INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN.
Ƴañ Bìñdiga Sun Sace Fatima Adam Tare Da Wasu Mutane Dake Cikin Motar Su A Jihar Zamfara, Cikin Daren Yau Litinin
Allah Ya Kuɓutar Da Su Cikin Aminci!
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Israela ta amince da matakin kwace gaba dayan yankin Gaza ya koma karkashin mulkinta.
Dan hakane ta kirawo duka sojojinta da suka yi ritaya dana karta kwana dan gudanar da wannan gagarumin aikin.
Israela dai bata bayyana zuwa yaushene zata rike zirin na gaza ba watau saidai abinda Allah yayi.
Kasar ta Israela tace a wannan sabon mataki zata bari a shiga da kayan agaji cikin Gaza amma zata saka ido ta tabbatar basu fada hannun kungiyar Hamas ba.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, saura kiris ya daina jin labarai da karanta jaridu saboda yanda yake ganin 'yan Najeriya a cikin wahala.
Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar Katsina.
Yace amma duk da haka ya dage ya tsaya tsayin daka dan tabbatar da ganin ya dora Najeriya a turbar gaskiya.
Shugaba Tinubu yace kuma zuwa yanzu an fara ganin sakamakon matakan da ya dauka.
Inda yace lamura sun fara dawowa daidai
Rahotanni sun ce manhajar WhatsApp da ake amfani da ita wajan Chatin da kasuwanci da sada zumunta zata daina aiki a cikin wayoyi kirar iPhone guda 3.
Masu irin wadannan wayoyi saidai ko su canja waya ko kuma su yi upgrading Operation System dinsu.
Kamfanin Meta wanda shi ke da WhatsApp yace daga yanzu wayoyi masu manhajar iOS 15.1 zuwa sama ne kawai zasu iya amfani da WhatsApp.
Hakan na nufin wayoyin iPhone 5s, iPhone 6, da iPhone 6 Plus duk ba zasu iya yin amfani da WhatsApp ba.
Kakakin WhatsApp ya shaida cewa a duk shekara sukan duba su ga wace waya ce ta fi tsufa wadda kuma babu mutane da yawa dake amfani da ita sai su dakatar da WhatsApp akanta.
Sunce wadannan wayoyi basu da manhajojin tsaro da ya kamata.
Wadannan wayoyi dai an yisu ne tsawon shekaru sama da 10 kuma ...
INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Mahaifin Abale Ya Rasu.
Za a yi jana'izarsa bayan sallar la'asar a Darmanawa Royal City a Kano.
Allah Ya gafarta masa.
Lauyoyin Jihar Zamfara Sun Goyi Bayan Gayyatar Gwamna Dauda A Gaban Majalisa Kan Ŕikicin Majalisar Ďokoki.
Kungiyar lauyoyin Jihar Zamfara ta bayyana goyon bayanta ga matakin da Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta dauka na gayyatar Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, da shugabannin majalisar dokokin jihar domin su bayyana kan rikicin da ke kara tsananta a majalisar dokokin jihar da kuma tabarbarewar tsaro a fadin jihar da ke arewa maso yammacin Nijeriya.
Wannan kungiya, wadda ke da matsayi a fannin kare doka da tsarin mulki, ta bayyana kiran a matsayin matakin da kundin tsarin mulki ya amince da shi, bisa tanade-tanaden sashe na 88 da 89 na Kundin Tsarin Mulki na 1999, wanda ya ba Majalisar Tarayya damar gudanar da bincike kan batutuwan da suka shafi jama’a da kuma kiran jami’ai mas...
Gwamnatin Kenya ta bayyana jifa da takalmi da aka yi wa shugaban ƙasar, William Ruto a wani gangamin siyasa a ranar Lahadi, a matsayin “abun kunya”.
Bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya bugi hannun shugaban ƙasar na hagu, a yayin da ya ke magana.
https://twitter.com/citizentvkenya/status/1919295562660098502?t=JznCzRShAKV-GnuJ17gZpg&s=19
Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Isaac Mwaura, ya yi Alla-wadai da lamarin tare da kiran a kama waɗanda suka aikata hakan.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya ce “me zai faru idan dukkanmu muka fara jifar juna da takalma? Wane tarbiyya muke koya wa ƴaƴan mu?” Ya kuma buƙaci a girmama muƙamin shugaban ƙasa.
Kafofin watsa labarai a Kenya na bayar da rahoton cewa an kama mutum uku dangane da lam...
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, na cewa kimanin mutum 11 wasu ‘yan bindiga suka kashe a garuruwan Zamfarawa da Dogon Hayi da kuma Ɗan Kurmi.
Harin ya zo ne mako ɗaya bayan da ƴanbindigar suka karɓi harajin da ya kai naira miliyan 60, wanda suka tilastawa dagatai tattara waɗannan kuɗi daga wajen jama’a.
Sai dai, duk da haka sun ci gaba da kai wa mutanen hare-hare.
Jihar ta Zamfara dai ta sha fama da hare-haren ƴanbindiga waɗanda ke garkuwa domin neman kuɗin fansa.
Duk da irin ƙoƙari da gwamnati ke cewa tana yi na daƙile ayyukansu - hakan ya citura saboda yadda suke ci gaba da cin karensu babu babbaka.
Rundunar ƴansandan jihar Nasarawa ta ce ta fara bincike kan mutuwar wasu ƙananan yara biyar a garin Agyaragu cikin ƙaramar hukumar Obi a jihar.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Ramhan Nansel, ya fitar yau Litinin a birnin Lafia.
Sanarwar ta ce an gano gawawwakin yaran ne a cikin lalatacciyar motar da ke ajiye a gidan wani Mista Abu Agyeme.
Ta ce tuni kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa, Shetima Jauro-Mohammed ya umarci gudanar da cikakken bincike don tabbatar da haƙiƙanin abin da ya faru.
A ranar Lahadi da misalin ƙarfe 5:30 na yamma ne, wani magidanci ya kai rahoto ga 'yansanda cewa an gano ƙananan yara kwance shame-shame ba sa motsi a cikin wata lalatacciyar mota da ke yashe a harabar wani gida.
Yaran waɗanda shekarunsu suka kama...