Saturday, December 20
Shadow
Sabon Fafaroma, Pope Leo ya jawo cece-kuce bayan da yace ba ruwansa da masu auren jinsi

Sabon Fafaroma, Pope Leo ya jawo cece-kuce bayan da yace ba ruwansa da masu auren jinsi

Duk Labarai
Sabon Paparoma Pope Leo XIV ya bayyana cewa, aure tsakanin mace da namiji ne suka gani a Baibul. Lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke yaba masa, wasu kuma na sukarsa. Fafaroma da ya mutu, Pope Francis yayi suna sosai wajan nemawa 'yan Madigo da Luwadi da masu auren jinsi 'yanci. Wannan magana da sabon fafaroman yayi ana ganin ya zo da sabon canji.
Arewa maso yamma ta Tinubu ce a 2027>>Inji APC

Arewa maso yamma ta Tinubu ce a 2027>>Inji APC

Duk Labarai
APC a shiyyar Arewa-maso-yamma ta sanar da goyon bayan ta ga Tinubu a zaɓen 2027. Jam'iyyar APC a shiyyar Arewa-maso-yamma ta kada kuri'ar amincewa da shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takara gabanin zaben shugaban kasa na 2027. An bayar da amincewar ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kaduna a jiya Asabar, inda kuma aka amince da Tinubu a matsayin dan takarar daya tilo. A cikin sanarwar da Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna ya karanta, shiyyar ta jaddada biyayyar ta ga jam’iyyar APC tare da yin alkawarin “cikakken goyon baya ga manufar shugaba Tinubu na samar da wadata, daidaito da kuma sauyi mai dorewa ga daukacin ‘yan Najeriya”. “Muna godewa kuma muna yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa kyakkyawan jagoranci da ya ke yi, da sauye-sauyen da ya yi,...
Tinubu ya dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-Yamma, inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani

Tinubu ya dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-Yamma, inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani

Duk Labarai
Tinubu ya dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-Yamma, inji Uba Sani. Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya daidaita harkar tsaro a yankin Arewa maso Yamma tare da farfado da harkokin noma da 'yan ta'adda suka durkusar da su a baya. Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar, Sani ya ce yankin da a da ke zama cibiyar ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga, yanzu yana samun sauyi mai ma’ana. “Tun kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023, yankin Arewa maso Yamma ne cibiyar ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifukan tashin hankali,” in ji shi. “Ba za ka iya yin tafiya daga wuri zuwa wani wuri ba. Manoma ba za su iya zuwa gonakinsu ba. Rayuwa ta kasance...
Akwai fargabar dabbobi za su yi tsada lokacin babban sallah a Najeriya

Akwai fargabar dabbobi za su yi tsada lokacin babban sallah a Najeriya

Duk Labarai
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu fataucin dabbobi da kayan abinci a Najeriya, ta ce akwai fargabar dabbobi za su iya yin tsada a lokacin babbar sallah. Sun ce hakan zai iya faruwa ne saboda takunkumin da gwamnatin Nijar ta saka na haramta fitar da dabbobi zuwa ƙasashen waje. Ƴan kasuwar sun roki hukumomin Nijar su kalli maslahar al’umma su cire haramcin. Shugaban ƙungiyar, Dakta Muhammad Tahir ya shaida wa BBC cewa za a samu koma-baya a harkar sayar da dabbobi. "Idan gwamnatin Nijar tana ganin matakin da ta ɗauka shi ne zai kawo saukin abubuwa, to gaskiya akwai matsala, saboda ƴan Nijar da ke hada-hadar dabbobin idan ba su samu mai saye ba babban koma-baya ne," in ji shi. Ya ce akwai shanu da raguna sama da 50,000 waɗanda aka saya daga Chadi, inda yanzu haka suke maƙale a iyakar Cha...
Gwamnatin Borno ta haramta sare itatuwa ba bisa ka’ida ba

Gwamnatin Borno ta haramta sare itatuwa ba bisa ka’ida ba

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Borno ta amince da kudurin haramta sare itatuwa ba bisa ka'ida ba a faɗin jihar. Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya sanar da haka ranar Juma'a, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin kare muhalli da inganta lafiyar al'umma. Haka kuma, gwamnan ya amince da kudurin tsaftace muhalli wanda za a riƙa yin shara a a kowace Asabar ɗin farkon wata a faɗin jihar. "A don haka, duk wani mutum da aka samu yana sare itatuwa ba bisa ka'ida ba, za a ci tararsa naira 250,000 ko kuma ɗaurin shekara uku a gidan yari. Idan ya sake aikata laifin, hukuncinsa shi ne ɗaurin shekara biyar ko tarar naira 500,000 ko kuma a zartas masa da duka hukuncin," in ji gwamna Zulum. Gwamnan ya ce waɗanda aka samu ba sa tsaftace muhallinsu za a ci su tarar da ta kai naira 100,000 saboda saɓa wa umarnin...
Tinubu zan mara wa baya a zaɓen 2027 – Wike

Tinubu zan mara wa baya a zaɓen 2027 – Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce ba zai yi takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027 ba, sannan zai mara wa Tinubu baya. Wike ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da sashen Pidgin na BBC, inda ya ce har yanzu shi ɗan jam'iyyar PDP ne. "Ba zan sake yin takara ba. Ba zan yi takara da mutumin da nake yi wa aiki ba. Waye zai yi nasara idan ba shi ba?" kamar yadda Wike ya faɗa. Wike wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Rivers, ya yi takarar zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP don zama ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, sai dai ya yi rashin nasara a hannun tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar. Ministan na Abuja ya kuma nuna ɓacin-ransa kan matakin jam'iyyar na kin ware tikitin takarar shugaban ƙasa wa yankin kudu, abin da ya janyo ta faɗa rikici...
Kudi na Kauye: Mutanen Kauyen Bauchi Dake kan hanyar zuwa Saudiyya sun dauki hankula bayan da suka dauki hotuna da farar Budurwa me aiki a cikin jirgin sama

Kudi na Kauye: Mutanen Kauyen Bauchi Dake kan hanyar zuwa Saudiyya sun dauki hankula bayan da suka dauki hotuna da farar Budurwa me aiki a cikin jirgin sama

Duk Labarai
Mutanen Bauchi dake kan hanyar zuwa Kasar Saudiyya sun dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta bayan da aka gansu suna daukar hotuna da farar budurwa me aikin cikin jirgi. Da yawa sun bayyana sha'awar lamarin inda aka rika cewa kudi na Kauye https://twitter.com/Sadeeq_Malo/status/1923781115208233070?t=0VK5P3ufXddZ4Ts4xyU_Jg&s=19 Hotunan sun dauki hankula sosai.