Monday, December 15
Shadow
Shugaba Tinubu ya haramta sayo kayan da ake iyayi a cikin gida daga kasashen waje

Shugaba Tinubu ya haramta sayo kayan da ake iyayi a cikin gida daga kasashen waje

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a kokarin karfafa tattalin arzikin Najeriya ya hana sayo kayan da ake iya yinsu a cikin gida daga kasashen waje. Majalisar zartaswa tuni ta amince da wannan kudirin a zamanta na ranar Litinin inda aka bayyana cewa an yi hakanne dan karfafa masana'antun gida Najeriya. Da yake magana ga manema labarai bayan zaman, ministan yada labarai, Mohammed Idris yace an dauki wannan mataki ne dan karfafa amfani da kayan da aka kerasu a cikin gida. Yace sun kwaimwayi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ne a kokarin da yake na karfafa masana'antun kasarsa ta Amirka
Ana ta caccakar wani ɗansanda saboda ya ɗaura wa Ganduje takalmi

Ana ta caccakar wani ɗansanda saboda ya ɗaura wa Ganduje takalmi

Duk Labarai
Ana ta caccakar wani ɗansanda saboda ya ɗaura wa Ganduje takalmi. Wani ɗansanda na shan matsin lamba a kafafen sada zumunta bayan da aka gan shi ya na ɗaura wa Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC mai mulki, igiyar takalmi. A cikin wani bidiyo da ya karade intanet, an ga Ganduje tsaye yayin da dansandan da ba a bayyana sunansa ba ya durƙusa ya na ɗaura masa igiyar takalmi. Bidiyon da ya bayyana a yanar gizo ranar Litinin ya janyo ce-ce-ku-ce daga jama’a. Wasu sun yi mamakin yadda dan sanda da ke cikin kayan aiki zai aikata irin wannan abu, yayin da wasu kuma suka ce wata kila Ganduje ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar dan sandan.
Fadar Shugaban Kasa ta karyata maganganun Adesina kan ci gaban Najeriya

Fadar Shugaban Kasa ta karyata maganganun Adesina kan ci gaban Najeriya

Duk Labarai
Fadar Shugaban Kasa ta karyata maganganun Adesina kan ci gaban Najeriya Fadar Shugaban Ƙasa ta karyata maganganun da aka danganta wa Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Akinwumi Adesina, inda ya ce halin da ‘yan Najeriya ke ciki a yanzu ya fi na shekarar 1960 muni. Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin yada labarai , ya wallafa a shafinsa na X cewa Adesina ya dogara da wasu ƙididdiga “da ba su dace da bayanan da ake da su ba.” A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, “Babu wani mai lura da gaskiya da zai ce Najeriya ba ta samu ci gaba ba tun daga 1960. Yanzu haka, yayin da muke jiran sabon tsarin ƙididdigar GDP daga NBS, za mu iya cewa ba tare da jayayya ba cewa ya ninka na lokacin 'yancin kan mu sau 50, ko ma sau 100.” Onanuga ya zargi Adesina da yin ...
Fiye da ɗalibai miliyan 1.5 sun samu ƙasa da maki 200 a jarrabawar UTME ta 2025

Fiye da ɗalibai miliyan 1.5 sun samu ƙasa da maki 200 a jarrabawar UTME ta 2025

Duk Labarai
Fiye da ɗalibai miliyan 1.5 sun samu ƙasa da maki 200 a jarrabawar UTME ta 2025. Daga cikin ɗalibai 1,955,069 da suka zauna jarrabawar UTME ta shekarar 2025, fiye da miliyan 1.5 daga cikinsu sun samu ƙasa da maki 200 a jarrabawar. VANGUARD ta rawaito cewa rahoton kididdiga na sakamakon UTME na shekarar 2025 da Hukumar Jarrabawa ta JAMB ta fitar a ranar Litinin ya nuna cewa ɗalibai 420,415 kawai ne suka samu sama da maki 200 a wannan jarrabawar. A yayin da ɗalibai 4,756 suka samu sama da maki 320, kimanin ɗalibai 7,658 ne suka samu tsakanin maki 300 da 319.
Akwai haɗari kwanciya da waya a ƙarƙashin matashi-kai – Kwararre

Akwai haɗari kwanciya da waya a ƙarƙashin matashi-kai – Kwararre

Duk Labarai
Akwai haɗari kwanciya da waya a ƙarƙashin matashi-kai - Kwararre. Wani ƙwararre mai ba da shawara kan harkokin fasaha a TMB Tech, Akin Ibitoye, a yau Litinin ya gargadi ‘yan Najeriya game da lafiya da kuma illolin da ke tattare da kwanciya da wayoyin hannu a karkashin matashin kai ko a gefen gadajensu. Da ya ke magana a shirin Brief Morning a gidan Talabijin na Channels, Ibitoye ya jaddada cewa na'urorin tafi da gidanka na iya hana barci, da shafar lafiyar kwakwalwa da kuma haifar da hadarin gobara saboda tsananin zafi da batirin lithium-ion ka iya haddasa wa. "Kada ku kwana da wayar salula a ƙarƙashin matashin ku,” in ji shi. Ba ku sani ba."
Kafar mu kafar Kwankwaso a siyasa duk inda ga tafi zamu bishi – Abba Gida Gida

