Talauci ne tushen matsalar tsaron arewacin Najeriya – Gwamnan Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce tsansar talauci da koma bayan tattalin arziki su ne manyan abubuwan da ke haifar da masaloli tsaro a yankin arewacin Najeriya, inda ya yi gargaɗin cewa muddin ba a magance su gaba ɗaya ba to yankin zai ci gaba da fuskantar matsalolin tashe-tashen hankaln.
Gwamnan ya bayyana hakan a cikin shirin siyasa na Sunday Politics na gidan talibijin na Channels, inda ya ce gwamnatinsa ta soma ne da fito da hanyoyin yaƙi da talauci da rashin aikin yi tsakanin matasa, inda ya alaƙanta hakan ga irin ƙwarewar da ya ya samu lokacin da ya ke shugaban kwamitin da ke lura da bankuna na majalisar dattawan a lokacin yana ɗan majalsar dattawan.
"Lokacin da aka zaɓe ni a matsayin gwamnan Kaduna, abinda na soma yi shi ne duba girman matsalar talaucin da ake fama...








