Tuesday, December 16
Shadow
Kalli Bidiyo da Hotuna: Yanda ‘yan tà’adda suka kai hari sansanin sojoji a jihar Yobe, sun kàshè sojoji 4 da kona motocin yakin sojojin, daga farkon shekara zuwa Yanzu, Rahotanni sun bayyana cewa sun tashi sansanin sojoji sama da 8

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana a baya cewa, mayakan kungiyar Ìśìśì sun dauki alhakin kai harin da yayi sanadiyyar mutuwar sojojin Najeriya 4 da jikkata wasu a jihar Yobe. Kungiyar ta kuma wallafa hotunan harin da ta yi ikirarin kaiwa. An ga hotunan konannun motocin sojoji yayin da wasu kuma aka ga suna ci da wuta. https://twitter.com/Sazedek/status/1918787069247132094?t=xhNqOFWtBQr7VEQh5qsw1Q&s=19 Kungiyar ta yi ikirarin kai hari da tarwatsa sansanin sojoji sama da 10. Saidai Maau shashi sun ce sansanin sojoji 8 ne suka tarwatsa daga farkon shekararnan zuwa yanzu.
Kalli Bidiyo: “A dinga kula da mata, kada a bar su haka babu Jima’i, domin kyalesu babu jima’i akwai cutarwa a ciki”>>Inji Sheikh Al-Karmawi

Kalli Bidiyo: “A dinga kula da mata, kada a bar su haka babu Jima’i, domin kyalesu babu jima’i akwai cutarwa a ciki”>>Inji Sheikh Al-Karmawi

Duk Labarai
Babban Shehin malamin Addinin Islama, Sheikh Al-Karmawi ya bayar da shawarar a daina barin mata babu Jima'i. Yace hakan cutarwa ne. Ya bayyana hakanne a wani wa'azinsa dake ta jawo a kafafen sada zumunta. https://twitter.com/bapphah/status/1918895251189592065?t=K0AO9Uk750A9Bup-4p91AQ&s=19 “https://x.com/bapphah/status/1918895251189592065?t=zHgr9Re-qk-WI1r0zfWm3g&s=19 Wasu dai sun sokeshi akan lamarin inda wasu musamman mata suka yaba masa.
Kalli Bidiyo: Gwamnan Kano Ya Sa An Kwashe Almajiran Da Ke Kwana A Kan Titi An Kai Su Gidan Gwamnati An Ba Su Abinci Da Wajen Kwana

Kalli Bidiyo: Gwamnan Kano Ya Sa An Kwashe Almajiran Da Ke Kwana A Kan Titi An Kai Su Gidan Gwamnati An Ba Su Abinci Da Wajen Kwana

Duk Labarai
Gwamnan Kano Ya Sa An Kwashe Almajiran Da Ke Kwana A Kan Titi An Kai Su Gidan Gwamnati An Ba Su Abinci Da Wajen Kwana. https://twitter.com/Sadeeq_Malo/status/1918912112694342051?t=VeplQnJIjUgsntDSyUIQzw&s=19 A daren jiya ne dai gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gudanar da ran-gadi domin duba aikin ƙawata titin Lodge Road da gwamnatinsa ke yi inda ake sanya fulawoyi da fitilu masu amfani da hasken rana, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito. A lokacin ne kuma gwamnan ya ci karo da wasu yara suna bacci a kan titin. Da aka bincika sai aka gano yara ne almajirai da ke gararamba a gari. Nan da nan gwamna ya ba da umarni a kai su gidan gwamnati su ci abinci su kwanta zuwa washe-gari a maida su hukumar Hisbah daga nan a maida su makarantarsu su miƙa su a hannun iyaye...
Shin wai Har yanzu ana Tantamar wa yafi wani tsakanin Rarara da Sarkin Waka ko yanzu an gano wanda ke kan gaba?

Shin wai Har yanzu ana Tantamar wa yafi wani tsakanin Rarara da Sarkin Waka ko yanzu an gano wanda ke kan gaba?

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} An jima ana hada Rarara da Naziru Sarkin Waka tare da tunanin a tsakaninsu wanene yafi wani. Ko da bayan wakar da Rarara yawa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zuwansa Katsina, sai da aka yi wannan kwatance. Tambayar anan shine har yanzu ba'a gano wanene yafi wani ba a tsakanin su.
Ka kiyaye mu, Bamu Gama Jimamin Fafaroma Francis ba, Kada ka yi mana Izgilanci>>Cocin Katolika ta yi Allah wadai da Shugaban Amurka Donald Trump kan saka hotonsa sanye da kayan Fafaroma

Ka kiyaye mu, Bamu Gama Jimamin Fafaroma Francis ba, Kada ka yi mana Izgilanci>>Cocin Katolika ta yi Allah wadai da Shugaban Amurka Donald Trump kan saka hotonsa sanye da kayan Fafaroma

Duk Labarai
Cocin katolika reshen Birnin New York na kasar Amurka sun yi Allah wadai da shugaban kasar Amurka, Donald Trump saboda saka hotonsa sanye da kayan Fafaroma. Donald Trump a safiyar jiyane ya dauki hankula bayan da aka ganshi sanye da kayan Fafaroma a wani hoto da fadar shugaban kasar ta White House ta wallafa a kafar X, hoton da aka yi amannar na AI ne. A sanarwar cocin Katolika, tace bata dade da jimamin binne Fafaroma Francis ba kuma a yanzu ana kokarin zaben sabon Fafaroma dan haka Trump ya kiyayesu kada ya musu izgilanci.
Karanta Jadawalin Jihohi 10 da suka fi tsananin Talauci a Najeriya

Karanta Jadawalin Jihohi 10 da suka fi tsananin Talauci a Najeriya

Duk Labarai
Masana sun yi bincike inda suka gano jihohi 10 da suka fi talauci a Najeriya. Ga jadawalin jihohin kamar haka: 1. Sokoto State• Poverty Rate: 87.73%• Region: North West• Capital: Sokoto• Population (2023): 5.52 million 2. Taraba State• Poverty Rate: 87.72%• Region: North East• Capital: Jalingo• Population (2023): 3.27 million 3. Jigawa State• Poverty Rate: 87.02%• Region: North West• Capital: Dutse• Population (2023): 5.83 million 4. Ebonyi State• Poverty Rate: 79.76%• Region: South East• Capital: Abakaliki• Population (2023): 3.32 million 5. Adamawa State• Poverty Rate: 75.41%• Region: North East• Capital: Yola• Population (2023): 4.25 million 6. Zamfara State• Poverty Rate: 73.98%• Region: North West• Capital: Gusau• Population (2023): 4.52 milli...
Dole mu magance matsalar tsaro idan muna son masu zuba hannun jari su shigo Najeriya>>Shugaba Tinubu

Dole mu magance matsalar tsaro idan muna son masu zuba hannun jari su shigo Najeriya>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dolene gwamnati ta zage ta magance matsalar tsaro idan tana son masu zuba hannun jari su shigo Najeriya. Shugaban ya bayar da tabbacin Gwamnati na kwato garuruwan dake hannun 'yan ta'adda musamman a Arewa maso gabas. Shugaban ya bayyana hakane yayin ganawa da dattawa jihar ta Katsina a ziyarar da ya kai jihar inda yayi Alwashin yin amfani da na'urorin zamani da sauran kayan aiki na zamani dan magance matsalar garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro. Shugaban yace babu 'yan kasuwar da zasu je inda babu tsaro su zuba hannun jari, dan haka yace zasu hada hannu da gwamnatoci a kowane matakai su magance matsalar.