Monday, December 22
Shadow
Kasashen Larabawa sun yi Allah wadai da kasar Israyla saboda hanasu kaiwa Falasdiynawa ziyara da ta yi

Kasashen Larabawa sun yi Allah wadai da kasar Israyla saboda hanasu kaiwa Falasdiynawa ziyara da ta yi

Duk Labarai
Ministocin harkokin wajen ƙasashen Larabawa sun bayyana rashin jin daɗinsu ga gwamnatin Isra'ila, game da rashin amincewa da tawagar ƙungiyar ƙasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gaɓar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasɗinawa. A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa'ud, ya ce matakin da Isra'ila ta ɗauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya. A ranar Asabar wani jami'in Isra'ila ya ce batun samar da ƙasar Falasɗinu ne manufar ziyarar. Cikin wata sanarwar haɗin-gwiwa, ƙasashen Masar da Qatar sun ce za su ruɓanya ƙoƙarinsu don a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza. Shugaban ƙungiyar ƙasashen Larabawa da ministoci huɗu sun gana da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ta kafar Intanet....
Mutanen da ambaliyar ruwa ta kàshè a Neja sun kai 200, in ji jami’ai

Mutanen da ambaliyar ruwa ta kàshè a Neja sun kai 200, in ji jami’ai

Duk Labarai
Mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a garin Mokwa na jihar Neja sun kai sama da 200, in ji jami'ai. Akwai wasu kusan 500 da ba a gani ba har yanzu, yayin da ake ci gaba da aikin ceto. Mataimakin shugaban karamar hukumar Mokwa, Musa Kimboku ya shaida wa BBC cewa an dakatar da aikin ceto saboda hukumomi sun yi imanin cewa watakila babu wanda ya rage da rai. Ambaliyar wadda aka bayyana cewa ba a ga irinta ba tsawon shekara 60, ta lalata gidaje a anguwannin Tiffin Maza da Hausawa, bayan tafka mamakon ruwan sama ranar Laraba da daddare. Hukumomi za su fara tono gawawwaki da aka binne don bincike, a wani yunkuri na kauce wa yaɗuwar cutuka, kamar yadda Maigarin Mokwa Muhammad Aliyu ya bayyana. Mazauna yankin sun bayyana cikin kaɗuwa yadda suna kallo suka rasa ƴan uwansu da gidajensu...
Kalli Bidiyo yanda sojojin Israyla suka budewa Falasdiynawa wuta suka kàshè 22 yayin da suka taru suna karbar Tallafin Abinci

Kalli Bidiyo yanda sojojin Israyla suka budewa Falasdiynawa wuta suka kàshè 22 yayin da suka taru suna karbar Tallafin Abinci

Duk Labarai
Rahotanni daga Falasdinu na cewa, Sojojin kasar Israela, IDF sun budewa taron Falasdiynawa wuta a yayin da suka taru suke karbar tallafin abinci. Lamarin yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla mutane 22. Wakilin majalisar Dinkin Duniya ya bayyanawa Kamfanin dillancin labaran AFP cewa raba kayan tallafi a gaza ya zama tarkon Mutuwa. Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta tabbatar da faruwar lamarin. Saidai wata gidauniyar agaji a Gaza tace rahoton bashi da inganci. Kalli Bidiyon anan
Ma’aikatan Shari’a zasu tsunduma yajin aikin sai mama ta gani gobe, Litinin

Ma’aikatan Shari’a zasu tsunduma yajin aikin sai mama ta gani gobe, Litinin

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Ma'aikatan shari'a na Najeriya karkashin Kungiyarsu ta (JUSUN) sun nace akan tafiya yajin aiki gobe, Litinin, 2 ga watan Mayu. Ma'aikatan bangaren babbar kotun tarayya ne zasu tafi yajin aikin inda bangaren kotun Koli suka fasa shiga yajinnaikin. Wata majiya tace shugaban hukumar DSS ya zauna da ma'aikatan tsawon awanni 4 amma duk da haka sun ce ba zasu fasa tafiya wannan yajin aikin ba. Sakataren kungiyar, Comrade Mohammed Isah yace zasu fara yajin aikin gobe Litinin inda yace yana kiran duka ma'aikatansu da su zauna a gida kada su je wajan aiki. Saidai yace a goben ma akwai wani zama sa za'a sake yi.
Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu ya jefa Mutanen Najeriya cikin matsanancin Talauci>>Inji Janar Buratai

Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu ya jefa Mutanen Najeriya cikin matsanancin Talauci>>Inji Janar Buratai

Duk Labarai
Tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta jefa 'yan Najeriya cikin matsin talauci. Ya bayyana hakane a wajan taron zagayowar ranar haihuwar tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi. Yace gwamnatocin baya a hankali suka rika jefa 'yan Najeriya cikin talauci amma Gwamnatin Tinubu, Lokaci guda ta jefa mutane saboda tsare-tsaren ta data gudanar masu tsauri. Saidai yayi fatan nan da shekaru biyu masu zuwa a samu saukin rayuwa wanda yace idan ba haka ba, akwai matsala.
Kasar Ìran ta Kàshè wani munafiki dan kasarta dakewa Kasar Israyla leken Asiri tana biyanshi kudi

Kasar Ìran ta Kàshè wani munafiki dan kasarta dakewa Kasar Israyla leken Asiri tana biyanshi kudi

Duk Labarai
Kasar Iran ta kàshè wani dan kasarta me suna Pedram Madani dan kimanin shekaru 41 wanda ijiniya ne saboda samunsa da laifin yiwa kasar Israyla leken Asiri a Iran din. An kashe shine ta hanyar Rataya bayan samunsa da laifin haduwa da wakilan kungiyar leken Asirin kasar Israela ta Mossad da karbar kudi yana musu aiki. An ratayeshine ranar 28 ga watan Mayu a gidan yarin Ghezelhesar Prison, Karaj. Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi Allah wadai da lamarin.
Jihar Ekiti ta Haramta Shan Tàbà

Jihar Ekiti ta Haramta Shan Tàbà

Duk Labarai
Jihar Ekiti, ta haramta shan Taba a babban birnin jihar, Ado Ekiti. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Felani Oyebanji ne ya bayyana hakan a wajan zagayowar ranar yaki da shan taba ta Duniya a birnin Ado Ekiti. Yace illar da taba kewa lafiyar dan adam ce tasa suka dauki wannan mataki. A wani labari me kama da wannan ma, kasar Faransa ma na shirin haramta shan taba sigari.