Kafar mu kafar Kwankwaso a siyasa duk inda ga tafi zamu bishi – Abba Gida Gida

Duk Labarai
Kafar mu kafar Kwankwaso a siyasa - Abba Gida Gida Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya sake jaddada kudurinsa na mara wa Sanata Rabiu Kwankwaso baya a dukkan harkokin siyasa. Gwamna Yusuf ya sha alwashin bin tafarkin siyasar Kwankwaso, yana mai cewa, "duk inda ya dosa a siyasa, magoya bayansa za su bishi." Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi ga kansiloli 484 daga kananan hukumomi 44 a fadar gwamnati ranar Lahadi. Abba ya kuma karyata zarge-zargen da tsohon sakataren gwamnatin jiha, Baffa Bichi, ya yi masa, inda ya kira shi da "makaryaci marar kunya," yana mai bayyana zarge-zargen a matsayin karya kuma abin dariya. Gwamnan ya fi mayar da hankali kan zargin cewa Kwankwaso na karɓar Naira biliyan biyu duk wata daga gwamnatin jihar Kano, yana mai cewa wannan zar...
Gwamnatin sojin Nijar ta hana sojoji yin ritaya

Gwamnatin sojin Nijar ta hana sojoji yin ritaya

Duk Labarai
Gwamnatin sojin Nijar ta hana sojoji yin ritaya A jamhuriyar Nijar, gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta ce ta ɗauki matakin hana jami’an tsaro yin ritaya a wannan shekara ta 2025 ko da kuwa shekarunsu sun kai na ajiye aikin. Wannan matakin na ƙunshe ne cikin wata takarda da ministan tsaro na Nijar, Janar Salifu Modu, ya aike wa hafsan hafsoshin sojin ƙasar, inda ya buƙaci a riƙe ɗaukacin sojojin da shekarunsu suka kai su yi ritaya daga aikin tsaro bisa la'akari da ɗimbin ayyuka da kuma alƙawuran da ke gaban sojojin a duka fadin ƙasar. Hukumomin tsaron ƙasar sun ce sun ɗauki wannan mataki ne saboda buƙatar da ke da akwai ta ƙarin sojoji a fagen daga musamman yadda ƙasar ke ci gaba da fuskantar hare-hare daga kungiyoyi masu ɗauke da makamai a yankunan ƙasar da dama. Shugaban ƙung...
Zulum zai mayar da ‘yan gudun hijira 6,000 gidajensu saboda ‘ƙaruwar karuwanci’ a sansanoni

Zulum zai mayar da ‘yan gudun hijira 6,000 gidajensu saboda ‘ƙaruwar karuwanci’ a sansanoni

Duk Labarai
Gwamnan jihar Borno a arewacin Najeriya ya bayyana shirinsa na mayar da iyalai 6,000 da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu sakamakon abin da ya bayyana da "ƙaruwar karuwanci" a sansanonin 'yan gudun hijira. Yawancin mutanen sun ftio ne daga ƙananan hukumomin Dikwa da Mafa, kamar yadda Gwamna Babagana Zlumu ya bayyana a sansanin 'yan gudun hijira na Muna da ke Maiduguri. A cewarsa, dole ne mutane su koma gidajensu domin su ci gaba da neman abin dogaro da kansu. "Mun lura cewa a sansanin 'yan gudun hijira akwai ƙaruwar karuwanci, da yawaitar 'yandaba, da cin zarafin yara, da kuma aikata laifuka iri-iri," in ji shi cikin wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar. Ya kara da cewa tuni aka mayar da kashi 75 cikin 100 na mazauna sansanin gidajensu. Gwamnan ya kuma ce kowane ma...
Ji Dalilai bakwai da ke ta’azzara talauci a yankunan karkarar Najeriya>>Inji Bankin Duniya

Ji Dalilai bakwai da ke ta’azzara talauci a yankunan karkarar Najeriya>>Inji Bankin Duniya

Duk Labarai
Wani sabon rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna yadda talauci ƙaruwa a yankunan karkara a Najeriya, inda alaƙluma ke nuna ya ƙaru zuwa kashi 75 cikin 100 a watan Afrilu. Rahoton da bankin ya fitar na watan Afrlun 2025, ya nuna cewa talaucin dai ya ƙaru a ɓangren karkara idan aka kwatanta da yadda yake a biranen ƙasar. Rahoton ya yi nazari kan girman talauci a ƙasashen duniya, yana mai bayyana kashi 30.9 cikin 100 na 'yan Najeriya na rayuwa ne kasa da dala biyu a kowacce rana a shekara ta 2018/2019 - kafin annobar korona. Haka kuma, rahoton ya nuna cewar 'wasu alkaluma da aka fitar na 2018/2019 ya nuna cewar akwai karin mutum miliyan 42 da suka sake faɗawa cikin talauci a Najeriya, wanda hakan ke nuni da fiye da rabin al'ummar ƙasar wato kashi 54% da aka yi ƙiyasin na fama da t...