Sunday, December 21
Shadow
Kalli Bidiyo: Matashi ya yi fatan shi da mahaifiyara su dawwama a wutar Jahannama saboda ta haifoshi yana wahala

Kalli Bidiyo: Matashi ya yi fatan shi da mahaifiyara su dawwama a wutar Jahannama saboda ta haifoshi yana wahala

Duk Labarai
Wani matashi na shan Tofin Allah tsine bayan da yayi wani Bidiyo yana tsinewa mahaifiyarsa inda yace ta haifishi yana shan wahala abinci ma da kyar yake samu. Da yawa sun tsine masa inda suka rika tunawa mutane da su rika yin addu'ar Kwanciya da iyali dan ana tunanin hakan zai sa ba za'a rika haifo irinsa ba. https://www.tiktok.com/@danharuna44/video/7512774919676071173?_t=ZM-8x5VUudR9x0&_r=1 Saidai matashin ya bayyana cewa dan neman suna yayi kuma da talauci, inda yace iyayensa mutanen kirki ne kuma baya son a zagesu. https://www.tiktok.com/@danharuna44/video/7514262265588157702?_t=ZM-8x5Vf2vz8OW&_r=1 Wasu dai sun bayar da shawarar a kai yaron gidan mahaukata dan da alamar yana da tabin hankali.
Ba zamu baiwa Atiku takarar shugaban kasa a 2027 ba, dan kudu zamu tsayar takarar shugaban kasa a PDP>>Inji Wike

Ba zamu baiwa Atiku takarar shugaban kasa a 2027 ba, dan kudu zamu tsayar takarar shugaban kasa a PDP>>Inji Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya nanata cewa dole jam'iyyar PDP ta tsayar da dan takara daga kudancin Najeriya a shekarar 2027. Wike ya bayyana hakane a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da ya gudana ranar Litinin a Abuja. An gudanar da taronne dan warware matsalar dake tattare da jam'iyyar da kuma saitawa jam'iyyar Alkibla. Wike yayi gargadin cewa jam'iyyar PDP ta kama hanyar kashe kanta inda yace idan ba'a gyara ba aka ajiye jiji da kai da son rai ba, abinda ya faru a jam'iyyar a shekarar 2023 zai sake maimaita kansa. Yace kuma idan ana son Adalci da amfani da tsarin raba daidai da tsarin mulkin jam'iyyar PDP, dole a tsayar da dan takara daga kudancin Najeriya a jam'iyyar ta PDP.
Kalli Bidiyon me dokar bacci: An kama Dansanda na satar Wayar wutar Lantarki

Kalli Bidiyon me dokar bacci: An kama Dansanda na satar Wayar wutar Lantarki

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wannan wani dansanda ne da aka kama bisa zargin satar Wutar Lantarki. Rahoton yace an kamashi ne a Makurdi, babban birnin jihar Benue inda jamaa suka dakeshi. A Bidiyon an ganshi rigarshi da jini inda kuma ya amsa laifinsa da inda ya sato wayoyin wutar da aka ganshi dasu. Kalli Bidiyon anan Da yawa dai sun yi Allah wadai da halinsa.
Kalli Bidiyo: An kama jami’in Soja da ma’aikacin hukumar kula da gidan gyara hali suna Fàshì da makami

Kalli Bidiyo: An kama jami’in Soja da ma’aikacin hukumar kula da gidan gyara hali suna Fàshì da makami

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wannan wasu jami'an tsaro ne, daya sojan ne dayan kuma jami'in hukumar kula da gidajen gyaran hali ne da aka kama bisa zargin fashi da makami. Dukansu sun amsa laifukan da ake zarginsu. An dai gansu cikin shigar kayan sojoji. Kalli Bidiyon anan: Da yawa dai sun bayyana su a matsayin maciya amanar kasa.
Sojoji Sun Kàshè Manyan masu ikirarin Jìhàdì A jihar Bòrnò

Sojoji Sun Kàshè Manyan masu ikirarin Jìhàdì A jihar Bòrnò

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} A ranar Litinin, 9 ga watan Yuni 2025, dakarun haɗin gwiwa na sojoji sun kai farmaki maɓoyar ƴan ta’adda na Boko Haram da ISWAP a Nzalgana da ke ƙaramar hukumar Gujba da kuma yankin Timbuktu Triangle. Sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na X ta ce an kashe ƴan ta’adda da dama ciki har da jagororinsu. Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Ameer Malam Jidda, wani babban kwamanda da ke da tasiri a ƙauyukan Ngorgore da Malumti. Sojojin sun ƙara cewa sun kuma ƙwato makamai da was...
Ka shiga taitayinka, naga take-takenka baka a da’a>>Shugaba Tinubu ya gargadi Sanata Ali Ndume bayan da yace ‘yan Najeriya na cikin wahala

