a jihar inda dama saidai su koma amfani da janareta, ko Sola wanda kuma basu da wannan saidai su hakura. Kamfanin Yola Electricity Distribution Company, YEDC yace dauke wutar ya zama dole dan a inganta injinan ko yanayin samar da wutar. Kamfanin ya bayyana jin dadin hakurik mutane da hadin kan da suka bayar kan wannan aiki.
Shugaban karamar hukuma ya rasu makonni bayan hawansa kujerar mulki a Katsina

Shugaban karamar hukuma ya rasu makonni bayan hawansa kujerar mulki a Katsina

Duk Labarai
Sabon zababben shugaban karamar hukumar Bakori da ke jihar Katsina, Hon. Aminu Dan Hamidu, ya rasu kasa da wata biyu bayan karbar rantsuwar kama aiki. Hon. Hamidu, wanda ya hau kujerar shugabancin karamar hukumar a watan Afrilu 2025, ya rasu a ranar Litinin, 9 ga Yuni, 2025. Har yanzu ba a bayyana musabbabin mutuwarsa a hukumance ba. Sai dai rahotanni da ba a tabbatar da su ba na nuna cewa yana fama da rashin lafiya tun kafin rasuwarsa. Kaula Mohammed, sakataren yada labarai ga Gwamna Dikko Umaru Radda, ya tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa. A cikin sanarwar, Gwamna Radda ya bayyana alhini da jimamin da ya shiga sakamakon rasuwar Hon. Hamidu, yana bayyana mamacin a matsayin “dan jam’iyya na kwarai, tsohon ma’aikacin gwamnati mai kwarewa, kuma ɗan siyasa na ƙasa da ya s...
Bèllò Tùrjì ya ƙaƙaba harajin Naira Miliyan 50 kan manoma a Zamfara da Neja

Bèllò Tùrjì ya ƙaƙaba harajin Naira Miliyan 50 kan manoma a Zamfara da Neja

Duk Labarai
Bello Turji ya ƙaƙaba harajin Naira Miliyan 50 kan manoma a Zamfara da Neja {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Mazauna wasu yankunan da dama a jihohin Zamfara da Neja sun sake shiga wani mawuyacin hali, bayan da sanannen jagoran ƴan bindiga, Bello Turji, ya bukaci a biya naira miliyan 50 kafin a basu damar fara aikin noma na bana. LEADERSHIP ta rawaito cewa wannan bukatar ta fito fili ne ta bakin wani mai nazarin tsaro mai suna Bakatsine, wanda ya wallafa bayani a shafinsa na X , inda ya bayyana cewa shugaban ƴan ...
Sanata Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur’ani a Kano

Sanata Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur’ani a Kano

Duk Labarai
Sanata Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur'ani a Kano Sanata Bashir Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur'ani da aka kammala kwanannan a jihar Kano. Kyaututtukan sun haɗa da gidaje biyu masu dakuna biyu da falo ga wadanda suka yi na biyu a gasar , da kuma gidaje masu dakuna uku ga wadanda suka yi na ɗaya a musabaƙar. Wadanda suka samu nasarar sun hada da:Maryam Abubakar Mu'az (wacce ta zo ta ɗaya a izifi 60 a mata, Ahmad Shu'aib (wanda ya yi ma daya a izifi 60 a maza), Zainab Hassan Shu'aib (ta biyu a izifi 60 a mata), da Ahmad Kabir Baturi (na biyu a izifi 60 a maza). Da ya ke jawabi jim kadan bayan mika mukullayen gidajen, Sen.Lado, wanda ya shirya gasar, ya ce an gudanar da ...
Kalli Bidiyon yanda Wike yake taka rawa a wajan kaddamar da babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja

