Monday, March 30
Shadow
Da Duminsa:Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za’a yi zaben shugaban kasa na shekarar 2027

Da Duminsa:Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za’a yi zaben shugaban kasa na shekarar 2027

Duk Labarai
Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta sanar da ranar 20 ga watan Fabrairu na shekarar 2027 a matsayin ranar da za'a gudanar da zaben shugaban kasa na shekarar 2027. Shugaban Hukumar zaben, Professor Joash Amupitan ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja ranar Juma'a. Yace zaben shugaban kasa dana 'yan majalisun tarayya za'a yishi ne ranar 20 ga watan Fabrairu inda kuma zaben Gwamnoni dana 'yan majalisar jihohi za'a yishi ne ranar 6 ga watan Maris. Ya bayyana cewa, sun shirya tsaf dan gudanar da zaben.
Kalli Bidiyon: Wasu matasan Sojojin Najeriya na shan Allah wadai saboda shiga gasar rawa a Tiktok

Kalli Bidiyon: Wasu matasan Sojojin Najeriya na shan Allah wadai saboda shiga gasar rawa a Tiktok

Duk Labarai
Wasu matasan Sojojin Najeriya na ci gaba da shan ruwan Allah wadai bayan da suka shiga gasar rawa a Tiktok. Gasar rawar ta samo asali ne bayan da wata matashiya ta bayyana ta soke waya a kugunta tana rawa, Bidiyon ta ya watsu sosai inda akai ta kwaikwayarta. Suma matasan sojojin sanye da kakinsu, an gansu sun yi irin wannan rawa sun dora a shafinsu na sada zumunta. Saidai lamarin ya jawo musu Allah wadai. https://www.tiktok.com/@gangasoja/video/7605187232965692692?_r=1&_t=ZS-93soWnaWDi5
Kalli Bidiyon: Abokan Gfresh Al-amin sun ce Saki 3 yawa Maryam Nicki Minaj amma gashi ya mayar da ita bata sake wani Auren ba

Kalli Bidiyon: Abokan Gfresh Al-amin sun ce Saki 3 yawa Maryam Nicki Minaj amma gashi ya mayar da ita bata sake wani Auren ba

Duk Labarai
Ana ta bararrabi tsakanin tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin da matarsa, Maryam Nicky Minaj da ya ce ya mayar da ita da abokansu. Abokan Gfresh Al-amin sun bayyana cewa, saki 3 yawa Maryam, a yayin da Gfresh din da Maryam ke cewa, Saki 2 ne tsakaninsu. A jiyane dai Gfresh ya fito a shafinsa na Tiktok yace ya mayar da matar tasa. https://www.tiktok.com/@u.s2824/video/7605739632839396626?_r=1&_t=ZS-93siMk639er https://www.tiktok.com/@feefy71/video/7606216375094250772?_r=1&_t=ZS-93sjuHyZcpN
Makwabcin Mutuminnan na Kano da ya kashe Naira Biliyan 1.5 ya gayyato Davido saboda Birthday din ‘ya’yansa ya bayyana halinsa

Makwabcin Mutuminnan na Kano da ya kashe Naira Biliyan 1.5 ya gayyato Davido saboda Birthday din ‘ya’yansa ya bayyana halinsa

Duk Labarai
Makwabcin mutuminnan na Kano wanda ya dauki hankula saboda Birthday din 'ya'yansa ya yi karin haske akan abinda mutane ke cewa na suka akan mutumin. A wata hira da aka yi dashi wadda ta dauki hankula a kafafen sada zumunta. An ga makwabcin mutumin na cewa, yana da kyauta sosai, shi yasa aka musu titi a layinsu, kuma me dubu-dubu suke ce masa saboda idan ya fara rabon Naira Dubu-dubu daga safe har yamma. Hakanan Akwai 'ya'yan makwabta da ya dauka aiki a kamfaninsa. https://www.tiktok.com/@abdul__turakee1/video/7606075685144218888?_r=1&_t=ZS-93sgkVl47tZ
Kalli Cikakken Bidiyon hirar da BBChausa ta yi da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Kalli Cikakken Bidiyon hirar da BBChausa ta yi da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Duk Labarai
Bayan yunkurin da DSS suka yi na kama tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a filin jirgin sama bayan ya dawo daga kasar Egypt. BBChausa, ta yi hira dashi A hirar wani abu da ya dauki hankula shina rashin saka maballin rigarsa. Ya tabbatar da cewa, EFCC sun gayyaceshi kuma zai amsa gayyatarsu ranar Litinin. Hakanan kuma yace APC Azzalumace amma dansa Bello Baya zalunci saboda irin tarbiyyar da ya bashi. https://twitter.com/i/status/2022175373933289806
Da Duminsa: Bayan da aka yi Yunkurin kamashi a filin Jirgi, EFCC tace ta aikawa Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sammace

Da Duminsa: Bayan da aka yi Yunkurin kamashi a filin Jirgi, EFCC tace ta aikawa Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sammace

Duk Labarai
Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa, ta aikawa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sammacen ya bayyana a gabanta. Hakan na zuwane bayan da aka yi yunkurin kamashi a filin jirgi amma abu ya faskara. Rahotanni sun bayyana cewa, Lauyoyin EFCC ne suka tabbatar da hakan. Kuma sun ce, ElRufai ya amsa musu da cewa, zai bayyana a gaban EFCC din ranar Litinin.
Da Duminsa: Atiku Abubakar ya kaiwa Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ziyara har gida bayan da aka yi yunkurin kamashi

Da Duminsa: Atiku Abubakar ya kaiwa Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ziyara har gida bayan da aka yi yunkurin kamashi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kaiwa tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ziyara a gidansa. Hakan na zuwane bayan da DSS suka yi yunkurin kama ElRufai a filin jirgin sama bayan da ya dawo Najeriya daga Egypt. Babu dai wani bayani game da ganawar tasu. Hakan na zuwane bayan da Rotimi Amaechi ya kaiwa ElRufai ziyara har gida inda shima ya nuna masa yana tare dashi.