Ka shiga taitayinka, naga take-takenka baka a da’a>>Shugaba Tinubu ya gargadi Sanata Ali Ndume bayan da yace ‘yan Najeriya na cikin wahala

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Fadar shugaban kasar Najeriya ta gargadi Sanata Ali Ndume kan kalaman da yake yi wanda ta kira na rashin da'a ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Fadar shugaban kasar tace akwai rashin da'a a cikin kalaman na sanata Ali Ndume. Sanarwar ta fito ne daga bakin me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga inda yace maganar da Sanata Ndume yayi cewa akwai masu satar kudin talakawa da wadanda basu cancanta ba a cikin gwamnatin Tinubu bai kawo wata hujja akan ta ba. Yace Ndume n...
Duk da ni dan APC ne, bana goyon bayan Tinubu ya zarce a 2027 saboda ‘yan Najeriya na cikin wahala>>Inji Sanata Ali Ndume

Duk da ni dan APC ne, bana goyon bayan Tinubu ya zarce a 2027 saboda ‘yan Najeriya na cikin wahala>>Inji Sanata Ali Ndume

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume wanda ya fito daga jihar Borno ya bayyana cewa baya cikin 'yan jam'iyyar APC da suke neman shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce. Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Sanata Ali Ndume yace dalilinsa kuwa shine lamura sun kazance a kasarnan inda farashin kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabo, ga matsalar tsaro kuma rayuwa ta wa talaka tsanani. Yace 'yan Najeriya basa hangen wani abin ci gaba a gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu. Yace kuma kada shugaba Tinubu ya rudu da maganar Gwamnonin APC da suka ce suna goyon bayansa, ya tuna cewa, Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan gwamnoni 22 suka goyi bayansa amma duk da haka ya fadi zabe.
Ba dan kin goyon bayan Atiku da muka yi ba da yanzu ya jefa kasar cikin wahala da rikici>>Inji Wike

Ba dan kin goyon bayan Atiku da muka yi ba da yanzu ya jefa kasar cikin wahala da rikici>>Inji Wike

Duk Labarai
Ministan babban Birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa ba dan kin goyon bayan Atiku Abubakar da suka yi ba shi da gwamnoni da suka kira kansu da G5 ba da Tuni kasarnan na cikin rikici. Wike da sauran gwamnonin da suka hada dana Seyi Makinde na jihar Oyo da Samuel Ortom na jihar Benue, da Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Ifeanyi Uguanyi na jihar Enugu ne suka hadewa Atiku kai. Sun ce ba zasu goyi bayan Atiku ba inda suka goyi bayan Tinubu wanda hakan na daga cikin dalilin da yasa Atiku Abubakar ya fadi zabe. Wike a wajan taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa, ba su yi nadamar abinda suka aikata ba. Yace duk da rikicin dake cikin PDP, jam'iyyar ba zata ruguje ba. Ya bayyana cewa a ko da yaushe bin dokar jam'iyya da na kundin tsarin mulkin Najeriy...
Da Duminsa: Bayan Buratai: ‘Yan Bìndìgà sun sake baiwa wani baban dan siyasa hari

Da Duminsa: Bayan Buratai: ‘Yan Bìndìgà sun sake baiwa wani baban dan siyasa hari

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Abia na cewa, 'yan Bindiga sun budewa motar kwamishinan gidaje na jihar, Mr. Chaka Chukwumerije wuta inda suka fasa gilasan motar. Lamarin ya farune da daren ranar Asabar akan titin Enugu-Umuahia dake jihar Imo. Rahotanni sun ce lamarin ya farune a yayin da dan siyasar ya baro mahaifarsa, Umunneochi yana kan hanyar zuwa Umuahia. Akwai mutane 3 da suka rakashi saidai babu wanda ya jikkata a harin amma motarsu ta lalace da harin harsashi. A jawabinsa bayan faruwar lamarin, Chukwumerije ya bayyana cewa, Allah ne ya tsaresu a harin daya faru inda yace lamarin ya matukar girgizashi.