Kalli Bidiyon yanda Wike yake taka rawa a wajan kaddamar da babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya taka rawa a wajan kaddamar da gyaran da akawa babban dakin taro na kasa da kasa. A yayin kaddamarwar ya taka rawa. Kuma an sakawa dakin taron sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. https://twitter.com/channelstv/status/1932465426044236257?t=qnSAyxARa3IcYTrLTu6Ffw&s=19 Lamarin ya dauki hankula inda wasu suka yaba, wasu kuwa kushewa suka yi.
Kalli Bidiyo: Fasto ya bayyana cewa, Kiristoci ya kamata su rika layya ba Musulmai ba

Kalli Bidiyo: Fasto ya bayyana cewa, Kiristoci ya kamata su rika layya ba Musulmai ba

Duk Labarai
Wannan wani fasto ne da ya dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan cewa, Kiristoci ne ya kamata su rika layya ba musulmai ba. A cikin bidiyon wa'azinsa a cocinsa, Faston ya bayyana tarihin layyar inda yace sune suka fi alaka da ita ba musulmai ba. https://twitter.com/AsakyGRN/status/1931978207919542634?t=dPTtS3iOFejah7DlOGZ87w&s=19 Wasu dai sun yadda dashi inda wasu suka ce basu yadda ba.
Kalli Bidiyo:Fasto Jeremiah Omoto Fufeyin ya samar da rigar bacci ga mata wadda yace idan mace ta saka ta ko likitoci sun ce mijinta ya daina haihuwa sai ya mata ciki

Kalli Bidiyo:Fasto Jeremiah Omoto Fufeyin ya samar da rigar bacci ga mata wadda yace idan mace ta saka ta ko likitoci sun ce mijinta ya daina haihuwa sai ya mata ciki

Duk Labarai
Fasto Jeremiah Omoto Fufeyin ya bayyana cewa, ya samar da wata riklgar bacci ga mata wadda ko likita yace maniyyin mijinki ya tsinke, to idan kika saka rigar sai kin dauki ciki. Faston ya bayyana rigarne a cocinsa inda aka ganta dauke da hotunansa. https://twitter.com/dammiedammie35/status/1932178002495807492?t=3BXzkL3hLAI2kAiCZoVvgQ&s=19 Lamarin ya zowa mutane da mamaki matuka.
Idan na ci amanar Tinubu na zama shedan kuma Allah sai ya azabtar dani>> Ministan Ayyuka David Umahi

Idan na ci amanar Tinubu na zama shedan kuma Allah sai ya azabtar dani>> Ministan Ayyuka David Umahi

Duk Labarai
Ministan ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa saboda yaddar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya masa, idan ya ci amanarsa ya zama shedan. Umahi yace Tinubu ya bashi aikin sayo kayan wani aiki da za'a yi da kudin suka kai Naira Tiriliyan 1.6, yace amma abin mamaki Tinubun bai taba kiransa ya ji ko ya ake ciki ba. Umahi yace na kowane zai iya maka wannan abin ba dan haka shi ya fada har a gaban Tinubu cewa, daga Allah sai shi a wadanda yake girmamawa dan yafi iyalansa. Umahi ya bayyana hakane a Abakaliki yayin ganawa da manema labarai.
Kalli Bidiyon yanda wata ‘yar kasuwa ta fashe da kuka bayan da ta aikawa kawarta Naira Miliyan 6 ta sayo mata jakunkuna daga kasar China amma ta aiko mata kwali ba komai a ciki

Kalli Bidiyon yanda wata ‘yar kasuwa ta fashe da kuka bayan da ta aikawa kawarta Naira Miliyan 6 ta sayo mata jakunkuna daga kasar China amma ta aiko mata kwali ba komai a ciki

Duk Labarai
Wannan wata budurwace data aikawa kawarta da Miliyan 6 ta sayo mata da jakunkuna daga kasar China. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1932439373796024600?t=QekclgWoU8diB80kAAua1g&s=19 Saidai ta aiko mata da kwali babu komai a ciki, lamarin yasa ya fashe da kuka tana fadin gaba daya kudinta ne ta aika mata.