Gwamnan Zulum ya isa garin Marte garin da 'yan ta'adan BH suka kai mummunan hari kwanan nan, inda Gwamnan zai kwana a can tare da tawagarshi.
Muna Addu'ar Allah ya kawo mana karshen wannan musifan da ta addabi yankinmu na Arewa dama kasarmu Najeriya.
A wani gagarumin samame da suka gudanar, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da samun nasarar hallaka babban makusancin shugaban 'yan Bîndîgâ, Bello Turji, wato Alhaji Shaudo Alku, a ranar 18 ga Mayu, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan artabu ya auku ne a kusa da makarantar Tunfa da ke ƙaramar hukumar Isa, Jihar Sokoto. Rundunar ta ce an kashe tare da su wasu daga cikin mabiyansu da dama, ciki har da masu hannu wajen kai hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Wannan nasara na daga cikin kokarin da hukumomin tsaro ke ci gaba da yi don murkushe ayyukan ta’addanci da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
Allah ya kara tsare ƙasarmu da kuma bai wa jami’an tsaro nasara akan dukkan masu kawo fitina.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi da tsohon Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi sun hadu a fadar Vatican wajan rantsar da sabon Fafaroma Leo XIV.
Kayode Fayemi ne yawa Peter Obi jagoranci zuwa wajan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda ya fara magana da cewa, Shugaban kasa barka da zuwa cocin mu, mun gode da ka amsa gayyatar Fafaroma.
Tinubu ya amsa da cewa nine ya kamata ace na muku barka da zuwa.
Yace nine shugaban tawagar Najeriya a wannan taron, sun amsa masa da cewa dukkansu suna karkashin Tawagarsa.
Karamin yaro dan shekaru 16 ya dauki Bindigar mahaifinsa ya harbe kanwarsa ta mutu har lahira a jihar Delta.
Kakakin 'yansandan jihar, Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace lamarin akwai sosa Zuciya.
Ya kara da cewa, mahaifin yace shi mafarauci ne kuma dan nasa yakan rika wasa da Bindigar.
Yace zuwa ya zu ba'a kai ga tantance sunayen wadanda lamarin ya faru dasu ba.
Dattijon Jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa a yanzu babu dan siyasar dake da karbuwa kamar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN inda yace Tinubu bai yi wa Arewa Laifin komai ba.
Yace APC ce ke rike da mafi yawan jihohi kuna ko jihohin da jam'iyyar Adawa ke rike dasu duk sun nuna goyon bayan Tinubu dan haka bai ga me kada shi ba.
Yace amma watakila abubuwa na iya canjawa inda yace amma maganar gaskiya a yanda ake tafiya bai ga wani abu da zai hana Tinubu zarcewa a shekarar 2027 ba.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami'anta sun kama wani dattijo mai suna Ayuba Ashiru mai shekara 80 da kilo 2.3 na miyagun ƙwayoyi.
A wata sanarwa da kakakin hukumar na ƙasa Femi Babafemi ya fitar wadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 14 ga Mayun 2025 a yankin Dogarawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Garin jihar Kaduna ne bayan samun bayanan sirri a game da harƙallarsa.
Sanarwar ta ce an taɓa kama Ashirun bisa fataucin miyagun ƙwayoyi, aka ɗaure na shekara goma tsakanin 2014 zuwa 2024.
"Ya ce ya kasance a harƙallar fataucin miyagun ƙwayoyi na tsawon shekara 46," kamar yadda sanarwar ta nuna.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa jami'an hukumar sun kama wata dattijuwa mai suna Uloma Uchechi Su...
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja sun bayyana cewa, jami'an tsaro sun kama rikakken dan Bindiga da ake nema ruwa a Jallo cikin maniyyatan da ake tantance wa.
Sunan wanda aka kama din shine Yahaya Zango wanda jami'an tsaro sun jima da saka sunansa cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.
Ya je wajan tantance Alhazai inda ya bayar da fasfo dinsa nan kuwa jami'an DSS suka yi ram dashi aka wuce ofis dashi, kamar yanda Jaridar daily Trust ta ruwaito.
Wani tsohon sojan Najeriya wanda ya ajiye aikin da karfinsa me suna Abubakar Afan ya bayyana cewa an masa tayin zuwa kasar Rasha dan ya tayasu yaki da Ukraine a bashi Naira Miliyan 21 amma yaki.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a kafar Punchng inda yace dalilinsa na kin zuwa shine yasan addinin musulunci ya hana yin yaki saboda kudi, yace idan ya mutu bai san matsayinsa a wajan Allah ba.
Yace sannan akwai abokansa da sukewa Ukraine yaki bai san yanda zai yi ba idan ya je shi kuma yanawa Rasha yaki, shin zai je ya kashe abokan nasa ne?
Yace rayuwarsa ta fi kudin muhimmanci inda yace matarsa ma tace masa bata yadda yaje ba tunda dai basu rasa komai ba.
Yace a yanzu haka ya samu wani aiki ne a kasar Egypt inda yake can yayin da ya bar matarsa a gida Najeriya.
Wani Soja da ya shekara 2 bai ga iyalinsa ba, ya je wucewa ta garinsu inda ya tsaya suka gana da iyalin nasa a bakin titi.
https://twitter.com/Nasir1on1/status/1923995699449827565?t=qPo_i7XgAs8IR_EGa-e99Q&s=19
Lamarin ya dauki hankula sosai inda a kafafen sada zumunta inda akai ta sanya musu albarka da fatan Alheri.
Sabon Paparoma Pope Leo XIV ya bayyana cewa, aure tsakanin mace da namiji ne suka gani a Baibul.
Lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke yaba masa, wasu kuma na sukarsa.
Fafaroma da ya mutu, Pope Francis yayi suna sosai wajan nemawa 'yan Madigo da Luwadi da masu auren jinsi 'yanci.
Wannan magana da sabon fafaroman yayi ana ganin ya zo da sabon canji.